Gwamna Zulum Ya Aika da Muhimmin Sako ga Mutanen Borno kan Boko Haram
- Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya kai wata ziyarar jaje kan harin da 'yan ta'addan Boko Haram suka kai
- Farfesa Zulum ya yabawa jarumtar mutanen yankin kan yadda suka ki barin gidajensu duk da barazanar 'yan ta'addan Boko Haram
- Gwamnan ya ba su tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da daukar matakai domin tabbatar da tsaro a yankin
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Borno - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya mayar mutanen kauyuka uku zuwa matsugunansu.
Gwamna Zulum ya mayar da mutanen ne bayan da mazauna yankin Banki a karamar hukumar Bama suka nuna jarumta wajen kin barin gidajensu duk da barazanar Boko Haram.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cwwa gwamnan ya kai ziyara zuwa Banki a ranar Lahadi, inda ‘yan ta’adda suka kai hari a sansanin sojoji da kuma wasu wuraren fararen hula.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Zulum ya kai ziyarar ne domin jaje da yaba wa jama’a bisa karfin gwiwar da suka nuna.
Me Zulum ya ce kan Boko Haram?
"Na zo Banki ne domin na yaba muku bisa jarumtar da kuka nuna. Gaskiya abin alfahari ne sosai."
“Ba za mu bar wasu tsirarun ‘yan 'ta'adda su rusa wannan gari da ke samun ci gaba a kasuwanci da tattalin arziki ba.”
"Ina tabbatar muku cewa ‘yan ta’adda ba za su yi nasara ba, Insha Allah. Za mu karfafa tsaron wannan garin da ke kan iyaka, kuma za mu tallafawa matasanmu masu aikin sa-kai, maharba, da ‘yan sa-kai domin kara kare yankin.”
- Farfesa Babagana Umara Zulum
Gwamnan ya tabbatar da cewa an tanadi matakan tsaro masu karfi don hana sababbin hare-haren Boko Haram a garin.
Zulum zai mayar da mutane matsugunansu
A wani ɓangare na shirin farfaɗo da yankunan da rikici ya shafa, Zulum ya sanar da shirin mayar da mazauna kauyuka uku, Kumshe, Tarmu’a da Bula Yobe, duk a cikin ƙaramar hukumar Bama zuwa gidajensu.
"Za mu mayar da mutanen Kumshe, Tarmu’a da Bula Yobe. Mutanen nan sun cancanci rayuwa mai mutunci, kuma mun kuduri aniyar ganin hakan ya tabbata."
- Farfesa Babagana Umara Zulum
Haka kuma, Gwamna Zulum ya bayyana cewa ana gyaran hanyar Banki, inda aka tura manyan motoci 30 domin gyara hanyar wadda ta lalace sosai.

Source: Twitter
Zulum ya yi kira ga jama’a, musamman matasa, da su halarci aikin rajistar masu kaɗa kuri’a da ke gudana domin kyautata makomar al’umma.
Haka zalika, Gwamnan ya ziyarci ’yan kasuwa a kasuwar Banki, inda ya ja hankalinsu su kasance masu lura da kuma haɗin kai da jami’an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a yankin.
Gwamna Zulum na kokari
Wani mazaunin Borno mai suna Aliyu Biu ya shaidawa Legit Hausa cewa Gwamna Babagana Umara Zulum, yana kokari kan rashin tsaron da ya addabi jihar.
"Muna yabawa Gwamna Zulum kan irin namijin kokarin da yake yi dangane da matsalar rikicin Boko Haram."
"Yana zuwa gani da idonsa tare da bada tallafi ga jama'a da kuma samar da kayan aiki ga jami'an tsaro."

Kara karanta wannan
Hare hare da kona fadarsa ya tilastawa Sarki tserewa Kamaru, mutanensa sun bi shi
- Aliyu Biu
'Yan Boko Haram sun kona fadar basarake
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan ta'addan Boko Haram sun kai wani harin ta'addanci a garin Kirawa da ke jihar Borno.
'Yan ta'addan sun yi kisa tare da yin garkuwa da mutane a harin da suka kai a garin wanda yake iyaka da Kamaru.
Miyagun sun kuma kona fadar Hakimin garin, Alhaji Abdulrahman Abubakar, tare da wasu shaguna da gine-gine.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

