Sojoji Sun Samu Gagarumar Nasara kan 'Yan Bindiga a Sokoto

Sojoji Sun Samu Gagarumar Nasara kan 'Yan Bindiga a Sokoto

  • 'Yan bindiga dauke da muggan makamai sun kai wani harin ta'addanci a karamar hukumar Wurno da ke jihar Sokoto
  • Miyagun sun kai harin ne da daddare inda suka bude wuta kan mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba
  • Dakarun sojoji sun kai agajin gaggawa inda suka hallaka 'yan bindiga masu yawa tare da raunata wasu a kazamin artabun da suka yi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Sokoto - Dakarun sojojin Najeriya na Operation Fansan Yanma sun hallaka ‘yan bindiga da dama a jihar Sokoto.

Dakarun sojojin sun hallaka 'yan bindigan ne yayin wani kazamin artabu da ya gudana a kauyen Sabon Garin Kwargaba, cikin karamar hukumar Wurno ta jihar Sokoto.

Sojoji sun kashe 'yan bindiga a Sokoto
Dakarun sojojin Najeriya a bakin aiki. Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun farmaki bayin Allah a Nasarawa, an samu asarar rayuka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan bindiga sun kai hari

Majiyoyi sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a daren ranar Talata, 7 ga watan Oktoban 2025, da misalin karfe 11:30 na dare.

'Yan bindigan masu yawa dauke da muggan makamai sun kai farmaki a kauyen, inda suka rika harbi kan mai uwa da wabi domin tsoratar da mazauna yankin.

Sojoji sun ragargaji 'yan bindiga

Dakarun sojoji na rundunar Operation Fansan Yanma sun yi saurin zuwa wurin bayan sa suka samu kiran gaggawa.

Sojojin sun yi arangama da ‘yan bindigan a wani artabu mai tsanani wanda ya ɗauki mintuna da dama.

“An kashe ‘yan bindiga da dama yayin arangamar, yayin da wasu suka gudu dauke da raunukan harbin bindiga."
"Abin takaici, soja ɗaya da wata mace daga cikin mutanen kauyen sun rasa rayukansu a harin.”

- Wata majiya

Majiyar ta ƙara da cewa, an garzaya da wani soja da ya ji rauni a yayin harin zuwa asibitin koyarwa na jami’ar Usmanu Danfodiyo (UDUTH), Sokoto, inda ake duba lafiyarsa.

Kara karanta wannan

Kebbi: 'Yan bindiga sun yi ta'asa bayan kai mummunan hari, sun fille kan Sarki

An kuma tabbatar da cewa an tura karin jami’an tsaro zuwa yankin domin hana karin hare-hare da kuma dawo da zaman lafiya.

"Sojoji sun fara aikin zakulo ‘yan bindigar da suka tsere cikin daji, domin tabbatar da cikakken tsaro a yankin."

- Wata majiya

Sojoji sun fafata da 'yan bindiga a Sokoto
Taswirar jihar Sokoto, tarayyar Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Abin a yaba ne

Wani mazaunin Sokoto, Usman Abubakar, ya yaba kan nasarar da dakarun sojojin suka samu kan 'yan bindiga.

"Wannan abin a yaba ne. Muna fatan za su ci gaba da kara kaimi don murkushe miyagu."
"Suna bakin kokarinsu, muna rokon Allah ya ci gaba da ba su nasara a aikin da suke yi."

- Usman Abubakar

Karanta wasu labaran kan dakarun sojoji

Sojoji sun fafata da 'yan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji sun yi artabu da 'yan ta'adda a jihar Taraba da ke yankin Arewa maso Gabas na Najeriya.

Kara karanta wannan

Shiri ya baci: 'Yan bindiga sun hallaka jami'an tsaro a Zamfara

Sojojin na rundunar 6 Brigade na Operation Whirl Stroke, sun yi nasarar dakile harin da ‘yan ta’adda suka kai a kauyen Tor-Ikyeghgba, jihar Taraba.

Kwamandan rundunar, Brig. Janar Kingsley Uwa, ya yaba wa jaruntakar dakarun bisa kwazon da suka nuna da kuma saurin kai daukin da suka yi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng