Wata Sabuwa: Za a Rika Biya wa Talabijin da Radiyo Haraji, Jama'a Sun Fara Korafi

Wata Sabuwa: Za a Rika Biya wa Talabijin da Radiyo Haraji, Jama'a Sun Fara Korafi

  • Mazauna yankin kwaryar birnin tarayya Abuja (AMAC) sun nuna rashin amincewa da harajin talabijin da radiyo da aka dawo da shi
  • Wasu sun ce bai dace a dawo da maganar ba a irin wannan lokaci da ake ciki saboda tattalin arzikin ƙasa na cikin mawuyacin hali
  • Hukumar AMAC ta ce harajin yana bisa dokar kasa kuma an daɗe da kafa shi, amma yanzu ne aka fara aiwatarwa da shi da kyau

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Wasu mazauna Abuja sun yi watsi da sabon tsarin da hukumar birnin Abuja (AMAC) na dawo da karɓar haraji kan masu talabijin da radiyo.

Sun bayyana cewa dokar ta zo a lokacin da bai dace ba, kasancewar mutane da dama ke fama da matsin tattalin arziki da hauhawar farashi.

Kara karanta wannan

Kano: 'Dan jarida ya debo ruwan dafa kansa, ICPC ta kama shi kan zambar N14m

Ministan Abuja, Nyesom Wike
Hoton ministan Abuja da radiyo da talabijin. Hoto: Nyesom Ezonwo Wike
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa an tura takardun bukatar biyan harajin zuwa gidaje da wuraren kasuwanci, abin da ya tayar da kura a kafafen sada zumunta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Harajin da za a biyawa talabijin da radiyo

Takardar bukatar biyan kudin harajin ta bai wa mazauna kwanaki 21 kacal su biya, idan ba haka ba za su fuskanci hukunci ko a rufe wuraren kasuwancinsu.

Dokar ta tanadi cewa duk wanda ya mallaki talabijin, rediyo ko makamantansu, ya biya harajin shekara-shekara bisa nau’in wurin da yake.

Babban kamfani zai biya harajin N1,000,000, matsakaitan kamfanoni tsakanin N50,000 zuwa N200,000, yayin da gidaje za su biya daga N3,500 zuwa N20,000.

Mazauna Abuja sun yi watsi da harajin

Wasu mazauna AMAC sun bukaci a dakatar da tsarin harajin, suna kiran shi “ba daidai ba” da “zalunci.”

Wani ɗan kasuwa, John Achungu, ya bayyana cewa bai ga dalilin da zai sa a karɓi haraji kan talabijin da mutane ke amfani da shi ba.

Kara karanta wannan

Ana batun kisan kiyashin Kiristoci, CAN ta aika sako ga gwamnatin tarayya

Haka kuma, wata mai sayar da abinci a Wuse, Zainab Muhammad, ta koka da cewa an umurce ta da ta biya kudin cikin kwanaki 21.

Wani mazaunin Jabi, Samson Isah, ya ce tsarin ya zama kamar wulakanci ne ga talakawa da ke fafutukar rayuwa, yayin da wasu suka yi kira da a janye dokar gaba ɗaya.

Ra’ayoyin masana da sauran jama’a

Wani mai sharhi kan al’amuran jama’a, Toyin Ajayi, ya bukaci a wayar da kai kafin fara karɓar kudin harajin.

Ya ce wajibi ne a fayyace irin na’urorin da ake nufi da “na’urorin lantarki” don kaucewa cin zarafi daga jami’ai masu karbar harajin.

Ajayi ya ce dole ne hukumar ta bayyana yadda za a yi amfani da kudin da za a tara, don tabbatar da gaskiya da amincewar jama’a.

Ministan Abuja, Nyesom Wike
Ministan Abuja na magana a wani taro. Hoto: Nyesom Ezonwo Wike
Source: Facebook

Tun a kwanakin baya Punch ta wallafa cewa, hukumar AMAC ta ce dokar tana kan tsari kuma za a cigaba da karbar harajin.

Kakakin hukumar, Emmanuel Inyang, ya bayyana cewa an daɗe da kafa dokar amma ba a aiwatar da ita yadda ya kamata ba a baya.

Kara karanta wannan

NYSC: Jerin ministoci 6 da suka shiga badakalar takardun bogi a Najeriya

Wata mai amfani da sunan Bingel Baba'am a shafin X ta tabbatar da cewa an bukaci su biya harajin, kuma har an kawo masu takarda.

Atiku ya nemi a binciki Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya nemi a binciki shugaba Bola Tinubu da ministocinsa.

Atiku ya yi magana ne yayin da ministan kimiyya na kasa, Uche Nnaji ya yi murabus kan zargin mallakar takardun bogi.

Baya ga haka, Atiku ya yi Allah wadai da yadda aka bar ministan ya yi murabus maimakon a bincike shi kan zargin da aka masa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng