Fiye da Kwanaki 100 bayan Rasuwarsa, an Fara Shiryen Shiryen Birne Tsohon Gwamna

Fiye da Kwanaki 100 bayan Rasuwarsa, an Fara Shiryen Shiryen Birne Tsohon Gwamna

  • An fara shirye-shiryen jana’izar tsohon gwamnan Kwara wanda ya rasu a birnin Abuja yana da shekara 84 a duniya
  • Hidimomin za su hada da daren tunawa da shi a Abuja da kuma jana’iza a cocin All Saints a Oke Onigbin da ke jihar Kwara
  • Cornelius Olatunji Adebayo.ya taba zama gwamna, sanata, minista, da mamba a NADECO da ta yaki Sani Abacha

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - An fara shire-shiryen birne tsohon gwamnan jihar Kwara kuma tsohon Sanata, Cornelius Olatunji Adebayo.

Rahotanni sun tabbatar da cewa marigayin ya rasu a ranar 25 ga Yuni, 2025, a Abuja yana da shekara 84 a duniya bayan fama da jinya.

An fara shirin birne tsohon gwamnan Kwara
Tsohon gwamnan Kwara, Cornelius Olatunji Adebayo. Hoto: Aproko Kwara.
Source: Facebook

Rahoton TheCable ya tabbatar da cewa an fara shirye-shiryen jana’izar marigayin a yau Talata 7 ga watan Oktoban 2025 daga birnin Abuja.

Kara karanta wannan

Shirin 2027 ya kankama, jagororin jam'iyyar hadaka, ADC sun sa labule a Abuja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Takaitaccen tarihin marigayi tsohon gwamnan

An haifi Adebayo a garin Igbaja na jihar Kwara, kuma ya zama gwamna a shekarar 1983. Kafin nan an zabe shi sanata a 1979 duk karkashin jam’iyyar UPN.

Ya kuma rike mukamin Ministan Sadarwa daga 2003 zuwa 2006, tsohon gwamnan ya kasance mamba a kungiyar NADECO da ke fafutukar dawo da gwamnatin farar hula bayan zaben June 12, 1993, wanda MKO Abiola ya lashe.

Tsohon gwamnan ya ki karbar kujerar minista

A shekarar 1993, gwamnatin mulkin soja ta Sani Abacha ta yi wa Cornelius Adebayo tayin muƙamin minista, amma ya ƙi amincewa da kujerar a cewar rahoton Tribune.

A ranar 31 ga watan Mayu, 1995, wani bam ya fashe a birnin Ilorin, babban birnin jihar Kwara, Hukumar ƴan sanda ta kama Cornelius da wasu ƴan NADECO tare da tsare su kan al’amarin.

Cornelius ya gudu daga Najeriya a shekarar 1996 zuwa ƙasar Canada domin neman mafaka na ɗan wani lokaci, bayan da rahotanni suka ce gwamnatin soja na neman cafke shi.

Kara karanta wannan

Shettima ya ba da mamaki da ya kira Sanusi II da Sarkin Kano a taro a Abuja

Ana yabawa Cornelius Adebayo kan ɗumbin gyare-gyare a fannin ilimi a jihar Kwara lokacin da yake kwamishinan Ilimi daga 1975 zuwa 1978.

Jadawalin yadda za a birne tsohon gwamnan

An fara jana'izar da daren tunawa da hidimarsa cikin waƙoƙin yabo a dakin taro na 'Los Angeles' da ke Abuja da misalin karfe 5:00 na yamma.

A cewar iyalinsa, hidimomin jana’izar za su ci gaba a ranar 10 ga Oktoba 2025 da addu’a aa Ilorin, yayin da hidimar jana’izar tsohon gwamna za ta ci gaba.

An tabbatar da cewa jana'izar za ta gudana a cocin All Saints Anglican, Oke Onigbin da ke Kwara, da misalin karfe 10 na safe ranar 11 ga Oktoba.

Tsohon gwamna ya rasu a Oyo

A wani labarin, mutuwa ta ratsa jihar Oyo inda aka yi rashin ɗaya daga cikin waɗanda suka taɓa riƙe ragamar harkokin mulkin jihar.

Tsohon gwamnan jihar Oyo, Dr. Omololu Olunloyo, ya yi bankwana da duniya da safiyar ranar Lahadi, 6 ga watan Afirilun 2025.

Marigayin wanda ya taɓa zama shugaban farko na kwalejin fasaha ta Ibadan ya rasu ne ƴan kwanaki kaɗan kafin cikarsa shekara 90.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.