Dangote: PENGASSAN Ta Yi Martani ga Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima

Dangote: PENGASSAN Ta Yi Martani ga Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima

  • Kalaman Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima sun sosa wa kungiyar manyan ma'aikatan man fetur, PENGASSAN rai
  • A ranar Litinin ne Kashim Shettima ya zargi PENGASSAN da kawo tarnaki a kan ayyukan matatar Dangote da ke kawo sauyi a Najeriya
  • Mataimakin Shugaban Kasan ya kara da cewa Najeriya ta fi karfin wata kungiyar kwadago da ke shirin kawo nakasu ga cigaban tattalin arziki

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja – Kungiyar nan ta manyan ma'aikatan man fetur da iskar gas ta Najeriya (PENGASSAN) ta caccaki fadar shugaban kasa.

Kungiyar ta bayyana rashin jin dadinta bisa kalaman Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, wanda ya soki yajin aikin da kungiyar ta yi a kan matatar Dangote.

Mataimakin Shugaban Kasa ya kare Dangote
Hoton Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima Hoto: Kashim Shettima
Source: Facebook

The Cable ta wallafa cewa a yayin bude taron tattalin arzikin Najeriya na 2025 a Abuja, Shettima ya bayyana Dangote a matsayin ginshikin tattalin arzikin Najeriya.

Kara karanta wannan

PENGASSAN ta hukunta rassanta 2 kan rashin hana Dangote gas a yajin aiki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya yi gargadin cewa Najeriya tafi karfin PENGASSAN, kuma babu wanda ya kamata ya hana ruwa gudu a kasar nan saboda sabani da mutum guda.

PENGASSAN ta yi martani ga Kashim Shettima

Jaridar Punch ta wallafa cewa shugaban PENGASSAN na kasa, Kwamred Festus Osifo, ya maida martani ga kalaman Mataimakin Shugaban Kasa.

A kalamansa:

"Najeriya ta fi karfin Dangote da fadar shugaban kasa."

Ya ce manufar kungiyar ita ce kare ma’aikatan da aka sallama saboda shiga ƙungiyar, kuma za su ci gaba da daukar irin wannan mataki duk lokacin da irin wannan abu ya faru.

Haka kuma kungiyar ta yi martani ga mutanen da su ka fito zanga-zangar nuna goyon baya ga matatar Dangote a ranar Litinin.

Daruruwan masu zanga-zanga sun mamaye titunan Kaduna suna zargin PENGASSAN da hadin baki da masu shigo da man fetur domin hana ci gaban tace man cikin gida.

An yi zanga-zangar adawa da PENGASSAN

Kara karanta wannan

Labari mai dadi: Shugaba Tinubu ya umarci a rage kudin kujerar Hajjin 2026 a Najeriya

Jagoran zanga-zangar, Igwe Ude-Umanta, ya ce wannan yunkuri ne na ‘yantar da tattalin arzikin Najeriya daga mutanen da ke hana tace mai cikin gida.

Ya yi zargin cewa akwai wasu mutane da ke lalata masana'antar yadi a Kaduna, kuma yanzu suna son su hana matatar Dangote tsaya wa da kafafunta.

Wadanda su ka gudanar da zanga-zangar sun bukaci gwamnatin tarayya da ta hukunta shugabannin kungiyar don hana maimaituwar hakan.

PENGASSAN ta soki kalaman Kashim na kare Dangote
Hoton Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote Hoto: Getty
Source: Getty Images

Amma a martaninsa, Osifo ya ce:

"Wadanda suka fito zanga-zangar ba su san komai a kan batun ba."

PENGASSAN ta hukunta 'ya'yanta saboda Dangote

A wani labarin, mun wallafa cewa kungiyar manyan ma’aikatan man fetur da iskar gas ta Najeriya (PENGASSAN) ta dauki matakin rusa shugabannin wasu rassa.

Ta zargi shugabannin rassan Nigeria Gas Infrastructure Company Ltd (NGIC) da NNPC Gas Marketing Limited (NGML), da kin bayar da hadin kai a yayin yajin aikin da aka yi.

PENGASSAN ta zartar da wannan hukunci ne bayan ta gano cewa shugabannin biyu sun kasa rufe iskar gas gaba daya da ke zuwa matatar man Dangote kamar yadda aka bukata.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng