'Yan Sanda Sun Samu Nasara kan Mutanen da Ake Zargi da Kisan 'Yar Jarida a Abuja

'Yan Sanda Sun Samu Nasara kan Mutanen da Ake Zargi da Kisan 'Yar Jarida a Abuja

  • Jami'an rundunar 'yan sanda a birnin tarayya Abuja sun samu nasarar cafke wasu mutanen da ake zargin 'yan fashi da makami ne
  • An samu nasarar cafke mutanen ne bayan an samu bayanan sirri kan motsinsu a birnin tarayya Abuja
  • A cewar majiyoyi, mutanen da aka cafke na da hannu kan kisan da aka yi wa wata 'yar jarida da wani mai gadi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya (NPF) sun kama mutanen da ake zargi da kisan wata 'yar jarida, Somtochukwu Christella Maduagwu, a Abuja.

Jami'an 'yan sandan sun cafke mutanen ne guda 12 da ake zargi da hannu a harin da ya haifar da rasuwar yar jaridar da kuma wani mai gadi, Barnabas Danlami.

'Yan sanda sun cafke masu laifi a Abuja
Sufeto Janar na 'yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun. Hoto: @PoliceNG
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta ce a cewar wata sanarwa da ‘yan sanda suka fitar, dukkan waɗanda aka kama sun amsa cewa suna da hannu a cikin harin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace mutane yayin da 'yan sanda suka kashe miyagu a Zamfara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan fashin sun kai harin ne a rukunin gidajen Unique da ke kauyen Gishiri, a yankin Katampe, cikin babban birnin tarayya Abuja.

'Yan sanda sun bi umarnin shugaban kasa

Lamarin mai tayar da hankali ya faru ne a ranar 29 ga Satumba, lokacin da kimanin ‘yan bindiga 15 suka farmaki wani ginin bene mai hawa huɗu da ke ɗauke da dakuna 16 a yankin Katampe na Abuja.

An kama waɗanda ake zargin ne bayan umarnin da Shugaba Tinubu ya ba jami’an tsaro da su gano waɗanda suka yi kisan.

Zagazola Makama ya ce jami’an tawagar “Scorpion Squad” karkashin jagorancin ACP Victor O. Godfrey ne suka cafke wadanda ake zargin, ta hanyar amfani da na’urorin zamani da bayanan sirri.

Su waye 'yan sanda su ka cafke?

Sunayen mutanen da aka kama sun hada da:

  • Shamsudeen Hassan, karamar hukumar Malumfashi jihar Katsina
  • Hassan Isah mai shekara 22, Zariya, jiihar Kaduna
  • Abubakar Alkamu (Abba), 27 – Musawa LGA, Katsina
  • Sani Sirajo (Dan Borume), mai shekara 20, karamar hukumar Malumfashi jihar Katsina
  • Mashkur Jamili (Abba), mai shekara 28 – karamar hukumar Igabi jihar Kaduna
  • Suleiman Badamasi (Dan-Sule), mai shekara 21, karamar Malumfashi jihar Katsina
  • Abdulsalam Saleh (Na-Durudu), karamar hukumar Katsina jihar Katsina
  • Zaharadeen Muhammad (Gwaska), mai shekara 23, karamar hukumar Chikun jihar Kaduna
  • Musa Adamu (Musa Hassan), mai shekara 30, karamar hukumar Malumfashi jihar Katsina
  • Sumayya Mohammed (Baby), mai shekara 27, jihar Kaduna
  • Isah Abdulrahman (Abbati), mai shekara 25, karamar hukumar Zariya jihar Kaduna
  • Musa Umar (Small), mai shekara 31, karamar hukumar Maiduguri jihar Borno

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace matar babban jami'in gwamnati, suna neman miliyoyin Naira

Yadda aka cafke wadanda ake zargin

Majiyoyin ‘yan sanda sun bayyana cewa Shamsudeen, Hassan, Alkamu, da Sirajo aka fara cafkewa, kuma dukkansu sun amsa laifin da ake zarginsu da shi.

A lokacin bincike, Shamsudeen ya amsa cewa shi ne ya harbi mai gadi, Barnabas Danlami, lokacin da yake kokarin hana su shiga wurin.

Shi kuma Sirajo ya bayyana cewa ya yi kokarin kama Maduagwu lokacin da ta faɗo daga bene na uku, amma nauyinta ya rinjaye shi.

Shamsudeen ya kara da cewa shi ne ya tafi da motar Honda CR-V mallakar Maduagwu bayan sun gama harin, inda kowannensu ya karɓi N200,000 daga abin da suka sace.

'Yan sanda sun cafke mutanen da ake zargi kan kisan Somtochukwu
'Yar jarida, Somtochukwu Christella Maduagwu. Hoto: @renoomokri
Source: Twitter

An kuma kama wasu mutum uku a ranar 8 ga Oktoba, ciki har da Musa Umar da Hassan Isah, lokacin da jami’an 'yan sanda, suka tare su yayin da suke kan hanyar zuwa wani sabon harin fashi da makami a Maitama.

Dukkan waɗanda ake zargi suna hannun ‘yan sanda, kuma duk sun amsa laifuffukan da ake tuhumarsu da su.

Kara karanta wannan

Jama'an gari sun taimaki 'yan sanda, an fatattaki mayakan Boko haram a Borno

Majiyoyin ‘yan sanda sun ce kwamishinan ‘yan sanda na Abuja ya yaba da kwazon tawagar Scorpion Squad.

Ya kuma bada tabbacin cewa rundunar za ta ci gaba da sintiri domin kawar da ‘yan ta’adda da masu aikata laifuka daga babban birnin tarayya.

'Yan sanda sun kashe 'yan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an rundunar 'yan sanda a jihar Zamfara sun samu nasara kan 'yan bindiga.

Jami'an 'yan sandan sun hallaka 'yan bindigan ne bayan sun yi musu kwanton bauna a karamar hukumar Gusau.

'Yan sandan sun hallaka 'yan bindigan ne guda biyu lokacin da suka yi musayar wuta a cikin daji.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng