'Yan Bindiga Sun Sace Mutane yayin da 'Yan Sanda Suka Kashe Miyagu a Zamfara

'Yan Bindiga Sun Sace Mutane yayin da 'Yan Sanda Suka Kashe Miyagu a Zamfara

  • 'Yan bindiga dauke da makamai sun tattara wasu mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba a jihar Zamfara
  • Miyagun sun yi awon gaba da mutanen ne bayan sun kai wani harin ta'addanci a karamar hukumar Bukkuyum ta jihar
  • Jami'an tsaro sun fara kokarin gano sun kubutar da mutanen da aka sace domin dawo da su ga iyalansu cikin aminci

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Zamfara - Wasu ‘yan bindiga dauke da makamai sun sace mutane 30 yayin wani a jihar Zamfara.

'Yan bindigan sun yi awon gaba da mutanen ne lokacin da suka kai wani hari a kauyen Zamfarawa, da ke gundumar Zugu cikin karamar hukumar Bukkuyum ta jihar Zamfara.

'Yan bindiga sun sace mutane a Zamfara
Jami'an 'yan sanda a bakin aiki. Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tare babbar hanya a Zamfara, sun sace shugaban majalisar Malamai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane

Harin ya faru ne a ranar Talata, 7 ga watan Oktoba 2025, da misalin karfe 2:20 na rana, lokacin ‘yan bindigan suka yi dirar mikiya cikin kauyen.

'Yan bindigan wadanda suka zo da yawa, sun rika harbe-harbe don tsoratar da mazauna garin.

An ce maharan sun yi awon gaba mutane 30 zuwa wani wuri da ba a sani ba.

Bayan faruwar lamarin, jami’an tsaro sun kara tsaurara matakan bincike domin gano inda aka kai waɗanda aka sace tare da kokarin ceto su cikin koshin lafiya.

'Yan sandan Zamfara sun kashe 'yan bindiga

A wani ɓangaren kuma, rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da kashe wasu ‘yan bindiga biyu.

An kashe 'yan bindigan ne yayin musayar wuta tsakanin jami’an tsaro da miyagu a gundumar Mada, da ke karamar hukumar Gusau.

Majiyoyi sun bayyana cewa samun sahihan bayanan sirri sun taimaka wajen gano shirin ‘yan bindigan na kai hari a wasu kauyuka da ke yankin Mada.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sake ta'addanci a Kwara, an sace basarake da kashe mutane

A cewar rahoton, da misalin karfe 3:10 na safe a ranar 7 ga Oktoba, hadakar jami’an ‘yan sanda na musamman, jami'an rundunar CPG da mafarauta sun kai samame a kauyen Fegin Mahe, inda suka yi kwanton ɓauna a kan hanyar da ake zargin ‘yan bindigan za su bi.

'Yan sanda sun kashe 'yan bindiga a Zamfara
Taswirar jihar Zamfara, tarayyar Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Lokacin da ‘yan bindigan guda uku suka iso wurin, sai jami’an tsaron suka buɗe musu wuta, inda aka kashe biyu daga cikinsu, na uku kuma ya gudu da dauke raunin harbin bindiga.

Rundunar ‘yan sanda ta ce ana ci gaba da bincike domin cafke wanda ya tsere tare da tabbatar da tsaron yankin gaba ɗaya.

'Yan bindiga sun yi ta'asa a jihar Zamfara

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun 'yan bindiga sun kai mummunan hari a jihar Zamfara.

'Yan bindigan sun yi kisa tare da sace mutane masu yawa bayan sun tare matafiya a hanyar Mayanchi-Anka da yammacin ranar Juma'a.

Miyagun 'yan bindigan wadanda ke dauke da mugayen makamai, sun tare hanyar sannan kuma suka kashe mutane da yin awon gaba da wasu zuwa cikin daji.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng