Shettima Ya ba da Mamaki da Ya Kira Sanusi II da Sarkin Kano a Taro a Abuja

Shettima Ya ba da Mamaki da Ya Kira Sanusi II da Sarkin Kano a Taro a Abuja

  • Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana cewa gwamnati ta kafa shirin tallafawa ‘yan kasuwa
  • Ya ce manufofin tattalin arzikin gwamnati sun fara haifar da sakamako mai kyau fiye da yadda ƙwararru suka hango
  • Shettima ya ambaci Sarki, Khalifa Muhammadu Sanusi II, a matsayin aboki yayin da ya ke gabatar da jawabi a taron

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Kashim Shettima, ya bayyana cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta kafa asusun tallafi ₦200bn domin taimaka wa ƙananan ‘yan kasuwa da masana’antu.

Sanata Shettima ya bayyana haka ne a ranar Litinin, 6 ga Oktoba, 2025, yayin bude taron tattalin arzikin Najeriya karo na 31 da aka gudanar a Abuja.

Shettima da Sanusi II
Kashim Shettima da Dr. Muhammadu Sanusi II a wajen taron da aka yi a Abuja. Hoto: Masarautar Kano
Source: Facebook

Mataimakin shugaban kasar ya wallafa a X cewa za a ba su tallafin ne domin su samu damar faɗaɗa ayyukansu.

Kara karanta wannan

Bayan rage kudin Hajji, Tinubu ya ba malamin Musulunci kyautar babbar mota

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce wannan mataki na cikin tsarin sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnati ta fara aiwatarwa domin farfaɗo da masana’antu, ƙara samar da ayyukan yi, da rage talauci a tsakanin al’umma.

Tallafin N200bn da za a bayar

Shettima, wanda ya wakilci Bola Tinubu a taron, ya bayyana cewa duk wani matakin da gwamnati ke ɗauka yana bin ka’idar daidaita tsakanin tunanin tattalin arziki da bukatar jama’a.

Ya ce gwamnati ta lura da ƙalubale da dama da ƙananan masana’antu da ‘yan kasuwa ke fuskanta.

Mataimakin shugaban kasar ya ce shi ya sa aka samar da tallafin domin taimaka musu wajen samun rance, gudummawa da sauransu.

Ya ƙara da cewa:

“Mun ɗauki matakan da suka dace domin ƙarfafa masana’antu, samar da aikin yi, da kuma farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa.
"Wannan asusun tallafi zai buɗe ƙofofi ga matasa da marasa galihu domin su samu damar shiga harkokin kasuwanci.”
Shettima da wasu manyan baki a taron tattali a Abuja
Shettima da wasu manyan baki a taron tattali a Abuja. Hoto: Kashim Shettima
Source: Facebook

Kashim Shettima ya ce an fara samun sauki

Kara karanta wannan

'Domin samun sauki,' Ana neman Tinubu ya saka wa talaka tallafi a abubuwa 3

Shettima ya jaddada cewa sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa sun fara tasiri a fannonin daban-daban na tattalin arziki.

A cewarsa, ƙimar bunƙasar tattalin arzikin ƙasa ya kai kashi 4.23 cikin 100 a watan Satumban 2025, abin da ya zarce hasashen ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da na cikin gida.

Yadda Shettima ya kira Sanusi II da Sarki

Sarki Sanusi II, wanda ya kasance tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), ya halarci taron tare da fitattun shugabanni da masana daga sassa daban-daban na ƙasar.

A yayin jawabin nasa, Mataimakin Shugaban Ƙasa ya ambaci Sanusi II da Sarkin Kano duk da rikicin sarauta da ake da bangaren mai martaba Aminu Ado Bayero a kotu.

Masarautar Kano ta wallafa a X cewa Shettima ya ce:

“Aboki na kuma ɗan’uwana, Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II,"

Gwamnati Tinubu ta ce a rage kudin Hajji

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Najeriya ta yi magana kan rage kudin aikin Hajjin shekarar 2026.

Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ne ya bayyana haka bayan ganawa da shugabannin hukumar NAHCON.

Kara karanta wannan

'Rashin tsaro ba zai kare yanzu ba,' Gwamna ya fadawa 'yan Najeriya gaskiya

Shettima ya ce shugaban kasa ya ba hukumar NAHCON umarni ta mika sabon daftarin kudin aikin Hajji cikin kwana biyu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng