Duk da Nada Shi Shugaban APC, Yilwatda Ya Ki Barin Kujerar Minista bayan Wata 2
- A watan Yulin 2025 aka nada sabon shugaban jam'iyyar APC mai mulki bayan Abdullahi Umar Ganduje ya yi murabus
- Kusan watanni uku bayan zama shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda bai yi murabus daga mukamin minista ba
- Har ila yau, har yanzu babu wanda aka nada sabon minista a ma'aikatar jin kai da walwalar jama'a domin maye gurbin Nentawe
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Ana neman wata uku kenan da nada sabon shugaban jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.
Kusan watanni uku bayan nadinsa a matsayin shugaban jam’iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda bai yi murabus daga mukamin minista ba.

Source: Facebook
Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ita ta wallafa sanarwar nadin Nentawe a shafin X a ranar 24 ga watan Yulin 2025.

Kara karanta wannan
Atiku ya shiga sahun masu neman fito da shugaban kungiyar ta'addanci da aka kama tun 2021
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Nadin Nentawe bayan murabus din Ganduje
An nada Yilwatda ranar 24 ga Yuli, 2025 domin ya maye gurbin Abdullahi Ganduje wanda ya ajiye aiki saboda rashin lafiya.
Kusan wata uku kenan da karbar muƙamin shugaban APC amma har yanzu yana rike mukamai biyu wanda wasu lauyoyi ke ganin ya saba doka.
Kafin rike muƙamin minista a Najeriya, Nentawe ya nemi takarar gwamna karkashin APC a jihar Plateau a zaben 2023, cewar rahoton Punch.

Source: Twitter
Nentawe: Martanin lauyoyi kan rike kujeru 2
Lauyoyi da masana tsarin mulki sun gargadi cewa rike mukamin minista da shugabancin jam’iyya ya saba wa tsarin mulki kuma yana iya haifar da rikici.
Sashe na 147 da 192 na kundin tsarin mulki sun fayyace cewa ministoci suna yi wa kasa hidima kaco-kam ba wai jam’iyya ta siyasa kawai ba.
A cewar Ebun-Olu Adegboruwa:
“INEC bai kamata ta amince da Yilwatda ba a matsayin shugaban jam’iyya har sai ya ajiye mukaminsa na minista.”
Ya ce ya sabawa kundin tsarin mulki ga minista ya rike mukamin siyasa, yana bukatar Bola Tinubu ya sa shi ya bayyana albashin da yake karɓa.
“A halin yanzu a idon doka, jam’iyyar APC ba ta da shugaba saboda wannan rashin yin murabus.”
- Ebun-Olu Adegboruwa
Ana zargin Nentawe da son rai
Shi ma lauya Chris Nwufo ya fadawa Independent cewa wannan lamari ya nuna rashin mutunta kundin tsarin mulki da kuma dokokin cikin jam’iyyar APC.
Nwufo ya ce:
“Ta yaya minista da yake yi wa ‘yan kasa baki daya aiki zai rike mukamin shugaban jam’iyya mai son jam’iyya ɗaya?”
Ya ce wannan ya nuna rashin adalci da tsananin nuna son kai, yana bukatar gwamnati ta dauki mataki domin gyara abin kafin ya zama rikici.
Shugabannin APC sun saba ajiye mukamansu
A lokacin da Abdullahi Adamu ya zama shugaban jam'iyya, ya hakura da kujerar da yake kai a majalisar dattawa na Sanatan Nasarawa ta Yamma.
Haka majalisar tarayya rahoto ya faru da Abubakar Kyari wanda ya zama mataimakin shugaban jam'iyya APC na kasa (Yankin Arewa).
A baya, Mai Mala Buni ya taba rike jam'iyyar APC alhali yana gwamnan Yobe.
Nentawe ya magantu kan shigar Kwankwaso APC
A wani labarin, kun ji cewa shugaban APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, ya bayyana cewa ƙofar jam’iyyar a buɗe take ga Rabiu Kwankwaso.
Farfesa Nentawe ya ce lokacin da nasarar Bola Tinubu ta bayyana, za a ga da dama daga cikin waɗanda suka fita suna komawa APC.
Nentawe Yilwatda ya karɓi shugabancin jam’iyyar ne bayan Abdullahi Ganduje ya yi murabus daga kujerar bisa wasu dalilai.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

