Hukumar EFCC Ta Gayyaci Shugaban NAHCON kan Zargin Karkatar da N50bn

Hukumar EFCC Ta Gayyaci Shugaban NAHCON kan Zargin Karkatar da N50bn

  • Hukumar EFCC na binciken shugaban NAHCON, Farfesa Saleh Abdullahi Usman, bisa zargin karkatar da kudi a Hajjin 2025
  • Rahotanni sun nuna cewa ana zargin an karkatar da sama da Naira biliyan 50 wajen kwangiloli da tafiye-tafiye ba bisa ka’ida ba
  • Hakan na zuwa ne bayan gayyatar wasu jami'an hukumar alhazai da EFCC ta yi a kwanakin baya kan zargin almundahana

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta gayyaci shugaban Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON), Farfesa Saleh Abdullahi Usman.

Rahotanni sun nuna cewa an gayyace shi ne bisa zargin karkatar da kudi da suka kai sama da Naira biliyan 50 da suka shafi shirye-shiryen aikin Hajjin 2025.

Farfesa Abdullahi Saleh Usman na NAHCON
Shugaban hukumar NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman. Hoto: Jibwis Nigeria
Source: Facebook

The Guardian ta rahoto cewa Farfesa Usman ya bayyana kansa a ofishin EFCC da ke Abuja bayan samun takardar gayyata daga hukumar domin amsa tambayoyi kan zargin.

Kara karanta wannan

Kotu ta rufe asusun kamfanin jiragen sama kan zargin hannu a badakalar NNPCL

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan bincike na farko, an sallame shi amma an umurce shi da ya rika kai kansa ofishin har zuwa lokacin kammala bincike.

Ana zargin karkatar da N50bn a HAHCON

Binciken da EFCC ke gudanarwa na da nufin gano gaskiya kan zargin da ya shafi karkatar da makudan kudi da suka kai fiye da Naira biliyan 50 daga asusun NAHCON.

Daga cikin kudin da ake zargi an karkatar akwai Naira biliyan 25 da aka kashe wajen biyan haya da gina tantuna a Saudiyya.

Haka zalika akwai Naira biliyan 7.9 na masauki, da kuma Naira biliyan 1.6 da aka kashe wajen tafiye-tafiyen iyalan jami’an hukumar.

Majiyoyi daga cikin gwamnati sun ce an kuma tsare kwamishinan NAHCON mai kula da kudi, Aliu Abdulrazak, da daraktan kudi, Aminu Y. Muhammed a baya.

Daily Nigerian ta rahoto cewa an tsare su ne saboda zargin cewa suna cikin wadanda suka taimaka wajen almundahanar.

Kara karanta wannan

Dangote ya rage kudin gas na girki, ’yan kasuwa za su daidaita farashi

NAHCON ta ce za a yi binciken gaskiya

A wani zama da majalisar wakilai ta gudanar a baya, Farfesa Usman ya amince cewa akwai abubuwa marasa dadi da suka faru a hukumar.

Sai dai shugaban ya yi alkawarin tallafa wa duk wani bincike domin tabbatar da gaskiya da rikon amana.

A cikin wata sanarwa, hukumar NAHCON ta ce ba za ta kare kowa da aka samu da laifi ba, tana mai bayyana shirinta na yin aiki kafada da kafada da hukumomin bincike.

Da aka tuntube shi, kakakin hukumar EFCC, Dele Oyewale, ya ce za su mayar da martani daga baya, sai dai har zuwa lokacin da aka buga labarin, bai bayar da amsa ba.

Jami'an NAHCON a ofis
Shugaban NAHCON da wasu jami'ansa suna tattaunawa a Abuja. Hoto: NAHCON
Source: Twitter

Hukumar NAHCON ta yabi Tinubu da Shettima

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar alhazai ta kasa ta yaba wa gwamnatin Najeriya karkashin shugaba Bola Tinubu kan rage kudin Hajjin 2026.

A wata sanarwar da hukumar ta fitar, NAHCON ta yaba wa mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima kan gudumawar da ya bayar.

Kara karanta wannan

Yadda gwamnatin Abba ta shirya kashe N1.6bn don auren gata a jihar Kano

Shugaba Bola Tinubu ya yi umarni da a rage kudin kujerar aikin Hajjin 2026, kuma a yanzu haka ana kokarin jin yadda kudin zai kasance a bana.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng