Gwamna Mutfwang Ya Mika Bukatarsa ga Remi Tinubu a bainar Jama'a
- Gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang ya yi kalaman yabo ga uwargidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu
- Mutfwang ya yaba mata kan irin kauna, kulawar da goyon bayan da take nunawa mutanen jihar Plateau da yake mulka
- Sannan Gwamnan ya bayyana cewa ziyarar da take kawowa Plateau, ya sanya ta shiga cikin zukatan mutanen jihar
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Plateau - Gwamnan jihar Plateau, Barista Caleb Mutfwang, ya yabawa uwargidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu.
Gwamna Mutfwang ya yabawa Sanata Remi Tinubu ne bisa kauna, kulawa da goyon baya da take ci gaba da nunawa ga mutanen jihar Plateau.

Source: Twitter
Jaridar Leadership ta ce gwamnan ya bayyana haka ne a jawabinsa yayin jana’izar Mama Lydia Yilwatda, mahaifiyar shugaban jam’iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An gudanar da jana'izar Mama Lydia Yilwatda ne a hedikwatar cocin COCIN da ke Jos a karshen mako.

Kara karanta wannan
Sanata Barau ya tabo batun tazarcen Tinubu, ya hango abin da mutanen Kano za su yi a 2027
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na daga cikin mutanen da suka halarci jana'izar.
Gwamna Mutfwang ya yabawa Remi Tinubu
A cewarsa, jihar Plateau ta amfana sosai daga kauna da kulawar da uwargidan shugaban kasan take nunawa.
"Uwar kasarmu, Mai girma Sanata Oluremi Tinubu, sau biyu ta nuna mana kulawa irin ta uwa, ta zo don ta yi mana ta’aziyya da kuma karfafa mu a matsayin shugabanni da ke kokarin dawo da zaman lafiya a Plateau, bisa ga matsayinmu na ‘jihar zaman lafiya da yawon buɗe ido'".
"Kafin kanina, shugaban jam’iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bayyana kansa a fili a matsayin ɗan fari na shugaban kasa Bola Tinubu, tuni na riga na nemi ta zama uwata."
"Saboda haka, bari na maimaita cike da tawali’u da alfahari cewa ita ce uwata, uwarmu. Ziyarce-ziyarcen da take kawowa jihar Plateau sun sa ta kara shiga cikin zukatan mutanenmu."
- Gwamna Caleb Mutfwang
Gwamna Mutfwang: Mutanen Plateau na godewa Remi
Gwamna Mutfwang ya kuma jaddada cewa mutanen jihar za su ci gaba da nuna godiyarsu ta musamman ga uwargidan shugaban kasa.

Kara karanta wannan
An taso gwamna a Arewa a gaba ya koma APC, Tinubu zai iya karasa aikin da Buhari ya watsar

Source: Facebook
“Yayin da muke nuna godiya bisa kasancewarku a wannan wurin jana’iza mai cike da tausayi, ina kuma godiya a madadin mutanen Plateau, bisa ci gaba da goyon bayan da kuke bayarwa wajen ci gaban jihar.”
- Gwamna Caleb Mutfwang
Gwamna Caleb Mutfwang ya kara da cewa jihar za ta nemi shugaban kasa ya sake kai musu ziyara a nan gaba, domin ya ganewa idonsa yadda suke tafiyar da manufar gwamnatinsa ta "Renewed Hope Agenda.”
Remi Tinubu ta magantu kan zaben 2023
A wani labarin kuma, kun ji cewa uwargidan shugaban kasa, Bola Tinubu, Sanata Oluremi Tinubu ta tabo batun kalubalen da ta fuskanta kan zaben shekarar 2023.
Oluremi Tinubu ta bayyana cewa ta rika tambayar kanta cewa shin ko ta shirya zama uwargidan shugaban kasa mafi yawan al'umma a Nahiyar Afrika, saboda tsoro, firgicin da kadaicin da ta rika samun kanta a ciki.
Hakazalika, uwargidan shugaban kasan ta bayyana cewa wasu mutane na kusa da ita, sun ci amanarta tare da yaudararta.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng