An Taso Gwamna a Arewa a Gaba Ya Koma APC, Tinubu Zai Iya Karasa Aikin da Buhari Ya Watsar

An Taso Gwamna a Arewa a Gaba Ya Koma APC, Tinubu Zai Iya Karasa Aikin da Buhari Ya Watsar

  • Wata ƙungiyar matasa ta shawarci Gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba ya koma jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya
  • Kungiyar mai suna 'Concerned Taraba Youth Group' ta bukaci Gwamna Kefas ya haɗa kai da Bola Tinubu domin samun ayyukan more rayuwa
  • Ta ce hakan zai taimaka wajen farfado da manyan ayyukan gwamnati kamar aikin wuta na Mambilla da sauransu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Jalingo, Taraba - Kungiyar matasan Taraba ta ba da shawara mai muhimmanci ga Gwamnan jihar, Agbu Kefas domin kawo mata ci gaba.

Kungiyar mai suna 'Concerned Taraba Youth Group' ta roƙi Gwamna Agbu Kefas da ya haɗa kai da Shugaba Bola Tinubu ta hanyar shiga jam’iyyar APC.

An shawaric gwaman ya koma APC domin aiki da Tinubu
Gwamna Agbu Kefas na Taraba da Bola Tinubu. Hoto: Agbu Kefas, Bayo Onanuga.
Source: Facebook

An ba gwamna Kefas shawara ya koma APC

Kungiyar ta bayyana wannan kira ne a taron manema labarai a Jalingo a jiya Asabar 4 ga watan Oktoba, 2025, cewar rahoton Tribune.

Kara karanta wannan

Gwamna ya lallaba ya gana da Tinubu, za a saki jagoran 'yan ta'adda da Buhari ya kama a 2021

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har ila yau, ta ce haɗin kai da gwamnatin tarayya zai kawo ci gaban da ake bukata a bangarori da dama domin tabbatar da dorewar manyan ayyuka.

Mai magana da yawun kungiyar, Kwamred Shedrack Iremiya Gani, ya nuna damuwa da yadda wasu muhimman ayyukan gwamnatin tarayya ke ta lalacewa a Taraba.

Ya ce rashin daidaiton siyasa tsakanin jihar da gwamnatin tarayya ne ke sa a bar ayyukan kamar na Mambilla da hanyoyin Jalingo–Wukari.

Gani ya ce:

“Muna so Gwamna Kefas ya kafa tarihi ta hanyar barin PDP ya shiga APC domin jawo ayyukan ci gaba kamar yadda ke faruwa a jihohin APC.”
An roki gwamna Kefas ya koma APC
Gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba. Hoto: Agbu Kefas.
Source: Twitter

Alherin da Taraba za ta samu karkashin APC

Kungiyar ta bayyana cewa, idan Taraba ta zama jihar APC, hakan zai kawo ayyukan ci gaba, hanyoyi, da damar ayyukan yi ga matasa a cikin jihar, cewar Punch.

“Mun san Gwamna Kefas ya yi kokari wajen gyaran ilimi, kiwon lafiya da tallafa wa matasa, amma haɗin kai da Tinubu zai ƙara cigaba.”

Kara karanta wannan

Triumph: An shawarci Abba game da kalaman mataimakinsa, Sagagi kan zargin taba annabi

- Shedrack Iremiya Gani

Abin da kungiya ta hango a jihar Taraba

Kungiyar ta lissafo wasu manyan ayyuka da aka bari kamar gadar Ibi, gadar Namnai da kuma hanyoyin tarayya da ke cikin halin tabarbarewa.

Ya kara da cewa:

“Gwamnanmu na bukatar yin aiki tare da Shugaba Tinubu domin Taraba ta samu kulawar gwamnatin tarayya da cigaban tattalin arziki.”

A ƙarshe, matasan sun bayyana cewa Taraba ba za ta cigaba da zama a gefe ba yayin da ake aiwatar da 'Renewed Hope Agenda' ta Bola Tinubu a ƙasa baki ɗaya.

Gwamna ya musanta kashe N5bn kan tafiye-tafiye

A baya. kun ji cewa wasu rahotanni sun fito masu nuna cewa gwamnan Taraba, Agbu Kefas, ya kashe biliyoyin Naira wajen yin tafiye-tafiye zuwa kasashen waje.

Gwamnatin jihar Taraba ba ta gamsu da fitar wadannan rahotannin ba, inda ta bayyana cewa babu komai a cikinsu face karya wanda aka yi domin bata mata suna.

Kara karanta wannan

Uwargidan Shugaban ƙasa, Remi Tinubu ta samu sarauta a Gombe

Kwamishiniyar yada labaran jihar, Hajiya Zainab, ta bayyana cewa batun Gwamna Kefas ya kashe kudaden ba komai ba ne fa ce tatsuniyar gizo da koki.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.