Rikicin Dangote PENGASSAN: Sanusi II Ya Bayyana Matsaya, Sarki Ya Fadi Silar Rigimar
- Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya tofa albarkacin bakinsa kan rikicin matatar Dangote da kungiyar PENGASSAN
- Sanusi II ya bayyana cewa matatar man Dangote muhimmiyar kadara ce ga Najeriya wadda ya zama dole a ba ta kariya
- Sarkin ya nuna cewa dole ne matatar ta fuskanci adawa saboda ta toshe hanyar cin abincin wasu 'yan kasuwa da dama
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya yi magana kan rikicin matatar Dangote da kungiyar manyan ma'aikatan man fetur na kasa (PENGASSAN).
Sanusi II ya bayyana cewa dole ne matatar ta fuskanci adawa saboda ta bata ran wasu 'yan kasuwa da suka saba samun kudi ta wata irin hanyar kasuwanci.

Source: Twitter
Sanusi II ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a tashar News Central Tv.

Kara karanta wannan
Sarki Sanusi II da wasu fitattun 'yan Najeriya sun shiga rikicin Dangote da PENGASSAN
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An yi tattaunawar ne bayan taron tattalin arzikin Najeriya karo na 31 wanda aka gudanar a babban birnin tarayya Abuja.
Me Sanusi II ya ce kan Dangote da PENGASSAN
Sanusi II ya bayyana cewa rikicin ya samo asali ne saboda adawar da wasu 'yan kasuwa suke yi da matatar.
"Abin da ya faru da Dangote abin bakin ciki ne, domin ya tura sako mara kyau ga masu son zuba hannun jari a Najeriya."
"Matatar ta lalata tsarin kasuwanci na masu neman bashi, wannan ne dalilin da ya sa take fuskantar adawa."
"Ba wai maganar 'yanci ba ne, ba maganar tattalin arziki ba ne, magana ce ta mutanen da suke amfani da wani tsarin kasuwanci shekara 30 zuwa 40, sun ga kwatsam yana kokarin bacewa."
"Mutane ne da suka samu biliyoyi daga wannan kasuwancin, suna karbar tallafi don shigo da fetur wanda ba su shigowa da shi. Suna karbar kudi daga NNPCL a matsayin tallafi."
"Suna karbar kudi a yanayin da akwai nuku-nuku a ciki, yanayin da babu gaskiya. Yanzu wannan tsarin ya bace. Za mu zama masu fitar da albarkatun fetur zuwa kasashen waje."
"Za mu rika samar da albarkatun fetur a cikin gida, za mu rika adana kudaden kasashen waje."
- Muhammadu Sanusi II
Sanusi II ya yi magana kan shiga kungiya
Dangane da 'yancin shiga kungiya kuma, Sanusi II ya bayya cewa abu ne wanda yake bai zama dole ba.

Source: Twitter
"Idan direba yana son shiga kungiya, sai ya je ya yi aiki a kamfanin da yake barin ma'aikatansa su shiga kungiya. Idan direba ya zabi kada ya shiga kungiya don yi wa Dangote aiki, sai ya je ya yi aikinsa ga Dangote."
"Bai kamata a tilastawa mutanen da suka zuba kudinsu cewa dole sai sun amince da bukatun kungiyoyi ba. Ina ganin hakan ba daidai ba ne."
- Muhammadu Sanusi II
Sanusi II ya kare kansa kan rama dukan miji
A wani labarin kuma, kun ji cewa sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya fayyace abin da yake nufi kan batun mata su rama idan mazajensu sun doke su.
Sanusi II ya bayyana cewa an yi masa mummunan fahimta saboda ba abin da ake yadawa yake nufi ba a cikin maganganunsa.
Mai martaba Sarkin ya bayyana cewa bai ce mace ta rama duka ko mari idan mijinta ya yi mata hakan ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

