Tsaro: Tinubu Ya Gayyato Jonathan, IBB, Obasanjo Gwamnoni 36 da Manyan Kasa
- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tsara ganawa da majalisar kolin kasa da ta ‘yan sanda domin tattaunawa kan matsalar tsaro
- An shirya zaman ne a fadar shugaban kasa da ke Abuja domin samar da sababbin matakai da za su karfafa tsarin tsaro a fadin kasar
- Majalisar za ta tattauna kan rikice-rikicen da ke addabar Arewa da yankunan Najeriya tare da nazarin yadda sojoji ke aiki a Najeriya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Shugaba Bola Tinubu ya kira taron majalisar kolin kasa da kuma majalisar ‘yan sanda domin tattaunawa kan karuwar matsalar tsaro da ke addabar wasu sassan Najeriya.
An shirya taron ne a ranar Alhamis, 9, Oktoba, 2025 a zauren majalisar da ke fadar shugaban kasa, Abuja, inda manyan jiga-jigan kasar za su halarta kai tsaye ko ta yanar gizo.

Source: Facebook
Punch ta wallafa cewa fadar shugaban kasa ta ce matakin na daga cikin kokarin gwamnati wajen karfafa tsarin tsaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shirin taron majalisar koli da bayanin gwamnati
A wata sanarwa daga ofishin sakataren gwamnatin tarayya, mai dauke da sa hannun Dr. Emanso Umobong, an tabbatar da cewa an riga an aike da gayyata ga mambobin majalisar kolin kasa.
Sanarwar ta bayyana cewa taron majalisar kasa zai gudana da karfe 1:00 na rana, yayin da na majalisar ‘yan sanda zai fara da karfe 2:00 na rana.
Rahoton Business Day ya nuna cewa an ce tarurrukan za su mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi tsaro da harkokin ‘yan sanda a kasar baki daya.
Tasirin majalisar kolin kasa a Najeriya
Majalisar kolin kasa tana karkashin jagorancin shugaban kasa, wacce ke tattare da tsofaffin shugabannin kasa, tsofaffin alkalin alkalai, gwamnoni, da babban lauyan gwamnatin tarayya.
A cewar sanarwar, majalisa tana da rawar da take takawa wajen bayar da shawara kan manyan al’amuran kasa, ciki har da tsaro da nade-nade.

Source: Facebook
A kan haka ake sa ran tsofaffin shugabannni kamar Goodluck Jonathan, Janar Ibrahim Babangida, IOlusegun Obasanjo, gwamnoni 36 da sauransu za su halarci zaman.
Majalisar ‘yan sanda kuma tana da alhakin kula da tsarin gudanarwa da ayyukan rundunar ‘yan sanda, har da nada jami'ai da ladabtar da manyansu idan suka yi laifi.
Batutuwan da za a tattauna a taron
Majalisar za ta nazarci halin da ake ciki na tsaro, ta kuma tantance yadda ake gudanar da ayyukan soji a yankuna masu fama da hare-haren ‘yan bindiga, garkuwa da rikicin kabilanci.
Haka kuma, akwai tsammanin za a tattauna batutuwan siyasa da na gudanarwa, ciki har da zaben wanda zai gaji shugaban hukumar zabe mai barin gado.
Wata majiyar fadar shugaban kasa ta bayyana cewa taron zai zama muhimmin mataki wajen samar da sababbin hanyoyin magance rashin tsaro da bunkasa tsare-tsaren gwamnati.
Tinubu ya ba malamin musulunci mota
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ba babban limamin Oyo da ke Ibadan kyautar mota.

Kara karanta wannan
An kwayewa minista zani a kasuwa kan gabatar da digirin bogi ga shugaba Tinubu da majalisa
Rahotanni sun bayyana cewa an ba malamin motar ne domin samun damar cigaba da gudanar da harkokin addini.
Yayin da wasu jama'a suka yaba da kyautar motar, wasu na ganin hakan tamkar mika wuya ne ga 'yan siyasar Najeriya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

