Labari Ya Fara Sauyawa: Malami Ya Fadi Shirin Ahlus Sunnah kan Zaben 2027 a Kano
- Maganar zargin da ake yi wa Sheikh Abubakar Lawan Triumph a Kano ta dauki sabon salo, yayin da gwamnatin jihar ta shiga cikin lamarin kai tsaye
- Sheikh Ishaq Adam Ishaq ya bayyana cewa suna da shiri na musamman kan zaben 2027 domin su tabbatar da wanda zai tsaya tsayin daka wajen kare addini
- Ya shawarci Ahlus Sunnah da su yanki katin zabe domin tabbatar da muradinsu, yana mai cewa su ne suka fi yawa a Kano da masallatai
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Maganar zargin Sheikh Abubakar Lawan Triump a Kano ta fara daukar wani sabon salo yayin da gwamnatin jihar ta shiga lamarin.
Wasu na ganin an saka siyasa a cikin lamarin wanda ke neman raba al'ummar Musulmi gida biyu game da zaben da ke tafe.

Source: Facebook
Shirin Ahlus Sunnah a Kano kan zaben 2027
Sheikh Ishaq Adam Ishaq ya yi magana a faifan bidiyo kan lamarin wanda shafin Abdullahin Gwandu TV ya wallafa a manhajar Facebook.
A cikin bidiyon, Malamin ya ce akwai shirin da suke yi game da zaben 2027 a Kano domin tabbatar da wanda zai kare addini.
Shehin malamin ya kuma shawarci dukan Ahlus Sunnah da su je su yanki katin zabe da kuma gyara ga wadanda na su ya samu matsala.
"Sakonmu na karshe, ba wasa muke ba, duk wanda ya san bai da kuri'a ya je ya samu ana bayarwa da sauran wadanda ta su ke da matsala.
"Ba wai za mu yi zabe ba ne kan APC ko PDP ko NNPP ko wani abu, ko a ina kake ka zauna a jam'iyyarka, romon dimukradiyya idan ya zo ka karbi kayanka.
"Amma dai akwai ajanda ta Sunnah cewa za mu nuna mutum daya, wanda shi za a zaba wanda za mu yi hakan ne domin ya kiyaye addini.

Kara karanta wannan
'Za a maimata June 12': Malami a Kaduna ya yi hasashe mai ban tsoro kan zaben 2027
- Sheikh Ishaq Adam Ishaq

Source: Facebook
Malamin ya bayyana yawan mabiyansu a Kano
Har ila yau, malamin ya ce ko tambaya aka yi an san su waye suka fi yawa a Kano inda ya ce ko masallatan Juma'arsu ma sun fi yawa.
Sheikh ya kuma bambance mambobinsu da sauran mabiya wasu akidu inda ya ce da ka ga mabiyansu za ka suna da hankali da ilimi.
Ya kara da cewa:
"Wannan shi ne abin da za mu yi, saboda wallahi idan da za a tambaya a Kano su waye suka fi yawa, waye za ka ce, mu Ahlus Sunnah mun fi yawa.
"Mafi yawan Ahlus Sunnah za ka gansu masu hankali ne, ba za ka ga mutum yana ihu a titi kamar mahaukaci ba."
Sheikh Ishaq ya fadi hukuncin da ya kamaci Turji
A baya, mun ba ku labarin cewa Sheikh Ishaq Adam Ishaq ya yi watsi da ra'ayin tattaunawar sulhu da ‘yan bindiga, yana mai cewa Musulunci ya umurci a yake su.

Kara karanta wannan
Triumph: An shawarci Abba game da kalaman mataimakinsa, Sagagi kan zargin taba annabi
Malamin ya bayyana cewa addini da dokar kasa duk sun amince a kashe su ko a hukunta su matukar suna ci gaba da barna.
Ya kalubalanci masu cewa ‘yan bindiga sun fi karfin jami’an tsaro, yana mai jaddada cewa gwamnati na da ikon kawo karshen su.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
