Basaraken Borno da Mayakan Boko Haram Suka Konawa Fada Ya Yi Magana daga Kamaru

Basaraken Borno da Mayakan Boko Haram Suka Konawa Fada Ya Yi Magana daga Kamaru

  • Sarkin Kirawa a Borno, Abdulrahman Abubakar, ya tsere zuwa Kamaru bayan Boko Haram ta kai hari garin Kirawa, ta ƙone fadarsa
  • Sarki Abdulrahman ya bayyana cewa babu wani zaɓi da ya rage masa da wuce ya gudu zuwa Kamaru don tsira da rayuwarsa
  • Rahotanni sun bayyana cewa, fiye da mutane 5,000 suka tsere Kamaru bayan hare-haren Boko Haram sun tsananta a yankin Gwoza

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Borno — Sarkin Kirawa, Abdulrahman Abubakar, ya yi magana game da dalilin da ya sa ya tsere daga Najeriya zuwa kasar Kamaru.

Legit Hausa ta rahoto cewa sarkin ya yi hijira bayan ‘yan ta’addan Boko Haram sun kai mummunan hari a garinsa da ke karamar hukumar Gwoza, jihar Borno.

Sarkin Kirawa yayi magana daga Kamaru bayan Boko Haram ta kona fadarsa a Borno
Hoton fadar sarkin Kirawa da Boko Haram ta kona a Borno. Hoto: @ZagazOlaMakama/X
Source: UGC

Sarkin Kirawa ya yi magana daga Kamaru

Rahoton Daily Trust ya bayyana cewa mutane biyu sun rasa rayukansu, sannan ‘yan ta’addan sun ƙone fadar Sarki AbdulRahaman tare da lalata wasu gine-gine masu muhimmanci a garin.

Kara karanta wannan

Bayan yi wa matar Sarki tsirara, an kama mutum 10 da zargin yunƙurin hallaka basarake

A wata tattaunawa da kamfanin labarai na Reuters, sarkin ya ce “babu wani zaɓi da ya rage masa sai guduwa” bayan hare-haren sun tsananta.

“An bar ni ba tare da wani zabi ba sai na tserewa zuwa Kamaru. Mazauna garin suma sun hau manyan motoci suna tserewa zuwa iyakar kasar, wasu kuma sun nufi Maiduguri."

- Sarkin Kirawa, Abdulrahman Abubakar.

Fiye da mutum 5,000 sun tsere zuwa Kamaru

An ruwaito cewa fiye da mutane 5,000 daga yankin Gwoza sun tsere zuwa ƙasar Kamaru, bayan hare-haren da Boko Haram ke kaiwa a kananan hukumomin da ke makotaka da kasar.

Hakan ya sake bayyana raunin tsaro a yankunan kan iyakar Najeriya, inda jama’a ke fuskantar hare-haren ba tare da wata kariya mai ƙarfi ba.

A wani bidiyo da Boko Haram ta fitar, an nuna mayakan suna kona barikin soja, wanda hakan ya tabbatar da ikirarin da sarkin da mazauna yankin suka yi.

Kara karanta wannan

Tsautsayi: Tankar mai ta yi tsiya a cikin mutane ranar Juma'a, an rasa rayuka da yawa

Martanin gwamnan Borno kan halin da ake ciki

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya tabbatar da hare-haren yayin ziyararsa ta kimanta barnar da aka yi a yankin.

Mai girma Gwamna Zulum ya ce gwamnatinsa ta tura masu farauta da jami'an tsaro na CJTF domin taimakawa wajen tsaron al’umma.

Gwamnan ya bayyana cewa sojojin Kamaru sun taka muhimmiyar rawa wajen dawo da jama’a Kirawa shekaru da suka gabata bayan sun yi hijira saboda rikicin Boko Haram.

“Da taimakon sojojin Kamaru ne muka dawo da mutane garin Kirawa bayan shekaru bakwai da hijirarsu. Amma yanzu, bayan sojojin sun tafi, ‘yan ta’adda sun sake korar jama’a."

- Gwamna Babagana Zulum.

Gwamna Babagana Zulum ya ce akwai bukatar kawo karin jami'an tsaro a yankin Gwoza
Taswirar jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Asarar rayuka da dukiyar jama'a a Borno

A cewar Zulum, mutane biyu ne suka mutu, amma an babbake gidaje 50, motoci takwas, da manyan kayan aiki na gwamnati da na 'yan kasuwa.

“Mun gode wa Allah cewa ba a rasa rayuka da yawa ba, amma abin da aka lalata yana da yawa sosai. Dole ne a dawo da tsaro da sauri don jama’a su koma gidajensu,” in ji gwamnan.

Kara karanta wannan

Martanin da Sarki ya yi bayan zargin Peter Obi da rashin mutunta shi a sakon taya murna

Masana harkokin tsaro na cewa yankunan kan iyaka na Arewa maso Gabas suna cikin haɗari saboda rashin isassun jami’an tsaro da kayan aiki.

Mazauna Gwoza sun bukaci gwamnatin tarayya da ta sake tura sojoji da kayan aikin tsaro, tare da maido da tsarin tsaro na hadin gwiwa da Kamaru don dakile hare-haren Boko Haram.

Boko Haram sun kona fadar Kirawa

Tun da fari, mun ruwaito cewa, 'yan ta'addan kungiyar Boko Haram sun kai wani harin ta'addanci a jihar Borno, inda suka tafka ta'asa.

Miyagun sun hallaka mutum daya tare da kona gidaje da shaguna na mutanen garin Kirawa da ke karamar hukumar Gwoza.

Sanata Ali Ndume ya tabbatar da aukuwar harin, inda ya bukaci gwamnati ta kara tura jami'an tsaro zuwa yankin don kare rayuka da dukiyoyi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com