China Ta Zabi Jiha 1 a Najeriya, Za Ta Gina Tashar Wutar Lantarki da Wurin Kasuwanci

China Ta Zabi Jiha 1 a Najeriya, Za Ta Gina Tashar Wutar Lantarki da Wurin Kasuwanci

  • Kamfanin China, mai suna CCETC ya bayyana shirinsa na gina tashar samar da wutar lantarki da filin masana’antu a jihar Ogun
  • CCETC ya ce zai gina tashar wutar lantarki mai karfin 3MW kyauta a filin jirgin Gateway Agro-Cargo domin bunkasa tattalin arziki
  • Gwamna Dapo Abiodun ya ce wannan mataki na CCETC na daga cikin shirin gwamnatinsa na jawo hannayen jari daga kasashen waje

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ogun - Kamfanin samar da wutar lantarki na kasar Sin, CCETC, ya bayyana shirinsa na gina tashar wutar lantarki da filin masana’antu a jihar Ogun.

Shugaban kamfanin CCETC, Guo Xianda, ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa da gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, a Abeokuta a ranar Asabar.

Kamfanin China zai gina tashar samar da wutar lantarki da cibiyar kasuwanci a Ogun
Gwamna Dapo Abiodun tare da wakilan kamfanin CCETC na China a Abeokuta. Hoto: @DapoAbiodunCON
Source: Twitter

Ogun: Kamfanin China zai gina tashar wuta

Kara karanta wannan

Rashin imani: Yadda harin 'yan bindiga ya maida wani gari zuwa kufai a Kwara

Guo Xianda ya bayyana cewa wannan zuba jarin zai kara bunkasa sha’anin masana’antu da samar da ayyukan yi a Ogun da kasa baki daya, inji rahoton The Cable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma kara da cewa kamfanin zai kafa tashar samar da wutar lantarki mai karfin 3MW a tashar dakon kaya ta Gateway International Agro-Cargo.

Sannan kamfanin ba zai karbi kudin komai daga wajen kowa ba, yana mai cewa wannan aiki na musamman ne domin tallafa wa tattalin arziki da bunkasa harkokin sufuri da kasuwanci a yankin.

Kamfanin CCETC, wanda ke da hedikwata a Jiangsu, kasar Sin, ya riga ya zuba jari a Najeriya da wasu kasashen Afirka.

CCETC: Ayyukan China a Najeriya da Afrika

A cewar Xianda, kamfanin yana da ayyukan samar da wutar lantarki da suka kai fiye da 250MW a Najeriya, kuma yana shirin fadada ayyukansa zuwa 5,000MW a duk fadin nahiyar Afirka.

Ya bayyana cewa kamfanin zai mayar da hankali a fannoni uku: samar da wuta da rarrabawa, saka jari a cibiyar sadarwar wutar lantarki ta jihar Ogun.

Hakazalika, kamfanin zai samar da filin masana’antu da zai jawo kamfanonin kasar Sin su zuba jari a jihar. Wannan, a cewarsa, zai kara samar da ayyukan yi da habaka tattalin arzikin cikin gida.

Kara karanta wannan

Tazarce: An zakulo manyan abubuwa 6 da za su taimaka wa Tinubu ya ci zabe a 2027

Gwamnan Ogun Dapo Abiodun ya ce matakin China na gina tashar lantarki na daga shirinsa na jawo hannayen jari daga waje
Gwamna Dapo Abiodun yana jawabi a zauren majalisar dokokin jihar Ogun. Hoto: @DapoAbiodunCON
Source: Twitter

Gwamnati ta yabawa kamfanin China

A sanarwar da ya fitar a shafinsa na X, Gwamna Dapo Abiodun ya yaba wa CCETC saboda wannan zuba jari, yana mai cewa hakan na cikin manufar gwamnatin jihar ta jawo masu zuba jari daga kasashen waje.

“Kamfanin zai mai da hankali kan abubuwa uku masu muhimmanci — samar da wuta mai dorewa, inganta hanyar rarrabawa, da kafa filin masana’antu da zai jawo masana’antun kasar Sin zuwa Ogun."

- Gwamna Dapo Abiodun.

The Nation ta rahoto cewa gwamnan zai kai ziyara don duba ayyukan da kamfanonin Sahara da Powergen ke gudanarwa a fannin wuta domin tabbatar da sahihiyar wutar lantarki a jihar.

Wannan, a cewarsa, wani bangare ne na shirin gwamnati na tabbatar da wutar lantarki mai dorewa ga masana’antu da al’umma baki ɗaya.

Gwamna ya hada kai da China kan wuta

A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin Gombe ta dauko aikin da zai kawo karshen matsalar wutar lantarki a jihar bayan matsalolin da suka faru.

Kara karanta wannan

Rikicin shugabanci: Jami'an tsaro sun mamaye ginin sakatariyar jam'iyyar PDP

Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya zai yi aiki da kamfanin China domin samar da tashar lantarki mai amfani da hasken rana a jihar Gombe.

A halin da ake ciki, gwamnatin Gombe ta rattaba hannu a kan yarjejeniyar gina tashar lantarki mai amfani da hasken rana mai girman megawat 100.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com