Lambar Abba Kabir Ta Fito, Malamin Addini Ya Jero Gwamnoni 4 da Ka Iya Komawa APC

Lambar Abba Kabir Ta Fito, Malamin Addini Ya Jero Gwamnoni 4 da Ka Iya Komawa APC

  • Babban malamin addinin Kirista, Elijah Ayodele ya yi hasashe mai ban mamaki game da wasu gwamnonin adawa da za su iya komawa APC
  • Malamin ya gargadi ga Bola Tinubu cewa wasu gwamnonin adawa za su koma APC amma ba duka ne ke son taimaka masa
  • Limamin ya ce wasu daga cikinsu za su shiga jam’iyyar ne kawai don su sami albarkar shugaban ƙasa da kuma neman mukamai

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Fasto Elijah Ayodele, ya yi hasashen wasu gwamnoni da ka iya komawa APC.

Faston ya yi gargadi ga Shugaba Bola Tinubu cewa wasu daga cikin gwamnonin ba don Allah za su shiga APC ba sai don cimma burinsu.

Fasto ya gargadi Tinubu game da gwamnoni da ake zargin komawa APC
Fasto Elijah Ayodele da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: Primate Elijah Ayodele, Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Fasto ya yi hasashen gwamnoni da za su shiga APC

Kara karanta wannan

'Ka ba mu dama': Mutanen Sokoto sun tura sako ga Tinubu kan harin ƴan bindiga

Hakan na cikin wata sanarwa da Tribune ta samu wanda mai taimaka masa, Osho Oluwatosin, ya fitar a yau Lahadi 5 ga watan Octoban 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ayodele ya ce gwamnonin jam’iyyun adawa za su koma APC nan ba da jimawa ba, amma ba duka za su goyi bayan sa ba.

Ya ce Tinubu ya zama mai taka-tsantsan saboda wasu daga cikin waɗanda za su koma jam’iyyar ba su da niyyar taimaka masa, maimakon haka, za su zama abokan gaba a cikin jam’iyyar.

Ya bayyana cewa gwamnonin Taraba, Zamfara, Enugu da Kano ne daga cikin waɗanda ke shirye-shiryen komawa APC.

Gwamnonin da ake zargin za su koma APC
Gwamna Abba Kabir, Elijah Ayodele da Gwamna Dauda Lawal. Hoto: Abba Kabir Yusuf, Primate Elijah Ayodele da Gwamna Dauda Lawal.
Source: Facebook

Gargadin Fasto ga Tinubu kan gwamnonin

Sai dai, kamar yadda ya ce, wasu daga cikinsu na da niyyar taimaka wa shugaban ƙasa, amma wasu kuma za su shiga ne domin cimma muradunsu na siyasa.

“Kimanin gwamnonin adawa hudu za su koma APC — Taraba, Kano, Zamfara da Enugu. Amma ba duka za su tsaya kan yarjejeniyar tallafa wa shugaban ƙasa ba."

- Primate Ayodele.

Limamin ya kara da cewa wasu daga cikinsu za su koma jam’iyyar ne kawai don su sami albarkar Shugaban Ƙasa ko kuma su tabbatar da matsayinsu a siyasar jihohinsu.

Kara karanta wannan

Triumph: An shawarci Abba game da kalaman mataimakinsa, Sagagi kan zargin taba annabi

Ya kara da cewa:

“Wasu za su shiga ne kawai don su samu goyon bayan shugaban ƙasa — don haka batun wanda zai zama wane a 2027 zai zama mai zafi sosai."

Ayodele ya kuma shawarci Tinubu da ya binciki waɗannan sababbin mambobin jam’iyya da kansa domin gano waɗanda ke da muguwar niyya a ciki, ya ce akwai ‘yan APC da ma ba su ke fatan shugaban ƙasa ya yi nasara ba.

“Ba kowa cikin jam’iyyar zai taimaka wa shugaban ƙasa ba. Wasu makiya ne a cikin gida. Ya kamata ya gane su da wuri."

- Elijah Ayodele.

An roki gwamnan Taraba ya koma APC

Kun ji cewa wata ƙungiyar matasa ta shawarci Gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba ya koma jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.

Kungiyar mai suna 'Concerned Taraba Youth Group' ta bukaci Gwamna Kefas ya haɗa kai da Bola Tinubu domin samun ayyukan more rayuwa.

Ta ce hakan zai taimaka wajen farfado da manyan ayyukan gwamnati kamar aikin wuta na Mambilla da sauransu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.