Ministan Tinubu Ya Kama Kansa a kan Zarginsa da Takardun Karatun Bogi

Ministan Tinubu Ya Kama Kansa a kan Zarginsa da Takardun Karatun Bogi

  • Ministan Kimiyya da Fasaha, Uche Nnaji, ya amince cewa Jami’ar Najeriya Nsukka (UNN) ba ta taɓa ba shi takardar shaidar kammala karatu ba
  • Ya bayyana haka ne bayan wani bincike da aka shafe tsawon shekaru biyu ana yi, kuma an gano cewa takardun karatun Nnaji na bogi ne
  • Jami’ar UNN ta tabbatar da cewa Nnaji bai kammala karatu ba, kuma babu sunansa a cikin jerin waɗanda suka kammala a shekarar 1985

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, AbujaMinistan Kimiyya da Fasaha na Tarayya, CIf Uche Nnaji, ya amince a gaban kotu cewa Jami’ar Najeriya Nsukka (UNN) ba ta taɓa ba shi takardar shaidar digiri ba.

Ministan ya tabbatar da wannan bayani ne a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja yayin da ake takaddama a kan sahihancin takardun karatunsa.

Kara karanta wannan

An kwayewa minista zani a kasuwa kan gabatar da digirin bogi ga shugaba Tinubu da majalisa

Uche Nnaji ya shiga matsala kan takardar karatu
Hoton Ministan Kimiyya da Fasaha,Uche Nnaji Hoto: Hon Uche Nnaji
Source: UGC

An gano Ministan Tinubu da takardun bogi

Tun a watan Yuli 2023 ake zargin Nnaji da ƙirƙirar takardar digiri da takardar NYSC da ya gabatar a ofisoshin gwamnatin tarayya, da su ka hada da ofishin SGF da SSS.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lamarin ya sa Ministan ya garzaya kotu, inda ya nemi umarnin kotu da zai hana jami’ar da jami’anta tsoma baki a cikin bayanan karatunsa kuma a tilasta ba shi bayanan karatunsa.

Sai dai Alƙaliya Hauwa Yilwa ta ki bayar da umarnin da Uche Nnaji ya nema, sannan ta dage zaman zuwa ranar 6 ga Oktoba 2025.

Uche Nnaji ya tabbatar UNN ba ta bashi kwalin kammala digiti ba
Minista a gwamnatin Tinubu, Uche Nnaji Hoto: Hon. Uche Nnaji
Source: UGC

Sai dai abin mamaki, a cikin rantsuwar da Nnaji ya gabatar, ya bayyana cewa duk da cewa ya kammala karatu a 1985, har yanzu bai karɓi takardar shaidar digirinsa daga jami’ar ba.

Jami'ar UNN ta karyata Ministan kimiyya

Amma jami’ar UNN ta musanta wannan, inda ta bayyana cewa Nnaji bai taɓa kammala karatunsa ba, kuma babu sunansa cikin wadanda su ka kammala karatu na shekarar 1985.

Kara karanta wannan

Gwamna ya lallaba ya gana da Tinubu, za a saki jagoran 'yan ta'adda da Buhari ya kama a 2021

Wani jami’in jami’ar ya ce bincike ya tabbatar da cewa:

“Nnaji bai kammala ba, kuma duk bayanan da ke cikin fayil ɗinsa sun tsaya ne tun lokacin da ya daina zuwa karatu.”

Da ya amince cewa UNN ba ta taɓa ba shi takardar digiri ba, ana ganin hakan na nufin Nnaji ya yarda cewa takardun da ya gabatar – ciki har da na NYSC – na ƙarya ne.

Wannan ya haifar da tambayoyi masu nauyi game da wurin da ya samo takardun da ya gabatar ga gwamnati har aka nada shi a matsayin Minista.

An taso mukarraban Tinubu a gaba

A baya, mun kawo labarin cewa masanin tsaro kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, Opialu Fabian, ya yaba da kokarin Shugaba Bola Ahmed Tinubu wajen yakar matsalar tsaro.

A cewarsa, gwamnatin Tinubu ta ware mafi girman kasafin kudi a tarihi ga bangaren tsaro, wanda ke nuna niyyar gaske na magance barazanar tsaro a sassa daban-daban na kasar.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi magana kan sahihancin zaben 2027 da tawagar tarayyar Turai

Sai dai Fabian ya caccaki wasu daga cikin mukarraban shugaban kasa, yana cewa duk da irin kuɗin da aka ware, da dama cikinsu ba su tabuka abin kirki ba wajen shawo kan matsalolin.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng