Rigiji Gabji: Atiku Ya Nemi a Binciki Tinubu da Ministocinsa kan Takardun Bogi

Rigiji Gabji: Atiku Ya Nemi a Binciki Tinubu da Ministocinsa kan Takardun Bogi

  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya bukaci gudanar da bincike mai zaman kansa kan Bola Tinubu da ministocinsa
  • Atiku ya fadi haka ne bayan murabus ɗin ministan kimiyya da fasaha, Uche Nnaji, da ake zargin ya gabatar da takardar karatu na bogi
  • Ya ce wannan abin kunya ne kuma ya nuna cewa akwai matsalar gaskiya da amana a cikin gwamnatin Tinubu tun daga sama har ƙasa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, ya yi kira ga gwamnati da ta kafa kwamitin bincike mai zaman kansa.

Ya bukaci haka ne domin tantance takardun karatu na dukkan ministocin da ke cikin majalisar zartarwa ta ƙasa, musamman na Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Atiku Abubakar tare da shugaba Bola Ahmed Tinubu
Atiku Abubakar tare da shugaba Bola Ahmed Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga|Paul Ibe
Source: Getty Images

Atiku ya yi wannan kira ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a safiyar Laraba, 8 ga watan Oktoban 2025.

Kara karanta wannan

Abin da Mahmood Yakubu ya fadawa Tinubu a takardar ajiye shugabancin INEC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa murabus ɗin Uche Nnaji daga mukaminsa na Ministan Kimiyya da Fasaha yunƙurin ɓoye abin kunya da ke cikin gwamnatin Tinubu.

Maganar Atiku kan murabus din Nnaji

Atiku ya bayyana cewa abin takaici ne yadda gwamnatin Tinubu ta ba Uche Nnaji damar yin murabus maimakon a kore shi tare da gurfanar da shi a kotu.

Ya ce hakan ya sake tabbatar da cewa gwamnatin a cike take da masu jabun takardu da rashin gaskiya.

Leadership ta wallafa cewa ya ce:

“Ba Nnaji kaɗai ke da laifi ba, DSS da ta tantance mutane kafin su shiga majalisar zartarwa ita ma ta gaza.
"Ita ce ta ce Nasir El-Rufai bai cancanta ba amma ta amince da wanda ake zargi da takardun bogi. Wannan gazawa ce babba da ta sa duniya ke yi wa Najeriya kallon raini.”

Atiku ya nemi a binciki Tinubu

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa ya ci gaba da cewa matsalar jabun takardu ta fara ne tun daga kan shugaban ƙasa da kansa.

Kara karanta wannan

Ecuador: Matasa kusan 500 sun rufe shugaban kasa da jifa da duwatsu

Ya ce an dade ana muhawara kan shugaba Tinubu game da asalin sa, shekarunsa, da kuma takardun karatunsa.

Atiku ya ambaci batun jami’ar Chicago a matsayin misali, yana mai cewa:

“Idan mutum mai alamar tambaya kan gaskiyarsa ne ke jagorantar ƙasa, to karya da yaudara za su zama al’ada a gwamnati.”

Ya ce irin wannan jagoranci ne ke haifar da rashin gaskiya, bayanan bogi da kuma rashin amana a tsakanin ‘yan gwamnati.

Ministan Tinubu da ya yi murabus kan takardn bogi
Ministan Tinubu da ya yi murabus kan takardn bogi. Hoto: @ChiefUcheNnaji
Source: Twitter

Atiku ya nemi a binciki ministoci

Atiku ya bukaci gudanar da bincike mai zaman kansa kan takardun karatu da na aikin dukkan ministoci da shugabannin gwamnati, daga shugaba Bola Tinubu zuwa ƙananan ma’aikata.

Ya ce:

“’Yan Najeriya suna da haƙƙin sanin gaskiya kan waɗanda ke tafiyar da rayukansu da dukiyarsu.
Sai an tsaftace gwamnati daga irin wannan ƙazanta kafin a dawo da mutuncin ƙasa.”

Takardun bogi: Minista ya yi murabus

A wani rahoton, kun ji cewa ministan kimiyya da fasaha na kasa ya yi murabus kan zargin mallakar takardun bogi.

Uche Nnaji ya ajiye aiki ne bayan wani bincike ya bayyana cewa bai halarci jami'ar UNN ba da ya ce ya yi karatu a can.

Kara karanta wannan

Digirin bogi: An nemi Ministan Tinubu ya yi murabus, ya mika kansa ga hukuma

A bayanin da fadar shugaban kasa ta fitar kan lamarin, ta ce Uche Nnaji ya ce wasu ne suke masa bita da kulli saboda siyasa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng