'Yan Bindiga Sun Sake Ta'addanci a Kwara, an Sace Basarake da Kashe Mutane

'Yan Bindiga Sun Sake Ta'addanci a Kwara, an Sace Basarake da Kashe Mutane

  • 'Yan bindiga dauke da makamai sun yi aika-aika mai yawa a wasu hare-hare da suka kai a jihar Kwara
  • Miyagun 'yan bindigan sun hallaka wani malamin addinin Kirista bayan sun yi garkuwa da shi
  • Hakazalika sun kuma yi awon gaba da wani Hakimi bayan sun farmaki jama'a lokacin da suke shirin sallar Magriba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kwara - ‘Yan bindiga dauke da makamai sun sake kai mummunan hari a jihar Kwara.

'Yan bindgan sun kashe mutum ɗaya tare da sace wasu mutane biyu, ciki har da Hakimin kauyen Rani da ke karamar hukumar Patigi, jihar Kwara.

'Yan bindiga sun kai hari a jihar Kwara
Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq. Hoto: Abdulrahman Abdulrazaq
Source: Twitter

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa 'yan bindigan sun kuma kashe wani Fasto na cocin ECWA, Rabaran James Audu Issa, da ke kauyen Ekati na karamar hukumar Patigi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan bindiga sun kashe Fasto

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe shugaban jami'an tsaro da sace mutane a Neja

'Yan bindigan sun kashe shi ne bayan iyalansa sun biya kuɗin fansan da suka nema.

Shaidu sun bayyana cewa ‘yan bindigan sun kashe limamin cocin ne bayan sun karɓi kuɗin fansa daga danginsa.

Rahotanni sun nuna cewa an yi garkuwa da Fasto Issa ne tun ranar, 28 ga watan Agusta, inda masu garkuwar suka fara neman Naira miliyan 100 a matsayin kudin fansa.

Sai dai, iyalansa sun tattauna da su har suka amince su biya N5m, wanda aka bada domin a sake shi.

Bayan ‘yan bindigan sun karɓi N5m, sai suka sake neman karin N45m, amma kafin a ci gaba da tattaunawa sai suka kashe shi a karshen mako.

Wani shugaban al’umma da ya nemi a ɓoye sunansa ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici wanda ke nuna yadda ‘yan ta’adda ke kara samun karfi da rashin tsoro a yankin Kwara ta Arewa.

“Kisan gilla da aka yi wa Fasto ya nuna yadda ‘yan bindiga ke cigaba da aikata ta’asa cikin kasar nan, suna garkuwa da mutane, karɓar kudin fansa da kashe rayuka."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari a Abuja, an kashe babban likita tare da sace 'ya'yansa

- Wani shugaban al'umma

Miyagun 'yan bindiga sun sace Hakimi

Hakazalika, a ranar Lahadi ‘yan bindiga sun kutsa kauyen Rani da yamma yayin da mutane ke shirin sallar Magariba, inda suka sace mutum biyu, ciki har da Hakimin kauyen, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar da labarin.

Majiyoyi daga yankin sun ce ‘yan bindigan sun kashe mutum biyu kafin su tafi da Hakimin tare da wani mutum, lamarin da ya haifar da tsananin tsoro da firgici a cikin mazauna yankin.

"Rashin tsaro a Rani ya tabarbare sosai. Ba mu da damar fita ko zuwa gona saboda tsoron kada a sace mu. Rayuwa ta tsaya cak."
“Muna roƙon gwamnatin jiha da ta tarayya su kawo mana dauki, su turo jami’an tsaro da za su dawo da zaman lafiya a yankin Patigi.”

- Wani mazaunin yankin

'Yan bindiga sun yi ta'asa a Kwara
Taswirar jihar Kwara, tarayyar Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Me 'yan sanda suka ce kan lamarin?

Wani babban jami’in ‘yan sanda daga Patigi ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa:

Kara karanta wannan

Bayan yi wa matar Sarki tsirara, an kama mutum 10 da zargin yunƙurin hallaka basarake

"Mun sanar da hedkwatar rundunar ‘yan sanda ta jihar Kwara domin ɗaukar matakin gaggawa da kuma ceto waɗanda aka sace."

'Yan bindiga sun kashe shugaban 'yan sa-kai

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga sun hallaka shugaban 'yan sa-kai a jihar Neja.

'Yan bindigan sun hallaka shugaban 'yan sa-kan ne yayin da yake jagorantar wata tawaga zuwa aikin sinitiri .

Tantiran 'yan bindigan sun kuma yi awon gaba da mutane bakwai a hare-haren da suka kai a kauyukan Rijau da Magama.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng