Zargin Takardun Bogi: Za a Maka Hadimin Ministan Tinubu da Ya Yi Murabus a Kotu

Zargin Takardun Bogi: Za a Maka Hadimin Ministan Tinubu da Ya Yi Murabus a Kotu

  • Premium Times ta bayyana shirinta na gurfanar da kakakin tsohon ministan kimiyya, Robert Ngwu, bisa zargin ɓata suna
  • Robert Ngwu dai ya zargi jaridar da karɓar Naira miliyan 100 daga gwamnatin Enugu don gudanar da binciken takardun ministan
  • Amma babban editan jaridar, Musikilu Mojeed, ya ce zargin karya ne kuma suna da ƙwarin gwiwar tabbatar da gaskiya a kotu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Premium Times ta ce za ta ɗauki matakin shari’a kan Robert Ngwu, kakakin tsohon ministan kimiyya da fasaha, Uche Nnaji, bisa zargin ƙarya da ɓata suna.

Robert Ngwu ya dabawa kansa wuka a ciki ne lokacin da ya zargi jaridar da karɓar cin hancin Naira miliyan 100 daga gwamnatin jihar Enugu.

Jaridar Premium Times za ta yi karar hadimin tsohon minista da ya yi murabus
Tsohon ministan kimiyya da fasaha da ya yi murabus, Uche Geoffrey Nnaji. Hoto: @ChiefUcheNnaji
Source: Twitter

A zantawarsa da Channles TV a ranar Talata, Ngwu ya ce jaridar ta karbi kudin ne don gudanar da binciken kan takardun shaidar karatu da ake zargin ministan ya ƙirƙira.

Kara karanta wannan

Ana batun kisan kiyashin Kiristoci, CAN ta aika sako ga gwamnatin tarayya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An karyata kalaman hadimin tsohon minista

Sai dai, yayin da aka matsa masa da tambayoyi kan sahihancin ikirarinsa, Ngwu ya amince cewa babu wata hujja da ke tabbatar da zargin da ya yi.

Da yake mayar da martani, Musikilu Mojeed, babban Editan jaridar ya bayyana zargin a matsayin karya tsagwaronta da kuma ɓata suna, yana mai cewa jaridar ta gina kanta bisa gaskiya da aiki cikin ƙwararewa.

“Mun shafe kusan shekaru 15 muna aikin jarida cike da gaskiya da ƙwarewa. Ba wanda ya taɓa zarginmu da karbar cin hanci.
“Robert Ngwu ko Uche Nnaji ba za su iya rushe abin da muka dauki tsawon lokaci muna ginawa bisa doron gaskiya ba.”

- Babban editan Premium Times, Musikilu Mojeed.

Premium Times za ta kai Ngwu kotu

Musikilu Mojeed ya ƙara da cewa lauyoyin jaridar sun fara nazarin maganganun Ngwu kuma za su tabbatar da cewa ya kawo hujjoji a gaban kotu.

Kara karanta wannan

NYSC: Jerin ministoci 6 da suka shiga badakalar takardun bogi a Najeriya

Ya bayyana cewa:

“Ya kamata ya nuna yadda aka bai wa Premium Times kuɗin, da kuma yadda aka karɓa.
“Mu jarida ce mai tsayin daka kan gaskiya da bincike mai zurfi, kuma za mu ci gaba da yin hakan ba tare da shayin kowa ba.”

Ya jaddada cewa da zarar lauyoyin jaridar sun kammala bincike, za su maka kakakin tsohon ministan a kotu don a bi masu kadin wannan 'kage.'

Jaridar Premium Times za ta yi karar hadimin tsohon minista da ya yi murabus
Hoton wasu shafukan jaridar Premium Times. Hoto: @PremiumTimesng
Source: UGC

Gwamnatin Enugu ta karyata zargin Ngwu

A wani martani na daban, gwamnatin jihar Enugu ta nesanta kanta daga zargin cewa ta biya jaridar kuɗi don gudanar da binciken.

Daraktan yada labarai na ma’aikatar sadarwa ta jihar, Chukwuemeka Nebo, ya ce:

“Gwamnatin Enugu ba ta da wani hannu cikin wannan lamari. Abin da ya fi dacewa shi ne tsohon ministan ya kare sunansa kawai.”

Bayan rikicin ya yi ƙamari, Uche Nnaji ya aika da takardar murabus dinsa daga kujerar minista a ranar Talata, abin da ya ƙara jawo ce-ce-ku-ce kan lamarin.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu da ake zargi da takardun bogi ya fadi dalilinsa na ajiye aiki

Nnaji: Dalilin minista na yin murabus

A wani labarin, mun ruwaito cewa, ministan kimiyya da fasaha, Uche Nnaji da ya yi murabus daga mukaminsa ya kore shakku a kan dalilin ajiye aiki.

A makon da ya gabata ne aka fitar da rahoto da ke nuna cewa Nnaji na amfani da takardun kammala karatu na bogi daga jami'ar UNN.

Bayan ajiye aiki, Nnaji ya ce barin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ba ya nufin ya amsa zargin da ake yi masa na amfani da takardun karatun bogi ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com