Majalisar Wakilai Za Ta Kafa Dokoki kan POS da Kirifto a Najeriya

Majalisar Wakilai Za Ta Kafa Dokoki kan POS da Kirifto a Najeriya

  • Majalisar wakilai ta kafa kwamiti na wucin gadi domin nazarin yadda ake amfani da kudin Kirifto da POS a Najeriya
  • Shugaban majalisar, Abbas Tajudeen, ya ce matakin na da muhimmanci wajen hana zamba, safarar kudin haram
  • Kwamiti zai yi zama da hukumomi da masana kudi domin tsara doka da za ta kare ’yan kasa da inganta tsaron tattali

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Majalisar wakilan ta fara matakan tsara dokar da za ta kula da harkokin kuɗi ta intanet, musamman Kirifto da na’urorin POS a fadin Najeriya.

Wannan na zuwa ne bayan kaddamar da kwamiti na wucin gadi da Shugaban Majalisar, Abbas Tajudeen, ya yi a ranar Litinin.

Yadda ake hada hada a wajen wani mai POS
Yadda ake hada hada a wajen wani mai POS. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Daily Trust ta wallafa cewa Abbas ya bayyana cewa wannan mataki ya zama wajibi ne saboda yadda aka yawaita zamba, sata ta yanar gizo, da kuma safarar haramtattun kudi.

Kara karanta wannan

Kano: 'Dan jarida ya debo ruwan dafa kansa, ICPC ta kama shi kan zambar N14m

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce, duk da cewa tattalin arzikin Najeriya ya nuna yana kara bunkasa, akwai barazanar tsaro da ake bukatar magancewa cikin gaggawa.

Majalisa za ta sa dokar POS da Kirifto

Abbas Tajudeen ya ce babu dokoki masu fayyace yadda ake gudanar da harkar Kirifto a Najeriya, lamarin da ke iya ba da damar amfani da ita wajen safarar kudi da taimakon ta’addanci.

The Cable ta rahoto ya ce:

“Wannan fasaha tana da sarkakiya da rashin daidaituwa, saboda haka wajibi ne majalisa ta tsara dokar da za ta ba da kariya ga masu amfani da ita da kuma tabbatar da gaskiya a kasuwa.”

Ya kuma bayyana cewa kwamitin zai gudanar da zaman sauraron jama’a don tattara ra’ayoyi daga hukumomi da masana domin samar da cikakkiyar doka da za ta tsara harkar kuɗi.

Shugaban majalisar wakilai yana wani jawabi
Shugaban majalisar wakilai yana wani jawabi. Hoto: Abba Tajudeen
Source: Facebook

Goyon bayan tsarin tattalin Tinubu

Abbas ya ce shirin yana cikin kokarin tsarin gyaran tattalin arziki na Bola Ahmed Tinubu, ta hanyar kare kasa daga abubuwan da za su iya durkusar da tsarin kuɗi ko kawo cikas.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Za a rika biya wa talabijin da radiyo haraji, jama'a sun fara korafi

Ya kara da cewa majalisar ba za ta tsaya kallon yadda mutane ke amfani da fasahar zamani wajen cutar da jama’a ba.

Kwamitin majalisa ya fadi manufarsa

Shugaban kwamitin, Hon. Olufemi Bamisile ya ce duk da cewa Kirifto da POS sun kawo sauki da bunkasa kasuwanci, suna kuma haifar da barazana ga tsaro da amincin tsarin kuɗi.

Ya ce kwamitin zai mayar da hankali wajen tsara doka da za ta karfafa musayar kudi kuma a lokaci guda ta kare al’umma daga zamba da safarar kudi.

Bamisile ya ce za su yi aiki tare da hukumomi irin su Babban Bankin Najeriya (CBN), Hukumar Tsaro ta SEC, EFCC, ICPC, da kuma rundunar ’yan sanda domin samun bayanai masu inganci.

Legit ta tattauna da dan Kirifto

Wani dan Kirifto, Aminu Muhammad Baba ya bayyanawa Legit Hausa cewa bai kamata majalisar ta sanya dokokin da za su iya shafar harkar ba.

Aminu ya ce:

"Mutane da dama sun samu sana'a ta hanyar POS da Kirifto, saboda haka bai kamata a yi abin da zai kawo matsala a harkokin ba."

Kara karanta wannan

Ana batun kisan kiyashin Kiristoci, CAN ta aika sako ga gwamnatin tarayya

"Ya kamata 'yan majalisar su yi wasu abubuwan da za su amfani kasa."

Majalisa ta fadi shirin Tinubu kan zabe

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban majalisar wakilai, Abbas Tajudeen ya yi magana kan zaben da za a yi a 2027.

Ya bayyana cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya shirya gudanar da zabe mai inganci a fadin Najeriya.

Shugaban majalisar ya bayyana haka ne yayin ganawa da tawagar tarayyar Turai da ta zo Najeriya kan zaben kasar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng