Bayan Rage Kudin Hajji, Tinubu Ya ba Malamin Musulunci Kyautar Babbar Mota

Bayan Rage Kudin Hajji, Tinubu Ya ba Malamin Musulunci Kyautar Babbar Mota

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bai wa Babban Limamin Ibadan, Sheikh Abdul-Ganiyy Agbotomokekere, sabuwar mota
  • An isar da motar ne a ranar Lahadi, 5, Oktoba, 2025 ta hannun Sanata Yunus Akintunde, wanda ke wakiltar Oyo ta Tsakiya
  • Hakan ya jawo martani daban-daban daga jama’a, wasu na taya murna, wasu kuma na ganin bai dace da irin wannan kyauta ba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Oyo – Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya karrama Babban Limamin Ibadanland, Sheikh Abdul-Ganiyy Agbotomokekere, da sabuwar mota kirar Toyota Land Cruiser Prado.

An ba da kyautar ne a matsayin yabo ga rawar da yake takawa wajen samar da zaman lafiya da haɗin kan addini a jihar Oyo.

Limamin Oyo da shugaba Bola Tinubu ya ba mota
Limamin Oyo da Shugaba Bola Tinubu ya ba mota. Hoto:The Grand Imam of Oyo State Agbotomokekere|Bayo Onanuga
Source: Facebook

Legit Hausa ta tabbatar da yadda aka mika kyautar motar ne a wani sako da malamin ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Tinubu ya koma ofis, ya dawo birnin Abuja bayan kwashe kwanaki a Legas

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu daga cikin mabiya sun bayyana jin daɗinsu da wannan kyauta, yayin da wasu kuma suka ce irin wannan bai dace da matsayin limami ba a lokacin da jama’a ke fama da tsadar rayuwa.

Bola Tinubu ya ba malami kyautar mota

Sheikh Agbotomokekere ya karɓi motar tare da manyan malaman addini da mabiya a Ibadan, inda aka bayyana cewa kyautar ta fito kai tsaye daga shugaban ƙasa Tinubu.

Tribune ta wallafa cewa wani hoton da aka wallafa ya nuna rubutu da ke cewa:

“Sabuwar Toyota Land Cruiser Jeep 2025 kyauta daga Shugaba Bola Ahmed Tinubu ga Babban Limamin Ibadan.”

Wasu mutane kamar Gbola Halid Adesina da Daaru Thaqofa sun yi addu’a ga shugaban ƙasa, suna bayyana godiya da fatan alheri ga limamin da gwamnatin Tarayya.

Masu suka sun ce an yi kuskure

Sai dai wasu mutane sun yi suka mai tsanani, inda suka ce bai dace gwamnati ta rika bai wa manyan malamai kyaututtukan alfarma ba a lokacin da talakawa ke cikin ƙunci.

Kara karanta wannan

Bayan yi wa matar Sarki tsirara, an kama mutum 10 da zargin yunƙurin hallaka basarake

Wani mai suna Adam Tahir ya ce:

“Lokacin da masu mulki suka fara bai wa malamai kyauta maimakon su kula da talakawa, to al’amura sun baci.”

Ya ƙara da cewa irin wannan kyauta ba alama ce ta girmamawa ba, illa nuna yadda addini ke zama kayan siyasa.

A cewarsa:

“Mota kirar Land Cruiser ba ta magance yunwa; tana ƙara nauyi ne ga wanda ya karɓa.”
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Darasi daga rayuwar wasu malamai

Adam Tahir ya tuno yadda marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gummi ke ƙin karɓar irin waɗannan kyaututtuka daga gwamnoni, yana mika su ga matalauta da ɗalibai.

Ya ce hakan ne asalin abin da ke nuna mutunci na malamai wajen kaucewa abin da zai iya lalata niyyar su.

Gwamnatin Kano ta gargadi malamai

A wani rahoton, kun ji cewa majalisar shura da gwamnatin Kano ta yi karin haske kan korafin da aka shigar game da Sheikh Lawan Triumph.

Kwamitin ya bayyana cewa yana cigaba da nazari kan maganganun da malamin ya yi aka shigar da korafi a kansu.

Kara karanta wannan

Tsautsayi: Tankar mai ta yi tsiya a cikin mutane ranar Juma'a, an rasa rayuka da yawa

Baya ga haka, kwamitin ya gargadi sauran malamai a wasu jihohi da su daina tsoma baki wajen tattauna mas'alar yayin da ake bincike.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng