Kallo Ya Koma Majalisa yayin da Sanata Natasha Ta Shirya Komawa bayan Dakatarwa

Kallo Ya Koma Majalisa yayin da Sanata Natasha Ta Shirya Komawa bayan Dakatarwa

  • Ga dukkan alamu sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Sanata Akpoti-Uduaghan ta shirya komawa bakin aikinta a majalisar dattawa
  • Lauyoyin sanatan sun ja kunnen majalisar dattawa kan yin yunkurin hana ta halartar zaman majalisa tare da sauran sanatoci
  • Sun bayyana cewa tuni ta kammala wa'adin watanni shida na dakatarwar da aka yi mata daga majalisar dattawan ta Najeriya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta shirya komawa halartar zaman majalisa.

Sanata Natasha za ta koma majalisa ne a yau (Talata), tare da sauran 'yan majalisar dattawa, bayan kammala wa'adin watanni shida na dakatarwar da aka yi mata.

Sanata Natasha za ta koma majalisa
Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan na jawabi. Hoto: Natasha H. Akpoti
Source: Facebook

Daya daga cikin lauyoyinta, Victor Giwa, ya bada wannan tabbacin yayin wata hira da jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun da farko, Majalisar Dattawa ta jinkirta dawowarta daga hutu daga 23 ga Satumba zuwa 7 ga Oktoba, 2025.

Kara karanta wannan

Tsaro: Tinubu ya gayyato Jonathan, IBB, Obasanjo gwamnoni 36 da manyan kasa

Lauyoyin Sanata Natasha sun gargadi majalisa

Tawagar lauyoyin Sanata Natasha ta gargaɗi Majalisar Dattawa da ta guji wani yunkuri na hana ta shiga zauren majalisa, tana mai cewa ta riga ta cika hukuncin dakatarwa kuma doka ta ba ta damar komawa bakin aiki.

Victor Giwa ya bayyana kwarin gwiwa cewa komawarta majalisa ba za ta haifar da wata matsala ba.

"A gani na, wadda muke karewa kawai ta tafi ta fara aiki a ranar Talata. Duk wani abu da wasu za su ce ra’ayinsu ne kawai. Kamar yadda Femi Falana ya faɗa, Majalisar Dattawa ba za ta zama cibiyar da ke halatta abin da bai dace ba.”
"Ba za a bar wasu ‘yan tsiraru su rinjayi Majalisar Dokoki ba. Wannan majalisa dokar kasa ce ta samar da ita, don haka dole ne ayyukanta su kasance bisa doka, ba bisa son zuciyar shugabanni ba.”

- Victor Giwa

An bukaci a bar Natasha ta koma majalisa

A cewarsa, hana ta komawa zai zama kamar karyata hukuncin majalisar da kanta, kuma hakan zai jefa majalisar cikin rudani.

Kara karanta wannan

Rikici ya ɓarke a Majalisar Wakilai a yunƙurin tsige shugaban marasa rinjaye

Sanata Natasha Akpoti ta shirya komawa majalisa
Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan. Hoto: Natasha H. Akpoti
Source: Twitter
"Ta riga ta cika watanni shida na dakatarwa, don haka abin da kotu ke dubawa yanzu shi ne ko hukuncin da aka yanke a watan Maris ya yi daidai da doka. Ba shi da alaƙa da komawarta majalisa."
“Idan aka hana ta komawa, hakan na nufin kun karya dokar da kuka kafa da kanku, wadda ta ce za a dakatar da ita na watanni shida kacal.”

- Victor Giwa

Majalisa ta hana Natasha komawa bakin aiki

A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar dattawan Najeriya ta bayyana cewa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, ba ta da hurumin komawa kan kujerarta a majalisa.

Mukaddashin sakataren majalisar, Dr. Yahaya Danzaria, ya aika wata wasika zuwa ga sanatar, inda ya sanar da ita cewa wa'adin dakatarwar da aka yi mata bai kare ba, saboda haka ba za a bari ta koma bakin aiki ba.

Majalisar ta kuma tabbatar mata cewa za a sanar da ita matakin karshe bayan kotun daukaka kara ta yanke hukunci.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng