Matar Sojan Najeriya Ta Banka Masa Wuta da Fetur, Ya Mutu har Lahira
- Jami’in soja, Laftanar Samson Haruna, ya rasu bayan wuta da matarsa ta banka masa a yayin sabani da suka yi
- Rahotanni sun ce rikicin ya faru ne a barikin Wellington Bassey, Abak, jihar Akwa Ibom, inda sojoji ke bakin aiki
- A sakan jaje da ta fitar, rundunar sojan Najeriya ta tabbatar da faruwar lamarin tare da kama matar domin bincike
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Akwa Ibom – Rundunar sojan Najeriya ta tabbatar da mutuwar ɗaya daga cikin jami’anta, Laftanar Samson Haruna, wanda matarsa ta kona shi.
An ce matar shi ta kona shi da fetur ne yayin sabani a cikin gidansu da ke barikin Wellington Bassey, Ibagwa, ƙaramar hukumar Abak, jihar Akwa Ibom.

Source: Twitter
Zagazola Makama ya wallafa a X cewa lamarin ya auku ne ranar 22 ga Satumba, 2025, inda rahotanni suka nuna cewa rikicin tsakanin ma’auratan ya kai ga tashin hankali.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mutuwarsa ta jefa barikin sojoji da abokansa cikin alhini, musamman ganin cewa marigayin likita ne da ke aiki a bataliya ta 6.
Yadda mata ta kona mijinta soja
Rahotanni sun bayyana cewa rikicin ya fara ne bayan cacar baki tsakaninsa da matarsa, Retyit Obadiah Dalong Samson.
Leadership ta wallafa cewa a lokacin ne matar ta zuba man fetur a jikinsa sannan ta kunna masa wuta.
Jami’in sojan ya samu kuna mai tsanani kuma an kai shi asibitin rundunar da ke cikin barikin kafin a tura shi zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Uyo.
Duk da kulawar da likitoci suka ba jami'in sojan, Laftanar Samson Haruna ya mutu da sanyin safiyar Talata.
Sojoji sun tabbatar da kona sojan
Rundunar sojan Najeriya ta 2 da ke Uyo ta fitar da sanarwa ta bakin jami'in hulɗa da jama’a, Manjo Lawal Muhammad, inda ta tabbatar da mutuwar Laftanar Haruna.
A cewar sanarwar, an tabbatar da cewa rikicin cikin gida ne ya haddasa faruwar lamarin, wanda ya kai ga konewar gidansu da lalacewar wasu kayayyaki.
Sanarwar ta ce rundunar ta mika sakon ta’aziyya ga iyalan marigayin da abokan aikinsa, tana mai cewa za ta tabbatar da cewa an gudanar da cikakken bincike.

Source: Facebook
Matar sojan ta shiga hannun hukuma
A halin yanzu, rundunar sojan ta tabbatar da cewa an kama matar mamacin, kuma tana tsare yayin da ake gudanar da bincike kan lamarin.
Punch ta wallafa cewa sojoji sun yi gargadin cewa ba za su lamunci duk wani nau’i na tashin hankali ko aikata laifi daga jami’anta ko iyalansu ba.
Rundunar ta ce za ta ci gaba da kula da iyalansa yayin da ake shirin gudanar da jana’izarsa bayan kammala bincike.
Sojoji sun fatattaki 'yan ta'adda a Taraba
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar sojin Najeriya ta yi arangama da wasu 'yan ta'adda a jihar Taraba.
Rahotanni sun bayyana cewa an rasa rayuka yayin da aka yi kazamin fada tsakanin 'yan ta'adda da dakarun Najeriya.
Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa hakan na cikin kokarin jami'anta wajen kawar da bata gari a fadin kasar nan.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

