Hankali Ya Kwanta: Babban Alkawari da Tinubu Ya Yi Ga Kiristocin Arewacin Najeriya
- Shugaba Bola Tinubu ya yi alkawari babba ga al'ummar Kiristocin Arewacin Najeriya yayin ziyarar da ya kai a jihar Plaateau
- Shugaban ya ce burinsa shi ne haɗa kan al’ummar Najeriya, ya kuma tabbatar da cewa gwamnati za ta yi adalci ga dukkan addinai
- Ya bayyana hakan ne a cocin COCIN da ke Jos yayin jana’izar mahaifiyar shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Jos, Plateau - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ja hankulan al'ummar Najeriya musamman Musulmi da Kiristoci.
Tinubu ya ce yana da manufa ta haɗa kan al’ummar Najeriya, tare da yin alkawari ga al'ummar Kiristoci a yankin Arewa.

Source: Twitter
Tinubu ya yi alkawari ga Kiristocin Arewa
Hadimin shugaban kasa a bangaren sadarwa, Bayo Onanuga shi ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafin X.

Kara karanta wannan
Babu boye boye, an ji dalilin da ya sa Bola Tinubu bai jawo matarsa ta karbi musulunci ba
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban kasa ya tabbatar wa Kiristocin Arewa cewa gwamnatinsa za ta yi adalci ga kowa ba tare da nuna bambanci ba.
Tinubu ya bayyana haka ne a ranar Asabar yayin da yake ziyarar cocin 'Church of Christ in Nations (COCIN)' da ke Jos, jihar Plateau, inda ya gana da shugabannin Kirista daga Arewa.
Ya ce:
“Na fito daga gida mai asalin Musulunci, amma na auri mace Kirista wacce fasto ce, kuma ban taɓa tilasta mata ta canza addininta ba. Dukkanmu muna bauta wa Allah guda ɗaya.”
Shugaban ƙasar ya kuma yi kira ga shugabannin addini da su ci gaba da goyon bayan gwamnatinsa wajen inganta zaman lafiya da haɗin kai tsakanin Musulmi da Kirista.
A yayin jana’izar mahaifiyar shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Nana Lydia Yilwatda, wacce ta rasu tana da shekaru 83, Tinubu ya bayyana marigayiyar a matsayin uwa mai sadaukarwa da ta yi rayuwa wajen hidima ga jama’a.

Source: Facebook
Gwamna ya godewa Tinubu kan halartar jana'iza
Gwamnan Plateau, Caleb Mutfwang, ya gode wa shugaban ƙasa bisa halartar jana’izar duk da cunkoson aikinsa, tare da yabawa matakan da gwamnati ke ɗauka don kawo zaman lafiya a jihar.
Shugaban cocin COCIN, Rabaran Amos Mohzo, ya gode wa Tinubu bisa ɗaukar Kiristocin Arewa a manyan mukamai.
Faston ya ce daga cikinsu akwai George Akume (SGF) da Farfesa Nentawe Yilwatda (shugaban APC), yana mai cewa hakan ya nuna adalci da haɗin kai.
Ya kuma roƙi shugaban ƙasa da ya taimaka wajen dawo da ‘yan gudun hijira daga Borno da Adamawa waɗanda suka tsere zuwa Kamaru saboda hare-haren ‘yan ta’adda.
A wajen jana’izar, manyan jami’an gwamnati da ‘yan siyasa da dama sun halarta ciki har da Sanata Godswill Akpabio, Nuhu Ribadu, Femi Gbajabiamila, da tsofaffin gwamnonin Nasarawa, Bauchi, Plateau, Kogi, da Imo.
Tinubu ya magantu kan rashin mayar da matarsa Kirista

Kara karanta wannan
Gwamnatin Tinubu ta yi martani kan zargin jefa 'yan Najeriya miliyan 15 a bakin cikin talauci
Kun ji cewa Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ja hankalin yan Najeriya game da zaman lafiya musamman a tsakanin mabambantan addinai.
Tinubu ya bukaci ‘yan Najeriya su guji bambancin addini da kabilanci, yana mai cewa ƙauna da zaman tare su ne ginshiƙan ci gaba.
Gwamna Caleb Mutfwang ya gode wa Tinubu bisa halartar jana’izar mahaifiyar shugaban APC, yana mai jaddada kudurin gwamnati domin zaman lafiya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng