Masanan Bankin Duniya Sun Karantar da Tinubu Yadda Za a Gyara Tattalin Arziki

Masanan Bankin Duniya Sun Karantar da Tinubu Yadda Za a Gyara Tattalin Arziki

  • Bankin Duniya ya ce Najeriya ta samu nasara bayan cire tallafin man fetur da hada tsarin kudin kasashen waje da wasu bangarori
  • Bankin ya bukaci gwamnatin tarayya ta kara haraji a wasu bangarori da kuma rage kashe kudin da bai da amfani
  • Ya kuma shawarci gwamnati da ta binciki NNPC, ta sabunta dokokin saye da kasafin kudi, tare da barin Naira ta daidaita da kasuwa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Bankin Duniya ya ba Najeriya shawara kan gyaran tattalin arziki da inganta kudaden gwamnati domin kawo sauyi.

Bankin ya shawarci Gwamnatin Tarayyar Najeriya da ta ci gaba da takaita kashe kudi da kula da tsauraran matakan kudi domin tabbatar da daidaito.

Bankin Duniya ya ba Tinubu shawara kan tattalin arziki
Shugaban Bankin Duniya, Ajay Banga da Tinubu a fadar shugaban kasa. Hoto: @DOlusegun.
Source: Twitter

Tattalin arziki: Shawarar Bankin Duniya ga Tinubu

A rahotonsa na baya-bayan nan da TheCable ta samu mai suna 'Nigeria Development Update (NDU)' da aka fitar, bankin ya ce Najeriya ta samu gagarumar nasara wajen daidaita tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Najeriya ta karyata bankin duniya kan samun talakawa miliyan 139 a mulkin Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce tun bayan cire tallafin man fetur da hada tsarin musayar kudin waje an samu daidaito amma ya gargadi cewa wadannan nasarorin na iya lalacewa idan ba a kara tsaurara matakai ba.

Bankin Duniya ya bukaci Babban Bankin Najeriya (CBN) da ya ci gaba da saita haraji ta hanyar da ya dace tare da guje wa buga kudi domin cike gibin kasafin kudi.

Ya ce:

“A kara amfani da manufofin kudi (MPR) wajen daidaita yawan kudin da ke yawo, tare da gudanar da bude kasuwa (OMO) da sauran hanyoyin da suka dace.”

Bankin Duniya ya kuma nemi gwamnati ta fitar da bayanan kudi na kowane wata domin tabbatar da gaskiya, da kuma barin Naira ta daidaita da kasuwa ba tare da tsoma baki ba.

Bankin Duniya ya shawarci Tinubu kan kara haraji a wasu bangarori
Shugaba Bola Tinubu yayin zaman majalisar zartarwa. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Shawarwari kan karin haraji da kashe kudi

Bankin Duniya ya ba da shawara cewa gwamnatin tarayya ta karawa lafiyar jama’a haraji, ta kuma kara kudin VAT a hankali don dacewa da tsarin kasashen ECOWAS.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Za a rika biya wa talabijin da radiyo haraji, jama'a sun fara korafi

Haka kuma bankin ya shawarci gwamnati da ta daina kashe kudaden da ba su da amfani kamar siyan motoci da shirya horo, ta kuma takaita cire kudi daga asusun jihohi.

A bangaren makamashi, bankin ya bukaci gwamnati ta ci gaba da barin kasuwar fetur ta kasance kasuwa mai zaman kanta, tare da biyan bashin tallafin wutar lantarki da aka tara.

Neman bincike kan NNPC, sabon tsarin kasafin kudi

Daga karshe, Bankin Duniya ya bukaci gwamnati da ta gudanar da bincike na musamman kan kamfanin man fetur na kasa NNPC.

Ya kuma jaddada cewa gwamnatin Najeriya ta rage dogaro da bashi, ta kuma kara gaskiya da bin doka a tsarin kasafin kudi da gudanar da kudi.

Najeriya ta kalubalanci rahoton Bankin Duniya

A baya, kun ji cewa bayan rahoton Bankin Duniya, Fadar Shugaban Kasa ta ce alkaluman da suka nuna cewa mutane miliyan 139 a Najeriya na fama da talauci karya ne.

Hadimin Shugaba Tinubu shawara kan yada labarai, Sunday Dare, ya bayyana cewa rahoton ya dogara ne da bayanan tsohuwar kididdiga.

Dare ya ce Najeriya na kan tafarkin farfadowa da shirya gyare-gyaren da za su inganta tattalin arziki da walwalar ‘yan kasa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.