Kano: Abba Ya Biya Iyalin Ɗan Kwangilan da Ya Rasu N184m da Gwamnatin Ganduje Ta Hana

Kano: Abba Ya Biya Iyalin Ɗan Kwangilan da Ya Rasu N184m da Gwamnatin Ganduje Ta Hana

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da biyan Naira miliyan 184 ga iyalan marigayi Alhaji Sulaiman Abubakar na Dutsen-Ma Trading Company
  • Marigayin na bin gwamnatin wannan kuɗi tun shekara ta 2018 a zamanin tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje da ya yi wani aiki
  • Shugaban ƙaramar hukumar Dawakin Tofa, Anas Ɗan Maliki, ne ya taimaka wajen kai buƙatar iyalan zuwa ga Gwamna Abba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya amince da biyan kuɗin kwangila da ya kai Naira miliyan 184.5 ga iyalan marigayi Alhaji Sulaiman Abubakar.

Marigayi Sulaiman shi ne mai kamfanin Dutsen-Ma Trading Company, wanda ya kammala aiki a zamanin tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a shekarar 2018.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Jigon APC ya bukaci Dangote ya buga takara da Tinubu a 2027

Gwamnan Kano ya biya bashin 'dan kwangila
Hoton Gwamna Abba Kabir Yusuf Hoto: Sanusi Bature D/Tofa
Source: Facebook

A wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Shugaban Karamar Hukumar Dwakin Tofa, Anas Danmaliki ya nuna cewa thar ya rasu, gwamnati ba ta biya shi hakkinsa ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Dan kwangila na bin gwamnatin Kano bashi

Rahotanni sun bayyana cewa an ba marigayin wannan kwangila ne a zamanin tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta Ma’aikatar Lafiya.

Alhaji Sulaiman Abubakar ya yi aikin sabunta cibiyar lafiya ta Garo da ke ƙaramar hukumar Kabo, kuma ya kammala dukkanin abin da ya kamata a 2018.

An gano cewa Kamfanin marigayin ya kammala aikin tare da miƙa dukkannin takardun da suka dace, amma bai karɓi kuɗinsa ba kafin rasuwarsa.

Iyalan marigayin sun rubuta wa Gwamna Abba wasiƙar roƙon taimako a ranar 6 ga watan Mayu, 2025, suna neman a biya su kuɗin da mahaifinsu ke bin gwamnati.

Daga cikin abubuwan da su ka aika ga gwamnati akwai takardun kwangila, takardun biyan kuɗi da shaidar kammala aiki domin tabbatar da hujja.

Kara karanta wannan

Mai Mala Buni ya gwangwaje dan tsohon gwamna da mukami a gwamnatinsa

Kano: Yadda Abba ya sallami iyalan 'dan kwangilar

Shugaban ƙaramar hukumar Dawakin Tofa, Anas Ɗan Maliki, ya bayyana cewa iyalan marigayin sun zo gare shi domin neman taimakon karbo hakkinsu a hannun gwamnati.

Ya bayyana cewa ya shawarce su a kan su ajiye bukatar neman ganawa kai tsaye da gwamna, sai dai su rubuta buƙata a hukumance tare da haɗa takardunsu.

Anas Dan Maliki ya ce:

“Ina mai tabbatar musu cewa in dai Mai Girma Gwamna Abba ya ga takardarsu, zai ba da umarnin biyan su. Na ba su tabbaci kuma Alhamdulillah, Allah ya sa hakan ta tabbata."

Gwamnatin Kano ta fara binciken Ganduje

A baya, kun samu labarin cewa hukumar karɓar korafe-korafe da Yaki da cin hanci ta Jihar Kano ta tabbatar da fara bincike kan tsohon gwamnan jihar, Dr. Abdullahi Umar Ganduje.

A wannan karon, hukumar PCACC ta fara binciken ne dangane da zargin karkatar da makudan kuɗi a aikin tashar tsandauri da ke unguwar Dala da mallaka wa iyalansa kwangiloli.

Kara karanta wannan

Triumph: An shawarci Abba game da kalaman mataimakinsa, Sagagi kan zargin taba annabi

Shugaban PCACC, Saidu Yahya, ya ce binciken ya samo asali ne daga koke-koken jama’a, inda aka gano wasu manyan bayanai da ke nuna cewa an mallaka wa iyalan Ganduje kadarorin gwamnati.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng