Amupitan: Abubuwan da 'Yan Najeriya ke So Sabon Shugaban INEC Ya Yi
- ’Yan Najeriya da kungiyoyin siyasa sun bayyana abin da suke fata daga sabon shugaban hukumar zabe ta kasa INEC, Farfesa Joash Amupitan
- Ana sa ran shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai mika sunansa ga majalisar dattawa a mako mai zuwa domin tantancewa kafin tabbatarwa
- Rahotanni sun nuna cewa Amupitan ne Farfesa na shida da zai jagoranci hukumar INEC bayan shekaru 10 na jagorancin Farfesa Mahmood Yakubu
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Idan aka tabbatar da sunansa a majalisar dattawa, Farfesa Joash Amupitan zai zama sabon shugaban hukumar zabe ta kasa INEC.
Wannan na zuwa ne bayan saukar Farfesa Mahmood Yakubu, wanda ya jagoranci hukumar tsawon shekaru 10, tun daga 2015 zuwa 2025.

Source: Twitter
Vanguard ta wallafa cewa kungiyoyi da jam’iyyu daban-daban a fadin kasar sun bayyana ra’ayoyinsu, suna sa ran sabon shugaban zai kawo sauyi da tabbatar da gaskiya a zabe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kiran ADC ga sabon shugaban INEC
Jam’iyyar ADC ta shawarci Farfesa Amupitan da ya kasance mai gaskiya da biyayya ga ’yan Najeriya, ba ga jam’iyyar da ke mulki ba.
Mai magana da yawun jam’iyyar, Bolaji Abdullahi ya ce wannan dama ce ga sabon shugaban INEC ya sanya sunasa a tarihi ta hanyar gudanar da sahihin zabe.
Ya ce:
“Muna sa ran zai nuna cewa INEC ba kayan aiki ba ce ga gwamnati,"
Maganar gwamna Mutfwang kan Amupitan
Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya bayyana farin cikinsa kan lamarin, yana mai cewa Amupitan babban masani ne mai kishin kasa kuma shugaba marar son kai.
A cikin sanarwar da mai magana da yawun sa, Gyang Bere, ya fitar a Facebook, gwamnan ya ce nada shi zai kara karfafa tsarin dimokuradiyya da shugabanci nagari.

Source: Twitter
Ya kuma yabawa Shugaba Tinubu saboda ya bai wa yankin Arewa ta Tsakiya wannan muhimmiyar dama, yana mai fatan cewa sabon shugaban zai yi aiki da gaskiya da hangen nesa.

Kara karanta wannan
'Babban dalilin da ya sa na zabi Amupitan, shugaban INEC': Tinubu ya fadi hikimarsa
Obidient ta nemi a yi gaskiya a INEC
Kungiyar Obidient Movement ta taya Amupitan murna tare da bayyana fatan ganin sabuwar dokar zabe da za ta tabbatar da gaskiya a zabubbukan 2027.
Shugabannin kungiyar, Dr. Yunusa Tanko da Nana Kazaure, sun ce suna fatan sabon shugaban zai kawo tsarin da zai dawo da martabar hukumar da ta dusashe a baya.
CUPP: 'Ka samar da amincewar jama’a'
Kungiyar CUPP ta bayyana cewa babban aikin da ke gaban Amupitan shi ne dawo da amincewar jama’a da hukumar zabe.
Sakataren kungiyar, Peter Ameh, ya ce bayan zaben 2023 wanda aka caccaki INEC saboda matsaloli da rashin gaskiya, jama’a sun rasa amincewa da hukumar.
Ya ce:
“Farfesa Amupitan zai dauki nauyi mai girma – na dawo da amincewar da ta ruguje sakamakon gazawar BVAS da rashin bayyana sakamako cikin lokaci.”
Tinubu ya yabi tsohon shugaban INEC
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya yaba wa tsohon shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu.
Tinubu ya bayyana haka ne a wata wasika da mai magana da yawunsa ya bayyana wa manema labarai.
Shugaban ya bayyana cewa Mahmood Yakubu ya jagoranci gudanar da sahihin zabe a tarihin Najeriya a lokacinsa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

