Gidajen Mutane da Gonaki Sun Nutse cikin Ruwa, Ambaliya Ta Yi Barna a Najeriya

Gidajen Mutane da Gonaki Sun Nutse cikin Ruwa, Ambaliya Ta Yi Barna a Najeriya

  • Ruwan sama mai yawa ya jawo ambaliya ta mamaye gidaje, tituna, gonaki da shaguna a wasu kananan hukumomin jihar Anambra
  • Mazauna yankunan da ambaliyar ta shafa, sun gaggauta tattara ya-nasu ya-nasu sun fice daga gidajensu don tsira da rayukansu
  • Kwamishinan muhalli na jihar, Felix Odimegwu ya bayyana irin matakan da gwamnatin Anambra ta dauka kan ambaliyar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Anambra - An shiga tashin hankali yayin da gidaje suka nutse cikin ruwa a Ogidi, karamar hukumar Idemili ta Arewa ta jihar Anambra.

An rahoto cewa gidajen sun nutse cikin ruwa ne bayan wani mamakon ruwan sama da ya dauki sa’o’i da dama yana sauka a ranar Talata.

Ambaliyar ruwa ta nutsar da gidaje da gonaki a wasu garuruwan jihar Anambra
Hoton yadda ambaliyar ruwa ta nutsar da gidaje da wuraren kasuwanci. Hoto: @AppoSir
Source: Twitter

Ambaliyar ruwa ta cinye gidaje a Anambra

Jaridar Punch ta rahoto cewa mamakon ruwan saman wanda ya fara tun da safe, ya haddasa ambaliya a yankunan da dama sun saba ganin hakan.

Kara karanta wannan

Rashin imani: Yadda harin 'yan bindiga ya maida wani gari zuwa kufai a Kwara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya nuna cewa ambaliyar ta mamaye manyan hanyoyi, gidaje, da shaguna, wanda hakan ya dakatar da harkokin kasuwanci da zirga-zirga a yankin.

Wani mazaunin yankin ya shaida wa manema labarai cewa ruwan kogin Ukwuorji, Ogidi, ya cika ya tumbatsa, inda ya malalo zuwa cikin gidaje da wuraren kasuwanci.

Mutumin ya ce ko da aka ga yadda ruwan ke amai daga kogin, sai mutane suka tattara ya-nasu ya-nasu suka tsere daga gidajensu domin tsira da rayukansu.

Yankin Ogbaru ya fi fuskantar ambaliya

Haka zalika, an ruwaito cewa gidaje da gonaki da dama a karamar hukumar Ogbaru — wadda ke kan bakin kogin Neja — sun nutse a safiyar Talata, sakamakon karuwar ruwa a kogin.

Ogbaru na daya daga cikin yankunan da ambaliya ke yawan faruwa a kowace shekara, kuma wannan musfbar ta sake lalata kasuwanni, makarantu, majami’u, da gidaje na gwamnati da masu zaman kansu.

Wani mazaunin yankin ya ce:

Kara karanta wannan

Tsautsayi: Tankar mai ta yi tsiya a cikin mutane ranar Juma'a, an rasa rayuka da yawa

“Muna cikin hali mai tsanani. Ruwan ya cinye gonaki, ya lalata kayan abinci, kuma mutane da dama sun bar gidajensu suna neman mafaka a yankunan da ke da aminci."

Ambaliyar ta shafi kananan hukumomi 5

Rahotanni sun nuna cewa akalla kananan hukumomi biyar ne aka ruwaito suna fama da wannan ambaliya, ciki har da:

  1. Anambra ya Yamma
  2. Anambra ta Gabas
  3. Ogbaru
  4. Awka ta Arewa
  5. Ayamelum
Mummunar ambaliya ta jawo gidaje, gonaki da wuraren kasuwanci sun nutse a cikin ruwa a Anambra
Taswirar jihar Anambra da ke a Kudancin Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Hotuna da bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta sun nuna yadda ruwa ke kwarara a kan hanyoyi da cikin gidaje, yayin da makarantu da dama suka nutse har gwamnatin jihar ta ayyana Talata a matsayin ranar da babu karatu

Vanguard ta ce kungiyar OADDA ta kawo shawarar yadda za a magance matsalar.

Da yake magana kan lamarin, kwamishinan muhalli na Anambra, Felix Odimegwu, ya ce gwamnati ta riga ta fara daukar matakan gaggawa domin rage illar ambaliyar.

Odimegwu ya ce an fara rarraba tallafin agaji da kayan kariya ga mazauna yankunan da abin ya shafa, yayin da ake jiran rahoton kwararru kan tasirin ambaliyar.

Jihohin Arewa za su fuskanci ambaliya

Kara karanta wannan

Fargabar ambaliya: Kainji da manyan madatsu 3 a Najeriya na shirin kwararo ruwa

Tun da fari, mun ruwaito cewa, gwamnatin tarayya ta yi hasashen ambaliya za ta afku a wasu jihohin Arewa ciki har da Kano, Bauchi da sauransu.

Hukumar NiMet ta ce ambaliyar za ta afku ne yayin da za a samu ruwan sama da iska mai karfi a yawancin sassan Najeriya daga Litinin zuwa Laraba.

An shawarci mazauna jihohin da ambaliyar za ta sha da su dauki matakan gaggawa, sannan an bukaci masu ababen hawa su guji yin tuƙi yayin da ake ruwa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com