Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Magana kan Zargin Minista Na Amfani da Takardun Bogi

Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Magana kan Zargin Minista Na Amfani da Takardun Bogi

  • Ana ci gaba da matsa lamba ga Ministan kimiyya da fasaha ya yi murabus bisa zargin yin amfani da takardun bogi
  • Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa za ta jira ta ga yadda abubuwa za su kaya a gaban kotu kan lamarin
  • Ministan dai ya dage cewa ya kammala karatunsa a shekarar 1985, amma jami'ar UNN ta musanta hakan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Fadar shugaban kasa ta yi magana kan zargin yin amfani da takardun bogi da ake yi wa Ministan kimiyya da fasaha, Uche Nnaji.

Fadar shugaban kasan ta bayyana cewa za ta ɗauki mataki ne bayan hukuncin kotu kan zargin da ake yi wa ministan.

Fadar shugaban kasa ta fadi matsayarta kan zargin da ake yi wa minista
Shugaba Bola Tinubu da Ministan kimiyya da fasaha, Uche Nnaji. Hoto: @aonanuga1956, @ChiefUcheNnaji
Source: Twitter

Jaridar Leadership ta ce mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan lokacin da ta tuntube shi kan lamarin.

Kara karanta wannan

Uche Nnaji: Ministan Tinubu da ake zargi da amfani da takardun bogi, ya fito ya yi bayani

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me fadar shugaban kasa ta ce kan lamarin?

A cewar fadar shugaban basa, babu bukatar yin wata magana kan batun saboda yana gaban kotu a halin yanzu.

Bayo Onanuga ya ce gwamnatin tarayya za ta girmama tsarin shari’a kuma za ta jira hukuncin kotu kafin ta ɗauki matsaya kan lamarin.

"Wannan lamari yana gaban kotu. Mu jira hukuncin kotu tukunna."

- Bayo Onanuga

Jami'a ta karyata Ministan Tinubu

Wannan bayanin ya zo ne bayan bayanan da ke nuna cewa Jami’ar Najeriya, Nsukka (UNN) ta karyata takardar shaidar karatun digiri da Nnaji ya gabatar.

Jaridar Premium Times ta ce a wata wasika mai dauke da kwanan watan 2 ga Oktoba, 2025, wadda shugaban jami’ar, Farfesa Simon Ortuanya ya sanyawa hannu, jami’ar ta bayyana cewa bisa ga bayanan da ke hannunta, ministan bai kammala karatunsa ba.

"Daga dukkan bayanan da ke hannun Jami’ar Najeriya, Nsukka, ba mu samu wata shaida da ke nuna cewa ministan kimiyya da fasaha, Mista Geoffrey Uchechukwu Nnaji, ya kammala karatu a watan Yuli 1985 ba."

Kara karanta wannan

ADC ta tanka zargin da ake yi wa ministan Tinubu na yin amfani da takardun bogi

"Saboda haka, jami’ar ba ta bayar da takardar shaidar kammala karatu gare shi ba.”

- Farfesa Simon Ortuanya

Jami’ar ta kara da cewa wannan matsayar ta yi daidai da wata wasika da ta aika zuwa hukumar karɓar korafe-korafen jama’a a ranar 13 ga Mayu, 2025, wadda ta kunshi irin wannan bayani.

Uche Nnaji na fuskantar zargin yin amfani da takardun bogi
Ministan kimiyya da fasaha, Uche Nnaji. Hoto: @ChiefUcheNnaji
Source: Twitter

Sai dai a cikin takardun da Nnaji ya gabatar a kotu, ya amince cewa bai karɓi takardar shaidar kammala karatu daga jami’ar ba, yana mai zargin cewa rashin haɗin kai daga jami’ar ne ya haifar da jinkirin.

Duk da wannan, kiraye-kiraye daga kungiyoyin fararen hula da ‘yan adawa na karuwa, inda suke neman Uche Nnaji ya sauka daga mukaminsa har sai an kammala shari’ar.

Sai dai fadar shugaban kasa ta nace cewa ba za ta shiga cikin cece-kucen ba, tana mai jaddada cewa a bar tsarin shari’a ya yi aikinsa yadda ya kamata.

Uche Nnaji ya kare kansa

A wani labarin kuma, kun ji cewa Ministan kimiyya da fasaha, Uche Nnaji, ya yi bayani kan zargin da ake yi masa na yin amfani da takardun bogi.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar ADC ta sake taso Shugaba Tinubu a gaba kan rashin tsaro

Uche Nnaji ya karyata zargin da ake yi masa inda ya hakikance cewa ya kammala karatunsa a jami'ar UNN.

Ministan ya bayyana cewa ana jifansa da zargin yin amfani da takardun bogin ne kawai don a bata masa suna.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng