Majalisa Ta Cin Ma Matsaya kan Zargin Yi Wa Kiristoci Kisan Kiyashi a Najeriya
- Ana ci gaba da muhawara kan zargin cewa ana yi wa mabiya addinin Kiristoci kisan kare dangi a wasu sassa na Najeriya
- Majalisar Wakilan tarayya ta fito ta yi magana kan zargin wanda yake fitowa daga bakin wasu 'yan majalisu a kasar Amurka
- Mataimakin shugaban majalisar wakilan, Ben Kalu, ya gabatar da kudiri wanda aka amince da shi a ranar Laraba, 8 ga watan Oktoban 2025
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Majalisar Wakilai ta yi magana kan zargin zaluntar Kiristoci da yi musu kisan kare dangi a Najeriya.
Majalisar Wakilan ta karyata zargin tana mai bayyana irin wannan labari a matsayin karya tsagwaronta.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta ce hakan ya biyo bayan wata muhawara da aka gabatar a zauren Majalisar a ranar Laraba, 8 ga watan Oktoban 2025.

Kara karanta wannan
Atiku ya shiga sahun masu neman fito da shugaban kungiyar ta'addanci da aka kama tun 2021
Mataimakin shugaban majalisar, Benjamin Okezie Kalu ne ya gabatar da kuduri kan lamarin.
Gwamnati ta karyata zargin kisan Kiristoci
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, Ministan yada labarai da wayar da kai, Mohammed Idris, da wasu ƙungiyoyi a Najeriya sun karyata wannan zargi.
Sun bayyana cewa tsaron kasa da matsalolin ta’addanci ba su da alaka da addini guda ɗaya.
Haka kuma, kungiyar MURIC ta bayyana cewa Musulmai suna cikin waɗanda ke fuskantar hare-haren ta’addanci, don haka ba daidai ba ne a nuna kamar ana kai wa addini guda hari.
An gabatar da kudiri kan Najeriya a Amurka
Majalisar ta kuma bukaci a ɗauki mataki na diflomasiyya domin mayar da martani kan wani kudiri da aka gabatar a Majalisar Dattawan Amurka, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar da labarin.
Kudirin na neman a sanya Najeriya cikin jerin kasashen da ake zargin suna tauye ‘yancin addini.
Sanata Ted Cruz ne ya gabatar da kudirin wanda ya yi ikirarin cewa ana zaluntar Kiristoci a Najeriya.
A cikin kudurin, Benjamin Kalu ya bayyana damuwarsa kan labaran da ke nuna kamar gwamnati tana goyon bayan rikicin addini.
Majalisar bayan ta amince da kudurin, ta yi watsi da bayanin da ke nuna cewa gwamnati na goyon bayan rikicin addini da Najeriya ke fama da shi.
Ta jaddada cewa tsarin mulkin kasar nan ya bada cikakken ‘yanci ga kowa wajen gudanar da addini.

Source: Twitter
Matakin da majalisar Najeriya ta dauka
Majalisar ta umurci kwamitocinta kan harkokin waje, tsaro da leken asiri, cikin gida da harkokin ‘yan Sanda, da su tsara martanin diflomasiyya a hukumance ta ofishin ma’aikatar harkokin waje da ofishin Jakadancin Najeriya a birnin Washington D.C cikin kwana 21.
Ta bukaci su aika da takardar korafi ta diflomasiyya zuwa ga masu ɗaukar nauyin kudirin Amurka da kwamitocin da abin ya shafa a Majalisar Amurka.
Sannan su mika bayanan da suka nuna hakikanin gaskiyar lamura da matsayar gwamnati kan batun, domin kare mutuncin Najeriya a idon duniya.
CAN ta aika sako ga gwamnatin tarayya
A wani labarin kuma, kun ji cewa kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), ta nuna damuwa kan matsalar rashin tsaro.
Kungiyar CAN ta bayyana cewa wasu al'ummomin Kiristoci na fuskantar hare-hare a sassa daban-daban, musamman a Arewacin Najeriya.
CAN ta bukaci gwamnatin tarayya ta dauki matakan gaggawa domin kawo karshen muzgunawar da ake yi wa Kiristoci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

