Bankin Duniya: 'Abin da Ya Jawo Ƴan Najeriya Miliyan 139 Ke Rayuwa cikin Talauci'

Bankin Duniya: 'Abin da Ya Jawo Ƴan Najeriya Miliyan 139 Ke Rayuwa cikin Talauci'

  • Bankin Duniya ya ce mutane miliyan 139 a Najeriya ke rayuwa cikin talauci duk da ci gaban da aka samu a gyaran tattalin arziki
  • An yabawa Shugaba Bola Tinubu kan cire tallafin mai da sauyin musayar kudi, amma an nemi ya maida hankali kan rayuwar talakawa
  • Bankin Duniya dai ya yi gargadi cewa hauhawar farashin abinci na iya kawo barazana ga ci gaban sauye-sauyen gwamnatin tarayya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Najeriya – Babban Bankin Duniya ya bayyana cewa sama da ’yan Najeriya miliyan 139 na rayuwa cikin talauci a halin yanzu.

Bankin ya ce wannan ya faru duk da cewa tattalin arzikin ƙasar ya fara nuna alamun murmurewa sakamakon sababbin tsare-tsaren gwamnati.

Bankin Duniya ya ce 'yan Najeriya miliyan 139 ke rayuwa a cikin talauci
Wasu mata da 'ya'yansu na zaune a sansanin 'yan gudun hijira na Durumi da ke Abuja. Hoto: Anadolu / Contributor
Source: Getty Images

A cewar bankin, tattalin arzikin Najeriya na nuna alamun farfaɗowa, amma sauye-sauyen da gwamnati ta aiwatar bai kai ga isa ga mafi yawan al’umma ba tukuna, inji rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

AfDB: Tinubu zai karbi sabon rancen Naira biliyan 733, za a yi aiki a bangarori 3

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amfanin sauye-sauyen gwamnatin Tinubu

Yayin ƙaddamar da rahoton ci gaban Najeriya (NDU) a Abuja ranar Laraba, daraktan Bankin Duniya a Najeriya, Mathew Verghis, ya yaba wa gwamnati bisa ɗaukar matakan sauye-sauye masu ƙarfi, musamman a fannin musayar kudi da cire tallafin man fetur.

Mathew Verghis ya ce:

“A cikin shekaru biyu da suka gabata, Najeriya ta aiwatar da sauye-sauye masu muhimmanci — musamman a kan tsarin musayar kudi da cire tallafin man fetur.
"Wadannan matakai da gwamnati ta dauka sun shimfiɗa tubalin sauya tsarin tattalin arzikin Najeriya na shekaru masu zuwa.”

Mathew Verghis ya kara da cewa gyare-gyaren sun fara nuna sakamako, inda ake ganin karin kudaden shiga, ingantaccen tsarin bashi, daidaituwar kasuwar canjin kudi, da kuma karuwar ajiya a Babban Bankin Najeriya (CBN).

'Yan Najeriya miliyan 139 na cikin talauci

Duk da wannan ci gaban, Bankin Duniya ya bayyana cewa har yanzu yawancin ’yan ƙasar Najeriya ba su amfana da wani sauyin rayuwa mai kyau ba.

Kara karanta wannan

Mutane za su amfana da Najeriya ta fara shirin karbo bashin tiriliyoyin Naira daga China

“A shekarar 2025, mun kiyasta cewa ’yan Najeriya miliyan 139 ne ke rayuwa cikin talauci.
“Kalubalen yanzu shi ne yadda za a isar da nasarorin da aka samu daga matakan gwamnati zuwa ga ci gaban rayuwar kowa da kowa.”

- Mathew Verghis.

Vanguard ya ruwaito cewa, Rahoton NDU ya fitar da dabaru guda uku da za su taimaka wa gwamnati wajen kawo sauyi kai tsaye ga al’umma:

  • Rage hauhawar farashin kaya (musamman na abinci),
  • Inganta yadda ake kashe kuɗaɗen gwamnati cikin inganci,
  • Da kuma faɗaɗa tsarin tallafin jin kai.
Bankin Duniya ya ce 'yan Najeriya miliyan 139 ke rayuwa a cikin talauci
Hoton 'yan Najeriya a kan titi da ginin hedikwatar Bankin Duniya. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Hauhawar farashi na barazana ga cigaba

Mathew Verghis ya jaddada cewa hauhawar farashin abinci na daga cikin manyan matsalolin da ke rage amincewar jama’a ga sauye-sauyen tattalin arziki.

“Hauhawar farashin abinci na shafar kowa, musamman talakawa, kuma na iya rage goyon bayan jama’a ga manufofin gwamnati."

- Mathew Verghis.

Verghis ya tabbatar da cewa Bankin Duniya zai ci gaba da tallafawa Najeriya ta hanyar shawarwari, horo, da kuma tallafin kuɗi, domin tabbatar da cewa amfanin gyare-gyaren tattalin arziki ya isa ga kowane gida.

Kara karanta wannan

Shettima ya ba da mamaki da ya kira Sanusi II da Sarkin Kano a taro a Abuja

Najeriya ta zama kasa ta 2 mafi yawan talakawa

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Najeriya ta zama kasa ta biyu bayan kasar India da ke da yawan mutane masu rayuwa a cikin talauci a duniya.

Tsohon shugaban hukumar NBS, Yemi Kale ne ya bayyana haka a wurin wani taro da aka shirya ranar cikar Najeriya shekara 65 da samun yancin kai.

A cewar Yemi Kale, kamata ya yi a ce Najeriya ta wuce matakin da take a yanzu tun shekaru 10 da suka wuce, amma har yanzu talaucin bai ragu ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com