Mutane Za Su Amfana da Najeriya Ta Fara Shirin Karbo Bashin Tiriliyoyin Naira daga China
- Ministan Makamashi, Adebayo Adelabu ya ce Gwamnatin Tarayya na kokarin gina sabuwar tashar samar da wutar lantarki
- Adelabu ya bayyana cewa domin yin wannan aiki, Najeriya ta fara tattaunawa da bankin China domin karbo aron Dala biliyan 2
- Ya ce wannan aiki zai dawo da masu amfani da wutar lantarki, wadanda suka fita daga tsarin saboda rashin tabbas a Najeriya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Najeriya ta fara tattaunawa da bankin safarar kayayyaki na kasar China watau China Exim Bank domin karbo rancen Dala biliyan biyu.
Gwamnatin Najeriya na kokarin karbo wannan bashi ne domin gina tashar wuta ta musamman da nufin share hawayen 'yan Najeriya game da karancin hasken lantarki.

Source: Twitter
Ministan Harkokin Makamashi, Adebayo Adelebu ne ya bayyana haka a wurin taron tattalin arziki da aka gudanar a Abuja ranar Litinin, in ji Channels tv.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abin da Najeriya za ta yi da bashin $2bn
Adebayo Adelabu ya bayyana cewa aikin na daga cikin yunkurin da gwamnati ke yi na sauya tsarin samar da wutar lantarki ta yadda za a raba nauyin zuwa fannoni daban-daban.
A cewar Ministan, hakan zai jawo jawo manyan masana’antu da suka fice daga tsarin wutar lantarki na kasa saboda rashin tabbas, su dawo cikin tsarin.
Ya ce sabuwar tashar wutar za ta warware matsalar karancin wuta a yankin Gabas da Yammacin Najeriya, inda yawancin manyan masu amfani da wuta ke gudanar da harkokinsu.
“Wannan wani bangare ne na kokarin da gwamnati ke yi wajen sauya tsarin samar da wuta a Najeriya da kuma dawo da manyan masu amfani da wuta da suka gudu saboda rashin tabbas,” in ji shi.
Babban turken wutar lantarkin Najeriya ya sha faduwa sau da dama a cikin shekaru, abin da ake dangantawa da karancin karfin samarwa, matsalolin isar da wuta, da kuma kurakuran fasaha.
Shirin da ake yi na share hawayen 'yan Najeriya
Adelabu ya ce sabuwar tashar wutar da ake shirin ginawa za ta inganta isar da wuta da kuma tabbatar da cewa an samu isasshiyar wutar lantarki a yankunan masana’antu.
Ya kara da cewa, Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta riga ta amince da kudin aikin, rahoton Bussiness Day

Source: Facebook
Haka kuma, Ministan ya bayyana cewa karin kudin wuta da aka yi kwanakin baya a birane ya karawa masana’antu kudin shiga da 70% a shekarar 2024.
Mista Adelebu ya kuma bayyana cewa ana sa ran masana'antu za su samu karin kudin shiga da 41% a bana, zuwa Naira tiriliyan 2.4 ($1.6 biliyan).
TCN ya tabbatar da lalacewar layin lantarki
A wani labarin, kun ji cewa turken wutar lantarki da ke raba wuta zuwa jihohin Ribas, Kuros Riba, Bayelsa da Akwa Ibom ya samu matsala a daren Asabar.
Kamfanin TCN ya ce wutar da ake rabawa ta kan turken mai karfin 132KV ta katse, lamarin da zai jefa wasu yankuna cikin duhu kafin kammala gyara.
TCN ya bai wa jama’a hakuri bisa dauke wutar da aka yi sakamakon wannan matsala da ta faru tare da tabbatar da cewa za a dawo da wuta nan ba da jimawa ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


