Manhajar WhatsApp Za Ta Canza Tsarin Hira, Za a Daina Amfani da Lambar Waya

Manhajar WhatsApp Za Ta Canza Tsarin Hira, Za a Daina Amfani da Lambar Waya

  • Manhajar WhatsApp da ke karkashin kamfanin Meta na shirin kawo sauyi a tsarin amfani da lambobin waya wajen hira da mutane
  • Kafar sada zumuntar na shirin canza amfani da lambobin waya wajen haduwa da mutane zuwa amfani da suna watau 'username'
  • Sai dai wannan canji da manhajar ke shirin kawo wa yana kan gwaji amma ana sa ran da zaran ya tsallake matakin za a fara amfani da shi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Masu amfani da manhajar sada zumunta ta WhatsApp na shirin fara ganin sababbin sauye-sauye da nufin inganta kafar.

Bayanai sun nuna cewa WhatsApp na gwada sabon sauyi da zai ba masu amfani manhajar damar haɗuwa da tattaunawa ba dole sai da lambobin wayar juna ba.

Whatsapp.
Hoton tambarin manhajar sada zumunta ta WhatsApp. Hoto: Getty Images
Source: UGC

A wani rahoto da Vanguard ta wallafa, WhatsApp na shirin canza tsarin amfani da lambar waya wajen haduwa da mutane.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace mutane yayin da 'yan sanda suka kashe miyagu a Zamfara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauyin da ake shirin kawo wa a WhatsApp

Maaimaikon haka, masu amfani da WhatsApp za su iya ƙirƙirar suna na musamman watau "username" irin yadda ake yi a Instagram, Telegram ko X.

Rahotanni sun nuna cewa kawo tsarin amfani da sunaye yana daga cikin manyan sauye-sauyen tsare sirri da manhajar ta WhatsApp ke shirin aiwatarwa.

Wannan tsarin, wanda aka hango a shirin gwajin beta na WhatsApp, zai ba mutane damar yin hira da shiga dandali ta amfani da sunaye na musamman maimakon lambobin waya.

Dalilin WhatsApp na kawo tsarin suna

Manufar ita ce kara tsare bayanai da sirrin masu amfani da kafar sada zumuntar, da kuma saukaka wa masu manyan shafuka da wadanda suka bude dandali.

A cewar rahoton, tsarin zai kara ba yan kasuwa dama gudanar da kasuwancin su a WhatsApp cikin sauki, inda wasu ke ganin nemo lambobin waya na da cin rai.

Hotunan da suka fito game da sabon tsarin sun nuna filin saka 'username' a cikin bayanan mutum, wanda zai ba kowa damar zaɓar sunan da zai rika amfani da shi da ɓoye lambar wayarsa idan ya ga dama.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tare babbar hanya a Zamfara, sun sace shugaban majalisar Malamai

Kalubalen da za a iya fuskanta

Duk da dai wannan sabunta tsari na iya sa WhatsApp ta fi zama dandalin sada zumunta, akwai damuwa game da yiwuwar yin amfani da sunayen bogi ko kuma ɓatanci.

Ana sa ran WhatsApp zai ƙaddamar tsarin tantancewa don dakile irin wannan tunani mara kyau, in ji rahoton Times of India.

Manhajar WhatsApp.
Hoton wurin hira a Manhajar WhatsApp. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Sai dai bayanai sun tabbatar da cewa tsarin amfani da suna, na nan har yanzu cikin gwaji, Idan ya yi nasara, zai iya sauya yadda sama da mutane biliyan biyu ke hulɗa a WhatsApp.

An maka Facebook da X a gaban kotun Abuja

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamnatin Tarayya ta maka kafafen sada zumunta na X da Facebook a gaban kotun kan rubutun da dan gwagwarmaya, Omoyele Sowore ya yi.

Sawore, tsohon dan takarar shugaban kasa ya fusata gwamnatin Najeriya ne bayan ya caccaki Shugaha Bola Tinubu a shafukansa na X da Facebook.

Kara karanta wannan

Labari ya fara sauyawa: Malami ya fadi shirin Ahlus Sunnah kan zaben 2027 a Kano

Gwamnati ta gurfanar da su gaba ɗaya da tuhumar laifuffuka guda biyar a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja a ranar Talata 16 ga watan Satumbar 2025.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262