Sunayen Sababbin 'Yan Majalisar APC da Aka Rantsar Yau a Majalisar Wakilai

Sunayen Sababbin 'Yan Majalisar APC da Aka Rantsar Yau a Majalisar Wakilai

  • A yau Talata, 7 ga Oktoba, 2025, kakakin majalisar wakilai, Abbas Tajudeen, ya jagoranci rantsar da sababbin mambobi uku
  • Sababbin mambobin sun fito ne daga zaben cike gurbi da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta gudanar ranar 16 ga Agusta, 2025
  • Yayin da aka rantsar da 'yan majalisa uku, dukkansu 'yan APC, an fadi sunayen 'yan majalisa biyu da ba su karbi rantsuwa ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaban majalisar wakilai, Abbas Tajudeen, ya jagoranci bikin rantsar da sababbin mambobin majalisar uku a ranar Talata.

'Yan majalisar da aka rantsar sun samu nasara ne a zaben cike gurbi da hukumar INEC ta gudanar a ranar 16 ga Agusta, 2025.

An rantsar da sababbin 'yan majalisar wakilai 3 da aka zaba a zaben cike gurbi na ranasr 16 ga Agusta, 2025
Abbas Tajudeen yana jagorantar zaman majalisar wakilai a Abuja. Hoto: @HouseNGR
Source: Twitter

An gudanar da rantsuwar ne a zauren majalisar da ke Abuja, inda sakataren majalisa, ya karanta musu rantsuwar kama aiki kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Akpabio ya yi maganar farko bayan bude majalisa da dawowar Sanata Natasha

Zaben cike gurbin kujerun majalisa 5

Sababbin mambobin sun karbi rantsuwa a gaban sauran ‘yan majalisa, yayin da suka dauki alkawarin yin aiki cikin gaskiya da amana domin inganta wakilcin jama’a.

Idan ba a manta ba, Legit Hausa ta rahoto cewa INEC ta gudanar da zaben cike gurbi bayan mutuwar mambobi hudu na majalisar a 2024 da kuma murabus ɗin wani dan majalisa, Dennis Idahosa, wanda aka zabe shi a matsayin mataimakin gwamnan Edo a zaben gwamna na 2024.

Mambobin da suka rasu sun haɗa da:

  1. Ekene Adams (Kaduna)
  2. Isa Dogonyaro (Jigawa)
  3. Olaide Akinremi (Oyo)
  4. Oriyomi Onanuga (Ogun)

Bayan mutuwarsu, hukumar INEC ta gudanar da zaben cike gurbi a jihohin su domin cike kujerun da suka zama babu kowa kansu a majalisar.

Sunayen sababbin 'yan majalisa da aka rantsar

Jaridar Punch ta rahoto cewa, sababbin ‘yan majalisar wakilai da aka rantsar su ne:

  1. Omosede Igbinedion (APC, mazabar Ovia, jihar Edo) – ta maye gurbin Dennis Idahosa
  2. Muktar Rabiu (APC, Garki/Babura, jihar Jigawa) – ya maye gurbin Isa Dogonyaro
  3. Joseph Bagudu (APC, Chikun/Kajuru, jihar Kaduna) – ya maye gurbin Ekene Abubakar Adams

Kara karanta wannan

Sanata Natasha ta koma Majalisar Dattawa, ta zauna a kujerar da ta yi rigima da Akpabio

Sai dai Elegbeji Ayola (Sagamu/Ikenne/Remo ta Arewa, Ogun) da Oyekunle Sunday (Ibadan ta Arewa, Oyo) ba su samu damar halartar bikin rantsuwar ba.

Legit Hausa ta fahimci cewa, Mr. Sunday ne kaɗai ɗan jam’iyyar PDP daga cikin sababbin zababbun wakilai biyar.

Shugaban majalisar wakilai, Abbas Tajudeen ya bukaci sababbin 'yan majalisar su rike gaskiya da wakilci na-gari
Abbas Tajudeen yana jagorantar zaman majalisar wakilai a Abuja. Hoto: @HouseNGR
Source: Twitter

Bikin rantsuwa da martani daga Abbas

Bikin rantsuwar ya samu halartar manyan baki ciki har da tsohon mataimakin gwamnan Edo, Philip Shaibu, wanda ya zo da tawagarsa domin shaida rantsuwar Omosede Igbinedion.

An shigar da su cikin zauren majalisar bayan kudurin da shugaban masu rinjaye, Julius Ihonvbere, ya gabatar domin ba su izinin halartar zaman.

Kakakin majalisar, Abbas Tajudeen, ya taya sababbin mambobin murna, yana mai jaddada cewa majalisar tana buƙatar ƙwararrun wakilai da za su kawo ci gaba da wakilcin gaskiya.

Ya kuma yi kira gare su da su zama masu aiki tukuru wajen wakiltar jama’arsu ba tare da nuna bambancin jam’iyya ba.

APC ta sha kasa a zaben cike gurbi

A wani labarin, mun ruwaito cewa, INEC ta ayyana Folajinmi Oyekunle na PDP a matsayin wanda ya lashe zaben cike gurbi na Ibadan ta Arewa.

Kara karanta wannan

Majalisar wakilai za ta kafa dokoki kan POS da Kirifto a Najeriya

Farfesa Abiodun Oluwadare na jami’ar Ibadan ya tabbatar da sakamakon zaben, inda PDP ta samu kuri’u 18,404, sai APC ta samu kuri’u 8,312.

Wannan nasara ta PDP ta dawo musu da kujerar da suka rasa tun 2011, kuma ta maye gurbin marigayi Musiliu Akinremi (Jagaban) da ya rasu a kan kujerar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com