Majalisar Dattawa Ta Rantsar da Sababbin Sanatoci daga Jihohi 2, An Jero Sunayensu

Majalisar Dattawa Ta Rantsar da Sababbin Sanatoci daga Jihohi 2, An Jero Sunayensu

  • Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya jagoranci rantsar da sababbin sanatoci daga jihohin Edo da Anambra
  • Sanatocin guda biyu za su maye gurbin Gwamna Monday Okpebholo na jihar Edo da Marigayi Sanata Ifeanyi Ubah, wanda ya rasu a 2024
  • Akpabio ya ja hankalin sababbin Sanatocin da su zama masu bin dokoki da ka'idojin Majalisar wajen gudanar da ayyukansu na wakilcin jama'a

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Majalisar Dattawan Najeriya ta samu karin mambobi biyu da za su cike guraben da babu kowa a kai.

A zamanta na yau Laraba, 8 ga watan Oktoba, 2025, Majalisar Dattawa ta rantsar da sababbin sanatoci biyu, Sanata Joseph Ikpea da Sanata Emmanuel Nwachukwu.

Majalisar Dattawan Najeriya.
Hoton zauren Majalisar Dattawan Najeriya lokacin da sanatoci ke tsakiyar zama. Hoto: @NGRSenate
Source: Facebook

Sababbin sanatoci 2 da guraben da suka cike

Jaridar Punch ta tattaro cewa Sanata Joseph Ikpea shi ne zai wakilci kujerar mazabar Edo ta Tsakiya, wacce ta rasa wakilci bayan murabus din Monday Okpebholo wanda ya zama gwamnan Edo.

Kara karanta wannan

Amupitan: Farfesa daga jami'ar Jos na dab da zama sabon shugaban hukumar INEC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai kuma Sanata Emmanuel Nwachukwu, wanda zai wakilci Anambra ta Kudu, ya maye gurbin marigayi Sanata Ifeanyi Ubah, wanda ya rasu a watan Yulin shekarar 2024.

Tashar Channels TV ta ruwaito cewa an gudanar da rantsuwar ne a zauren majalisar a zaman yau Laraba karkashin jagorancin Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio.

Yadda aka rantsar da sababbin sanatoci 2

Magatakardar Majalisar Dattawa, Emmanuel Ojo, ne ya karanta musu rantsuwar kama aiki da biyayya kuma suka maimaita kamar yadda doka ta tanada.

Wannan ci gaban ya biyo bayan zabukan cike gurbi da aka gudanar kwanan nan domin cike guraben kujeru guda biyu da suka zama babu kowa a Majalisar Dattawa.

Kafin bikin rantsuwar, majalisar ta dakatar da wasu dokokinta na cikin gida na dan lokaci domin ba wa iyalai da baƙi masu daraja damar shiga zauren domin shaida lamarin.

Daga cikin wadanda suka halarta akwai tsohon Gwamnan Jihar Delta, James Ibori; tsohon Mataimakin Gwamnan Edo kuma Darakta-Janar na Hukumar Wasannin Najeriya (NIS), Philip Shaibu; da kuma wasu manyan ‘yan siyasa.

Kara karanta wannan

Yadda shugaban majalisa ya ceto shugaban marasa rinjaye daga yunkurin tsige shi

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio.
Hoton Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio. Hoto: @NGRSenate
Source: Facebook

Sanata Akpabio ya ja hankalin sanatoci

Da yake jawabi, Sanata Akpabio ya shawarci sababbin sanatoci da su koyi dokokin majalisar tare da bin su wajen gudanar da ayyuka bisa ka'ida da doka.

Idan ba ku manta ba, sababbin sanatocin sun samu nasara ne a zaben cike gurbin da hukumar INEC ta shirya kuma ta gudanar ranar 16 ga watan Agusta, 2025.

Da wannan rantsuwa da 'yan Majalisar biyu suka yi, yanzu majalisar dattawan Najeriya ta cika cifa ma'ana tana wakilci a kujerunta 109 baki ɗaya.

Jawabin Akpabio bayan dawowa hutun Sanatoci

A wani rahoton, kun ji cewa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya ce Majalisa ta 10 za ta ci gaba da zama mai gaskiya da amsa bukatun jama’a kai tsaye.

Sanata Akpabio ya fadi haka ne a zama. majalisarna farko bayan dawowa daga hutun shekara ranar Talata, 7 ga watan Oktoba, 2025.

Ya bukaci ‘yan majalisa su mayar da hankali kan gyaran tattalin arziki, ilimi, kiwon lafiya, da rage tsadar rayuwa a kasar nan.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262