Najeriya Ta Yi Rashin Dattijo: Tsohon Jakada Ya Rasu Yana da Shekaru 92
- Rahotanni da muke samu sun tabbatar da rasuwar tsohon jakadan Najeriya a Birtaniya jiya Laraba 8 ga watan Oktoban 2025
- An shiga jimami bayan rasuwar Dr Christopher Kolade, yana da shekaru 92 da haihuwa, kamar yadda iyalansa suka bayyana
- Iyalansa sun ce tsohon shugaban 'Cadbury Nigeria' ya rasu cikin aminci a ranar Laraba, bayan cikar Najeriya 65 da samun 'yanci
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Lagos - An tabbatar da rasuwar tsohon mai yada labarai kuma tsohon jakadan Najeriya a Birtaniya bayan fama da jinya.
Majiyoyi sun ce Dr Christopher Kolade ya rasu yana da shekaru 92 a jiya Laraba 8 ga watan Oktoba, 2025 da muke ciki.

Source: Twitter
An tabbatar da rashin dattijo a Najeriya
Iyalansa sun sanar da rasuwarsa a cikin wata sanarwa da Punch ta samu a ranar Alhamis 9 ga watan Oktobar 2025.
Sun bayyana cewa marigayin ya rasu cikin aminci a ranar Laraba tare da godewa Ubangiji bisa damar da ya ba marigayin a duniya.
Sanarwar ta ce:
“Mun gode wa Allah saboda rayuwarsa mai cike da bangaskiya da hidima ga al’umma, da albarkar da Ubangiji ya yi masa."
Takaitaccen tarihin marigayi Kolade
An haifi Kolade a ranar 28 ga Disamba, 1932 a Erin-Oke, Jihar Osun, mahaifinsa malamin coci ne na Anglican, ya yi karatu a kwalejin gwamnati da ke Ibadan.
Daga nan sai ya wuce kwalejin 'Fourah Bay' a Freetown, Sierra Leone, ya kammala karatunsa na gaba, daga bisani ya fara aiki a gidan rediyo na Najeriya.

Source: Original
Sauran mukamai da marigayin ya rike
Kolade ya rike mukamin Darakta Janar na hukumar yada labarai ta Najeriya kafin daga bisani ya zama shugaban kamfanin 'Cadbury Nigeria'.
Ya kuma yi aiki a matsayin jakadan Najeriya a Birtaniya, inda ya ba da gagarumar gudummawa, ya yi tabbatar da gaskiya da mutunci a tsarin diflomasiyya, cewar Premium Times.
Kolade ya koyar da darussa masu muhimmanci da suka hada a koyar da yadda za a gudanar da rikici a cikin al'umma a makarantar koyon kasuwanci ta Lagos.
Har ila yau, marigayin ya koyar da wasu darussa na musamman a jami'ar Pan-Atlantic da ke jihar Lagos.
Gudunmawar da marigayin ya bayar a jami'o'in Najeriya
Ya rike mukamai da dama a jami’o’i, ciki har da shugaban jami'ar Pan-Atlantic da kuma shugaban jami'ar McPherson da ke Jihar Ogun a Kudu maso Yammacin Najeriya.
Kolade ya sadaukar da rayuwarsa wajen inganta da’a da gaskiya a kasuwanci, ya jagoranci kungiyoyi kamar 'Integrity Organisation', GTE da CBI.
An yi rashin tsohon jakada a Zamfara
Mun ba ku labarin cewa Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yi ta'aziyyar rasuwar tsohon Jakadan Najeriya a kasar Tunisia, Ambasada Muhammad Jabbi Maradun.
Gwamna Dauda Lawal ya bayyana marigayin a matsayin dattijo wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen fafutukar kafa jihar Zamfara.
An tabbatar da cewa marigayin ya yi bankwana da duniya ne a birnin tarayya Abuja bayan ya dauki lokaci yana jinyar rashin lafiya.
Asali: Legit.ng

