'Ka ba Mu Dama': Mutanen Sokoto Sun Tura Sako ga Tinubu kan Harin Ƴan Bindiga

'Ka ba Mu Dama': Mutanen Sokoto Sun Tura Sako ga Tinubu kan Harin Ƴan Bindiga

  • Al’ummar wani yanki a Sokoto sun tura roko da neman alfarma ga gwamnati kan matsalar tsaro da ta ki ci ta ki cinyewa
  • Mutanen sun bukaci gwamnatin Bola Tinubu ta ba su damar ɗaukar makamai don kare kansu daga hare-haren ‘yan Lakurawa
  • Shugaban su, Alhaji Adamu Kebbe, ya zargi gwamnati da sakaci da barin jama’a cikin halin kunci da matsi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kebbe, Sokoto - A yayin da hare-haren ‘yan ta'addan Lakurawa ke ƙaruwa, mazauna wani yanki a Sokoto sun nemi alfarma.

Al'ummar yankin Karamar Hukumar Kebbe a Jihar Sokoto sun roƙi Gwamnatin Tarayya ta ba su damar ɗaukar makamai don kare kansu.

Al'ummar Sokoto sun bukaci ba su damar daukar makami
Taswirar jihar Sokoto da ke Arewa maso Yamma a Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Yan bindiga sun taso yan Sokoto a gaba

Mutanen sun bayyana damuwarsu a taron manema labarai da aka gudanar a ofishin yan jarida a Sokoto, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Sokoto: Ƴan bindiga sun tilasta mutane barin gidajensu, garuruwa 17 sun zama kufai

A yayin taron, mutanen suka ce ba za su iya jure kisan jama’a da lalata dukiya ba da yan bindiga ke yi musu ba.

Kungiyar da Alhaji Adamu Kebbe ke jagoranta ta zargi hukumomin jiha da ƙananan hukumomi da barin su cikin wani hali, tana cewa gwamnati ba ta mayar da martani yadda ya dace ba.

Ya ce:

“Ba za mu iya barci da ido biyu ba, an kusan kawar da garuruwanmu, amma gwamnati ba ta yin isasshen abu don kare mu."
Mazauna Sokoto sun roki Tinubu game da harin yan bindiga
Shugaba Bola Tinubu yayin wani taro a Abuja. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Rokon da yan Sokoto suka yiwa Tinubu

Haka kuma, sun roƙi Gwamnatin Tarayya ta samar da tallafin kai tsaye ga ƙananan hukumomi domin su iya ɗaukar matakan gaggawa wajen kare jama’a daga hare-hare.

Jihar Sokoto na daga cikin wuraren da rikicin ‘yan bindiga ya fi muni a shekarun baya-bayan nan, musamman a yankunan Isa, Sabon Birni, da Kebbe.

Duk da cewa gwamnatin jiha ta amince da tsanantar barazana, mazauna na cewa matakan da ta ɗauka basu isa ba wajen tabbatar da tsaro.

Kara karanta wannan

'Gadon Musulunci na yi': Tinubu ya fadi yadda yake rayuwa da matarsa Kirista

Masana tsaro sun gargadi cewa kiran jama’a su kare kansu alamar rashin imani da kariyar gwamnati ne, don haka akwai bukatar gaggawar matakin tarayya.

“Idan gwamnati bata iya kare mu ba, dole a bar mu mu kare kanmu."

- In ji wani ɗan ƙauye

A farkon watan Satumba 2025, matasan karamar hukumar Shagari sun yi barazanar ɗaukar makamai saboda gajiyawa da hare-hare da sace mutane da suka addabi yankin.

Sun nuna takaicin rashin matakin gwamnati da yadda matsalar tsaro ke lalata noma, iyalai, da rayuwar yau da kullum a yankin, cewar Daily Trust.

Yan bindiga sun tarwatsa ƙauyuka a Sokoto

Kun ki cewa mazauna Sokoto sun koka kan yawaitar hare-haren ‘yan bindiga na kisa da garkuwa da mutane da tilasta wa wasu yin hijira.

Shugabannin al’ummar yankin Kebbe, a taron da suka yi, sun ce akalla garuruwa 17 ne suka zama kufai saboda hare-haren 'yan ta'adda.

Sai dai, gwamnatin jihar Sokoto ta ba da tabbacin cewa tana yin duk mai yiwuwa don kawo ƙarshen matsalar tsaro a Kebbe da kewaye.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.