Akpabio Ya Yi Wa Jam'iyyun Adawa Shagube a Zauren Majalisa
- Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta kara yawan Sanatocin da take da su a majalisar dattawa
- Hakan na zuwa ne bayan sanataocin APC sun samu rinjaye da kaso biyu bisa uku a majalisar dattawan
- Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya yi wa jam'yyun adawa shagube kan yadda mambobinsu ke komawa APC
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya yi wa jam'iyyun adawa shagube.
Sanata Akpabio ya nuna cewa jam'iyyun adawa suna cikin wani hali duba da yadda mambobinsu ke komawa jam'iyyar APC mai mulki.

Source: Facebook
Me Akpabio ya ce kan jam'iyyun adawa?
Jaridar The Punch ta ce Sanata Akpabio, ya bayyana hakanne yayin sauya shekar Sanata Kelvin Chukwu daga jam’iyyar LP zuwa APC mai mulki.
Sanata Chukwu, wanda ke wakiltar yankin Enugu ta Gabas, ya bayyana sauya shekarsa yayin zaman majalisar na ranar Laraba, yana mai cewa rikice-rikicen cikin gida na LP ne suka tilasta masa daukar wannan mataki.
Sauya shekar tasa ta kara yawan Sanatocin APC a Majalisar Dattawa ta 10 zuwa mutum 73, wanda hakan ya sa jam’iyyar ta samu rinjaye da kaso biyu bisa uku.
Da yake mayar da martani, Akpabio ya yi wa jam’iyyun adawa shagube, yana mai cewa yawan sauya shekar da ake samu daga cikinsu, alamar rikici da rarrabuwar kai ne.
"Ina son mu samu adawa mai karfi da kuzari a Najeriya. Amma idan suka kasa shirya kansu, jam’iyyunsu kuma suka tarwatse, abin da ya dace su yi shi ne su zo su haɗu da mu, mu tafi tare don gina kasa."
"Ba za mu yi tsarin jam’iyya ɗaya ba. Shi ya sa INEC ke ci gaba da rajistar sababbin jam’iyyu. Don Allah, ku gyara gidanku. Na lura yadda kuke raguwa kullum, kuma ina tausayin abin da ke faruwa da ku."
"PDP ta durƙushe, laima ta yage. LP ta tarwatse. An daina labarin Accord Party, ADC ma ta mutu tun kafin ta je ko ina."
- Sanata Godswill Akpabio
Akpabio ya kuma taya Sanatocin APC murna bisa samun sabuwar kujera daga Enugu.

Kara karanta wannan
Majalisar Dattawa ta rantsar da sababbin sanatoci daga jihohi 2, an jero sunayensu

Source: Facebook
Shugaban marasa rinjaye ya yi martani
Sai dai, shugaban marasa rinjaye na majalisar, Sanata Abba Moro bai ji daɗin kalaman ba, inda ya mayar da martani, yana mai cewa ‘yan adawa ba su karaya ba duk da sauya shekar da ake yi, rahoton Vanguard ya tabbatar da labarin.
"Ina so na fada bisa girmamawa cewa kai ne shugaban majalisar dattawan Tarayyar Najeriya, kuma ina girmama ka, ranka ya daɗe.
"Amma duk da wasu nasarori da shugaban kasa ya samu, ina so na jaddada cewa, komai karancinmu, muna da karfin tsayawa da kanmu."
- Sanata Abba Moro
An rantsar da sababbin Sanatoci a majalisa
A wani labarin kuma, kun ji cewa an rantsar da wasu sababbin Sanatoci a majalisar dattawan Najeriya.
Majalisar dattawan ta rantsar da sababbin sanatoci biyu, Sanata Joseph Ikpea da Sanata Emmanuel Nwachukwu.
Sababbin sanatocin guda biyu da aka rantsar za su maye gurbin kujerun da suka kasance babu kowa a kai.
Asali: Legit.ng
