Dattawan Arewa Sun Fadi Mutanen da ke Son Durkusar da Matatar Dangote

Dattawan Arewa Sun Fadi Mutanen da ke Son Durkusar da Matatar Dangote

  • Kungiyar ACF ta bayyana damuwa kan wani yunkuri da ake zargi na hana matatar Dangote aiki yadda ya kamata
  • ACF ta ce wannan dambarwar na iya lalata tattalin arzikin Najeriya da kuma hana masu zuba jari shigowa ƙasar
  • Kungiyar ta bukaci gwamnatin tarayya ta kare matatar man daga munanan makirce-makirce na cikin gida da na waje

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano – Kungiyar dattawan Arewa ta ACF ta nuna damuwa kan abin da ta kira shirin da wasu ƙungiyoyi ke yi na durkusar da matatar Dangote.

Kungiyar ta ce ana yi wa matatar barazana ta hanyoyi daban-daban ciki har da tsoma bakin hukumomin gwamnati, matsalolin mai da rikice-rikicen ƙungiyoyin ma’aikata.

Dangote da wani bangare na matatar shi
Dangote da wani bangare na matatar shi. Hoto: Dangote Industries
Source: Getty Images

A cikin sanarwar da kakakin ACF, Farfesa T.A. Muhammad-Baba ya fitar, Daily Trust ta wallafa cewa kungiyar ta ce wannan lamari na iya zama barazana ga ci gaban tattalin ƙasar.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Jigon APC ya bukaci Dangote ya buga takara da Tinubu a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

AFC: Masu son durkusar da Dangote

Kungiyar ta bayyana cewa tun kafa matatar Dangote ake ƙoƙarin kawo mata cikas daga wasu da suka saba cin gajiyar tsohuwar hanyar shigo da mai daga waje.

Ta ce masu ruwa da tsaki a harkar mai ba su son ganin matatar ta yi nasara saboda hakan zai kawo ƙarshen rashawa da cin hanci da ya dade yana addabar fannin.

ACF ta bayyana cewa matatar Dangote na ɗaya daga cikin manyan kadarorin ƙasa da suka cancanci kariya ta musamman saboda tasirinta wajen inganta tattalin arziki.

Karin korafin ACF kan matatar Dangote

Kungiyar ta yi Allah wadai da matsin lamba da ake yi wa ma’aikatan matatar Dangote da su shiga ƙungiyar PENGASSAN da ta kira sabawa kundin tsarin mulki.

Ta bayyana rashin jin daɗinta kan yadda ƙungiyar ma’aikata ta ƙi bin umarnin kotu da ta hana ta tsoma baki cikin harkokin masana’antar.

The Nation ta rahoto cewa ACF ta ce wannan mataki yana iya kawo cikas ga cigaban matatar da kuma ma’aikatanta.

Kara karanta wannan

An taso gwamna a Arewa a gaba ya koma APC, Tinubu zai iya karasa aikin da Buhari ya watsar

Wani sashe na matatar Dangote da ke Legas
Wani sashe na matatar Dangote da ke Legas. Hoto: Dangote Industries
Source: UGC

Kira ga gwamnati da majalisar dokoki

Kungiyar ta bukaci gwamnati ta kare matatar daga duk wani shiri na lalata ta, tana mai cewa durkusar Dangote na iya kore masu zuba jari daga cikin gida da waje.

Ta nemi gwamnati ta sanya masana’antar cikin jerin kadarorin ƙasa masu mahimmanci domin ta samu kariya ta musamman da tsaro.

ACF ta kuma bukaci kafa kwamitin bincike na shari’a domin gano wadanda ke haddasa yawan yajin aiki da ke lalata muhimman masana’antu a ƙasar.

Kungiyar ta jaddada cewa ƙungiyoyin ma’aikata su guji zama 'yan amshin shata ga masu son kawo cikas ga cigaban masana’antu a Nahiyar Afirka.

An nemi Dangote ya shiga siyasa

A wani rahoton, kun ji cewa wani jigo a APC, Salihu Nataro ya bukaci Alhaji Aliko Dangote ya shiga siyasa.

Nataro ya ce akwai bukatar Aliko Dangote da gwamnan jihar Abia, Alex Otti su yi takara tare a zaben 2027.

Kara karanta wannan

'Ka ba mu dama': Mutanen Sokoto sun tura sako ga Tinubu kan harin ƴan bindiga

'Dan siyasar ya bayyana cewa Dangote da gwamna Otti suna da cikakkiyar kwarewar da za su kawo sauyi a Najeriya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng