Jam'iyyar ADC Ta Sake Taso Shugaba Tinubu a Gaba kan Rashin Tsaro
- Jam'iyyar ADC ta nuna rashin gamsuwarta kan yadda Shugaba Bola Tinubu yake daukar matsalar rashin tsaro
- ADC ta zargi shugaban kasan da yi wa lamarin rikon sakainar kashi ta hanyar nuna masa halin ko in kula
- Hakazalika, jam'iyyar ta nuna cewa shugaban kaaan ya fi damuwa da tarurrukan siyasa, maimakon kare rayukan 'yan Najeriya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Jam’iyyar ADC ta soki shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, kan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita.
ADC ta zargi Shugaba Tinubu da rashin nuna damuwa da halin matsanancin tsaro da kasar nan ke ciki, tana mai cewa ya fi maida hankali kan tarurrukan siyasa maimakon kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya.

Source: Facebook
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar na kasa, Malam Bolaji Abdullahi, ya sanyawa hannu kuma ya fitar a shafinsa na X.

Kara karanta wannan
Gwamna ya lallaba ya gana da Tinubu, za a saki jagoran 'yan ta'adda da Buhari ya kama a 2021
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me ADC ta ce kan Shugaba Tinubu
ADC ta ce maganganun da Shugaba Tinubu ya yi a Cocin Church of Christ in Nations (COCIN) da ke Jos, cewa manufarsa ita ce ya haɗa kan ‘yan Najeriya, ba komai ba ne face jawabin siyasa marar tushe.
Ta bayyana cewa abubuwan da shugaban kasan ya yi tun bayan hawansa mulki, sun nuna cewa bai san yadda zai hada kan 'yan Najeriya ba.
ADC ta bayyana cewa Najeriya na fuskantar hare-hare, inda ta kuma bude kofar bayar da shawarwari kan yadda gwamnati za ta magance matsalar tsaro.
"Jam’iyyar ADC ta damu matuka kan yadda shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ke nuna rashin tausayawa da rashin kulawa kan yadda matsalar tsaro ke kara ta’azzara a kasar nan."
"A matsayinsa na kwamandan rundunar sojojin Najeriya, wanda kundin tsarin mulki ya ba alhakin kare rayukan jama’a da dukiyoyinsu, zabin shugaban kasa na ci gaba da halartar tarurrukan siyasa da na bukukuwa a lokacin da ake fuskantar mummunan halin rashin tsaro, abin takaici ne kuma rashin sanin ya kamata ne.”
- Bolaji Abdullahi
ADC ta 'karyata' gwamnatin tarayya
ADC ta ce duk da cewa gwamnatin tarayya na ci gaba da faɗin cewa “ana samun ci gaba” a fannin tsaro, wannan magana ba gaskiya ba ce, domin jinin talakawan da ake zubarwa kullum shi ke tabbatar da akasin hakan.

Source: Facebook
"Yayin da ake tarwatsa kauyuka da rufe makarantu, jama’a na gudu daga gidajensu, shugaban kasa yana ci gaba da halartar jana’iza da bukukuwan abokan siyasarsa."
"Wannan na nuna cewa shugaban kasa ya fi damuwa da siyasa fiye da rayuwar ‘yan Najeriya.”
- Bolaji Abdullahi
Jam’iyyar ta kuma tuna cewa lokacin da daruruwan rayuka suka salwanta a jihar Plateau, shugaban kasan ya zauna a fadar Villa, yana mai yin tir da abin da ya kamata ya hana faruwa tun farko.
Atiku ya soki Tinubu
A wani labarin kum, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya caccaki Shugaba Bola Tinubu.
Atiku ya soki shugaban kasan ne kan ziyarar da ya kai zuwa jihar Plateau, don halartar jana'izar mahaifiyar shugaban APC na kasa.
Tsohon mataimakin shugaban kasan ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya yi basaja ne kawai da jana'izar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

