Sanata Barau Zai Raba Tallafin N20,000 ga Talakawa a Kano, an Ji Adadin da Za Su Samu

Sanata Barau Zai Raba Tallafin N20,000 ga Talakawa a Kano, an Ji Adadin da Za Su Samu

  • Talakawa da marasa galihu a jihar Kano za su samu tallafi daga wajen mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Barau Jibrin
  • Sanata Barau Jibrin zai bada tallafin na kudi a dukkanin kananan hukumomi 44 da ake da su a jihar Kano, ba iyaka yankin da yake wakilta ba
  • 'Dan majalisar tarayyar zai bada tallafin ne bayan an kammala zakulo mutanen da za su amfani da shi ta hanyar rarraba fom domin cikewa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Barau I. Jibrin, zai raba tallafin N20,000 ga marasa galihu a Kano.

Sanata Barau zai bada tallafin ga mutum 10,000 daga cikin talakawa da marasa galihu a kananan hukumomi 44 na jihar Kano.

Sanata Barau zai raba tallafi a Kano
Sanata Barau Jibrin a zauren majalisar dattawa. Hoto: @barauijibrin
Source: Facebook

Jaridar Leadership ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Ismail Mudashir, ya fitar ranar Lahadi, 5 ga watan Oktoban 2025 a Abuja.

Kara karanta wannan

Rashin imani: Yadda harin 'yan bindiga ya maida wani gari zuwa kufai a Kwara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Barau Jibril zai raba tallafi a Kano

Ya bayyana cewa za a zabi masu cin gajiyar tallafin a ranar Alhamis, 9 ga watan Oktoba, 2025, ta hanyar rarraba fom ɗin neman shiga shirin.

An bayyana cewa wannan shiri yana gudana ne ta hannun gidauniyar Barau I. Jibrin Foundation (BIJF), wadda Sanata Barau ya kafa domin tallafawa al’umma.

Gidauniyar ta gudanar da shirye-shirye da dama masu tasiri, ciki har da shirin bada tallafin karatun digiri na biyu a kasashen waje domin ɗalibai marasa galihu daga jihar Kano.

Sanarwar ta kara da cewa rarraba kuɗin wani ɓangare ne na kokarin Sanata Barau na inganta rayuwar talakawa da karfafa tattalin arziki a fadin jihar.

“Jimillar mutane 6,500 za a zaɓa daga yankin Kano ta Arewa, inda kowace daga cikin kananan hukumomi 13 za ta samar da masu cin gajiya mutum 500."
“Haka kuma, mutane 112 za a zaɓa daga kowace karamar hukuma ta Kano ta Tsakiya da Kano ta Kudu."

Kara karanta wannan

Tinubu zai je COCIN tattaunawa da shugabannin Kiristocin Arewa a Filato

Ismail Mudashir

Sanata Barau zai ba marasa galihu tallafi a Kano
Sanata Barau Jibrin a wajen wani taro. Hoto: @barauijibrin
Source: Twitter

Barau ya saba raba tallafi a Kano

Haka kuma, sanarwar ta jero tallafin da Sanata Barau ya bayar a fannoni kamar ilimi, lafiya, noma, tsaro da sufuri, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar da labarin.

"Karfafa mata da matasa ya kasance ginshikin manufar Sanata Barau, domin yana ci gaba da ƙarfafa ci gaban tattalin arziki da haɗin kan al’umma a Arewacin Najeriya da kasa baki ɗaya."

- Ismail Mudashir

Karanta wasu labaran kan jihar Kano

Barau ya gana da tsofaffin Kansiloli

A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya gana da wasu tsofaffin Kansiloli daga karamar hukumar Rimin Gado ta jihar Kano.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi magana kan sahihancin zaben 2027 da tawagar tarayyar Turai

Tawagar tsofaffin kansilolin wadda take a karkashin jagorancin sakatarensu, Hon. Ibrahim Jemomi, ta ziyarci Sanata Barau da wasu ’yan majalisar dattawa biyu, Muntari Dandutse da Babangida Hussaini.

Mataimakin shugaban majalisar dattawan ya bayyana cewa sun tattauna da tsofaffin Kansilolin kan muhimmin abubuwa da suka shafi ci gaban jihar Kano da kasa baki daya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng