Muhimman Abubuwa kan Sabuwar Shugabar Rikon INEC da Aka Haifa a Kano

Muhimman Abubuwa kan Sabuwar Shugabar Rikon INEC da Aka Haifa a Kano

  • May Agbamuche-Mbu ta karɓi ragamar shugabancin hukumar INEC bayan tafiyar Farfesa Mahmood Yakubu a makon nan
  • Rahotanni sun bayyana cewa sabuwar shugabar rikon ta fito ne daga jihar Delta amma an haife ta a yankin Arewa, jihar Kano
  • Agbamuche-Mbu lauya ce mai gogewar shekaru fiye da 30 da ke da ƙwarewa a harkokin doka da gudanarwa a Najeriya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta sanar da cewa May Agbamuche-Mbu ta karɓi ragamar aiki a matsayin mukaddashiyar shugabar hukumar.

Hakan na zuwa ne bayan bayan ajiye aikin Farfesa Mahmood Yakubu da ke daf da kammala wa'adin shekara 10 a hukumar.

May Agbamuche-Mbu yayin karbar aiki a hukumar INEC a Abuja
May Agbamuche-Mbu yayin karbar aiki a hukumar INEC a Abuja. Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Daily Trust ta hada wani rahoto game da May Agbamuche-Mbu jim kadan bayan karbar ragamar hukumar INEC.

Kara karanta wannan

INEC: Yakubu ya fadi dalilin ajiye aiki, Tinubu ya shirya nada magajinsa makon nan

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An gudanar da miƙa mata mulki ne a lokacin taron da aka yi da kwamishinonin zaɓe na jihohi (RECs) a hedkwatar hukumar da ke Abuja a ranar Talata.

An haifi May Agbamuche-Mbu a Kano

An haifi Agbamuche-Mbu a Kano amma asalinta 'yar asalin jihar Delta ce, sai dai ta yi wani bangare na rayuwarta a Arewa.

Ta halarci makarantar St. Louis da ke Kano kafin ta tafi jami’ar Ife (wanda yanzu ake kira jami'ar Obafemi Awolowo), a nan ta yi digiri a shekarar 1984.

Ta fara aiki a kotun kolin Najeriya a 1985 sannan daga baya ta zama lauya a Kotun Koli ta Ingila da Wales bayan ta kammala karatu a College of Law, London.

Kwarewa da aikin gwamnati da ta yi

Kafin ta shiga INEC, Agbamuche-Mbu ta kasance babbar lauya kuma abokiyar kafa kamfanin Norfolk, wani sanannen ofishin lauya da ke Legas.

Rahoton TVC ya nuna cewa ta yi aiki a matsayin lauya guda daya tilo a kwamitin tantance ayyukan fadar shugaban ƙasa tsakanin 2010 zuwa 2011.

Kara karanta wannan

Farfesa Mahmood Yakubu ya sauka daga mukamin shugaban INEC

Bayan haka, ta shiga kwamitin ministoci da ya tsara taswirar ci gaban sashen ma’adinai a 2016, kafin daga baya ta zama kwamishiniyar ƙasa a hukumar INEC a shekarar 2016.

Gudunmawa a fannin doka da zaɓe

A matsayin ta na kwamishina, ta taka muhimmiyar rawa wajen sauye-sauyen tsarin doka, haɗin gwiwa da masu ruwa da tsaki, da kuma ƙirƙirar manufofin gudanar da zaɓe a Najeriya.

Ta kuma kasance ƙwararriya a harkar sasanta rikice-rikice, inda ta rike mukamin sakatariya a Cibiyar Lauyoyi Masu Sasanta Rikici ta Najeriya.

Mahmood Yakubu da Tinubu bayan ajiye aiki
Mahmood Yakubu da Tinubu bayan zaben 2023. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

A wajen rubuce-rubuce kuwa, ta wallafa fiye da makaloli 120 a jaridar This Day tsakanin 2014 zuwa 2016, inda ta tattauna batutuwan doka, mulki da tsare-tsaren gwamnati.

Shugaban hukumar INEC ya yi murabus

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya ajiye aiki a ranar Talata, 7 ga Oktoban 2025.

Rahotanni sun bayyana cewa Farfesa Mahmood Yakubu ya ajiye aiki ne kafin wa'adinsa na shekara 5 ya karasa cika.

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya amince da ajiye aikin shugaban hukumar kuma an fara magana kan nada wanda zai gaje shi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng