'Ban Ce Haka ba': Sanusi II Ya Yi Karin Haske kan Cewa Mata Su Rama Dukan Mazajensu
- Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya ce an yi masa mummunan fahimta kan kalamansa game da dukan mata a Musulunci
- Sanusi II ya bayyana cewa bai ce mace ta rama mari ba, inda ya yi bayanin cewa maganarsa ta danganci tarihi ne, ba umarni ga mata ba
- Ya kara da cewa Manzon Allah SAW ya kushe masu dukan matansu, yana mai cewa dukan mace ba alamar mutunci ko kyawawan dabi’u ba ne
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Sarki Muhammadu Sanusi II ya yi karin haske kan kalamansa da suka shafi dukan mata a Musulunci.
Basaraken ya ce an yi masa mummunan fahimta saboda ba abin da ake yadawa yake nufi ba a cikin maganganunsa.

Source: Twitter
Dukan mata: Muhammadu Sanusi II ya kare kansa

Kara karanta wannan
Fusatattun matasa sun yi wa matar sarki tsirara, an lakadawa sarki da yarima duka
Hakan na ciki wani hira a faifan bidiyo da ya yi da shafin Sanusi II Dynasty ya wallafa a manhajar X a yau Asabar 4 ga watan Oktoba, 2025.
A cikin bidiyon, Sanusi II ya bayyana cewa bai ce mace ta rama mari ko duka da mijinta ya yi mata ba.
Sarkin ya ce ya yi maganar ne da ƴaƴansa inda ya ke fadawa diyarsa cewa ta rama idan har mai gidanta ya mare ta.
Ya ce:
"Ba haka na ce ba, duk da mutane sun dauka haka, cewa na yi na cewa ƴata idan mijinta ya mare ta, ta rama.
"Wannan ƴata na ce, ai kafin ma a saukar da wannan aya, mace ta zo wurin Manzon Allah SAW ta ce mijinta ya mare ta, ya ce ki je ki rama.
"Idan ka duba kasashen Musulunci gaba daya kamar Algeriya, Morocco, Tunisia da Saudiyya a dokokin aure babu inda aka ce miji ya daki matarsa."

Source: Twitter
Bayani daga bakin Manzon Allah SAW
Sarki Sanusi II ya bayyana cewa Manzon Allah SAW ya kushe wadanda ke dukan matansu da cewa ba mutanen kirki ba ne.

Kara karanta wannan
Martanin da Sarki ya yi bayan zargin Peter Obi da rashin mutunta shi a sakon taya murna
A cewarsa:
"Saboda ko da an yi izini, ba cewa aka yi abu ne mai kyau ba, Manzon Allah SAW ya ce cikinku akwai masu dukan matayensu amma ba su ne mutanen kirki ba.
"Wurin da ma ya ce a yi duka shi ne idan ta kawo wani namiji ko wani lamarin alfasha, ba kawai mutum matarsa ta yi masa rashin kunya ya kamata yana mari ba."
Basaraken ya bayyana yadda ya dace a yi duka kamar da asuwaki ko hannun riga ba kamar yadda ake yi yanzu ba.
Ya ce wasu kawai zage wa suke yi da duka, naushi wanda zai illata mata cikin fushi da wuce gona da iri.
Sanusi II ya bukaci ba mata dama a siyasa
A wani labarin, Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya ba da shawara kan shigan mata harkokin siyasa a Najeriya domin kara samun ci gaba.
Basaraken ya bukaci gwamnati ta cire shinge da ke hana mata shiga siyasa, kasuwanci da shugabanci wanda abin takaici ne.

Kara karanta wannan
Gwamna ya bukaci diyyar N100bn bayan tsohon kwamishina ya kira shi barawo a Facebook
Sanusi II ya bayyana yadda ya kawo sauyi lokacin da yake gwamnan babban bankin Najeriya, CBN.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng