Atiku Ya Shiga Sahun Masu Neman Fito da Shugaban Kungiyar Ta'addanci da Aka Kama Tun 2021
- Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ya shiga layin masu kira da a saki shugaban IPOB, Nnamdi Kanu
- Atiku ya bayyana cewa ci gaba da tsare jagoran haramtacciyar kungiyar IPOB cin zarafi ne ga doka bayan kotu ta ba da belinsa
- Gwamnatin Tarayya ta sake tsare Kanu tun 2021 bayan an kama shi a kasar Kenya, sai dai tana shan matsin lamba daga mutane da dama
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ya bayyana cikakken goyon baya ga fafutukar 'yancin jagoran kungiyar ta'addanci (IPOB), Nnamdi Kanu.
Atiku, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaɓen 2023 ya buƙaci gwamnatin tarayya ta saki jagoran IPOB, Mazi Nnamdi Kanu, ko ta gurfanar da shi a kotu bisa doka.

Source: Facebook
Atiku ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook da safiyar yau Alhamis, 9 ga watan Oktoba, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan kira na Atiku na zuwa yayin da manyan yankin Kudu maso Gabas ke kara matsa lamba don ganin an sako Nnamdi Kanu.
Masu kiraye-kirayen na ganin cewa sakin Kanu zai zama wata hanya ta samar da zaman lafiya mai dorewa a yankin Kudu maso Gabas, cewar rahoton Punch.
Atiku ya nemi a saki Nnamdi Kanu
Da yake goyon bayan sakin shugaban IPOB, Atiku ya bayyana cewa ci gaba da tsare Kanu duk da umarnin kotu da ya ba da belinsa, “rauni ne ga lamirin ƙasa” da kuma “tabo ga imaninmu ga mulkin demokuradiyya.”
Ya ce kin bin umarnin kotu da gwamnatin tarayya ke yi abu ne da ya nuna cin zarafi da amfani da iko ba bisa ka’ida ba, yana mai cewa hakan barazana ce ga adalci da daidaito a ƙasar nan.
"Ci gaba da tsare Nnamdi Kanu babban rauni ne ga lamirin ƙasarmu. Kin bin umarnin kotu da ta bayar da belinsa amfani ne da iko kuma cin zarafi ne ga adalci,” in ji Atiku.
Atiku ya goyi bayan fafutukar Sowore
Atiku ya kuma nuna goyon bayansa ga kamfen ɗin da Omoyele Sowore ke jagoranta domin ganin an saki Kanu ko kuma a gurfanar da shi a kotu.
Ya ƙara da cewa gazawa ce babba ga duk wani ‘dan kishin ƙasa idan aka bari batun Kanu ya ci gaba da zama “tamkar wanni rauni da ƙasar nan ta gaza warkarwa.”
“Mun gaza a matsayinmu na ‘yan ƙasa masu kishin ƙasa idan muka bar wannan batu ya ci gaba da zama raunin da ya fi karfin a yi maganinsa a ƙasar nan,” in ji shi.

Source: Facebook
Gwamna Otti ya gana da Tinubu kan Kanu
A wani labarin, kun ji cewa gwamnan jihar Abia, Alex Otti, ya ce nan ba da jimawa ba za a saki Nnamdi Kanu , shugaban haramtacciyar ƙungiyar IPOB.
Gwamna Otti ya sanar da shirin sako Kanu a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, bayan ganawarsa da Shugaba Bola Tinubu.
Alex Otti ya ce tattaunawa ta yi nisa kuma nan ba da jimawa ba Gwamnatin Ahugaba Tinubu za ta saki shugaban kungiyar ta'adanci, IPOB.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


