Ana Batun Kisan Kiyashin Kiristoci, CAN Ta Aika Sako ga Gwamnatin Tarayya

Ana Batun Kisan Kiyashin Kiristoci, CAN Ta Aika Sako ga Gwamnatin Tarayya

  • Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) ta nuna damuwa kan hare-haren da ake kai wa al'ummomin Kirista
  • CAN ta nuna cewa ta dade tana ankarar da kasashen duniya ta'addancin da ke ritsawa da mabiya addinin Kirista
  • Kungiyar ta bukaci gwamnatin tarayya da ta dauki matakan gaggawa domin kare rayuka da dukiyoyin 'yan Najeriya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) ta yi kira da babbar murya ga gwamnatin tarayya.

Kungiyar CAN ta bukaci gwamnatin tarayya da ta dauki ingantaccen mataki cikin gaskiya da adalci domin dakile hare-haren da ake kai wa al’ummomin Kirista tare da gurfanar da masu aikata laifin a gaban shari’a.

CAN ta aika sako ga gwamnatin tarayya
Shugaba Bola Tinubu tare da shugabannin kungiyar CAN. Hoto: @DOlusegun
Source: Facebook

Jaridar Leadership ta ce wannan kiran na cikin wata sanarwa da shugaban CAN na kasa, Archbishop Daniel Okoh, ya sanyawa hannu a ranar Laraba, 8 ga watan Oktoban 2025.

Kara karanta wannan

Zargin kisan Kiristoci: Kungiyar CAN ta fadi matsayarta kan rade radin a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar CAN ta damu kan kashe-kashe

Ya fitar da sanarwar ne dangane da karuwar rashin tsaro da kuma batun rikice-rikice masu nasaba da addini a kasar nan.

Archbishop Okoh ya bayyana cewa kungiyar ta bibiyi tattaunawar da ake yi a kasa cike da damuwa, yana mai jaddada bukatar a yi magana cikin gaskiya, tausayi, da natsuwa, musamman a irin wannan lokaci mai sarkakiya.

“CAN ta tabbatar da cewa al’ummomin Kirista da dama a wasu sassan Najeriya, musamman a Arewa, sun fuskanci hare-hare masu muni, rasa rayuka, da rushe majami’u."

- Archbishop Daniel Okoh

Ya bayyana cewa waɗannan abubuwan da ke faruwa, suna nuna bukatar gwamnati da jami’an tsaro su dauki matakan gaggawa don kare kowane ɗan kasa.

Shugaban na CAN ya kuma bayyana cewa kungiyar ta dauki tsawon shekaru tana jawon hankalin kasashen duniya kan cin zarafi da kisan da ke da nasaba da addini, rahoton Daily Post ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Majalisar wakilai za ta kafa dokoki kan POS da Kirifto a Najeriya

Ya bayyana cewa har wasika sun taba rubutawa zuwa kotun duniya ta ICC da ke Hague.

Sai dai ya nuna bakin ciki cewa duk waɗannan kokarin da suka yi, hakan bai haifar da sakamako mai gamsarwa ba daga hukumomi.

Wane sako CAN ta ba gwamnatin tarayya?

“Har yanzu damuwarmu ita ce, yawancin kukanmu na neman adalci da kariya, ba a daukar sa da muhimmanci."
"Muna sake kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su dauki matakai cikin gaggawa, gaskiya da adalci domin kawo karshen kashe-kashe, kare al’ummomin Kirista masu rauni, tare da tabbatar da cewa masu laifi sun fuskanci hukunci."

- Archbishop Daniel Okoh

Archbishop Okoh ya jaddada cewa wadannan hare-haren ba kawai alkaluma ba ne, amma labaran rayuka ne da suka salwanta da iyalai da suka tarwatse saboda tashin hankali.

CAN ta bukaci a kawo karshen kisan Kiristoci a Najeriya
Shugaban kungigar CAN na kasa, Archbishop Daniel Okoh. Hoto: Christian Association of Nigeria
Source: Twitter

Duk da cewa CAN ta yaba da kokarin gwamnati wajen magance matsalar tsaro, ta bukaci a kara azama da daidaito wajen kare kowa, tare da tabbatar da gurfanar da masu laifi a bainar jama’a.

CAN ta magantu kan kisan Kiristoci

Kara karanta wannan

Ana barazanar shigar da gwamnoni 36 da Wike kotu kan kudin tallafin mai

A wani labarin kuma, kun ji cewa kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) ta yi magana kan rade-radin ana yi wa Kiristoci kisan kiyashi a kasar nan.

Kungiyar CAN ta musanta rahotannin da ake yadawa masu nuna cewa ana yi wa Kiristoci kisan kare dangi a Najeriya.

CAN ta bayyana cewa hare-haren da ake yi a Najeriya ba su da tsarin addini, inda ta ce har Musulmi ana kashewa yayin sallar Asuba ko a masallatai.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng