Tirelar Siminti Ta Murkushe Keke Napep, Fasinjoji 5 da Ke ciki Sun Mutu nan Take

Tirelar Siminti Ta Murkushe Keke Napep, Fasinjoji 5 da Ke ciki Sun Mutu nan Take

  • Ana zargin motar Dangote ta kashe mutum biyar a Alapoka, Papalanto–Ilaro Road, jihar Ogun, bayan ta murkushe Keke Napep
  • Rahoton hukumar TRACE ya bayyana cewa mutane biyar da ke cikin Keke Napep din sun mutu nan take, lamarin da ya fusata matasa
  • Wannan ba shi ne karo na farko ba da motar Dangote ta haddasa mummunan hatsari, an ruwaito irin haka sau da dama a jihohin Najeriya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ogun — Wani hatsari mai muni da ya faru a ranar Juma’a da daddare a kan titin Papalanto–Ilaro ya yi sanadin mutuwar mutum biyar nan take.

An ce wata motar simintin Dangote ce ta rasa birki, inda ta murkushe Keke Napep da ke dauke da fasinjoji a hanyar da ke karamar hukumar Yewa ta Kudu a jihar Ogun.

Kara karanta wannan

Tsautsayi: Tankar mai ta yi tsiya a cikin mutane ranar Juma'a, an rasa rayuka da yawa

Tirela ta murkushe Keke Napep a Ogun, fasinjoji 5 sun mutu nan take.
Hoton tankar mai da wasu ababe hawa a titin Najeriya. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Tirela ta kashe fasinjojin Keke Napep 5

Jaridar Punch ta rahoto Babatunde Akinbiyi, kakakin hukumar kula da zirga-zirga ta jihar Ogun, watau TRACE, ya tabbatar da faruwar lamarin da misalin karfe 8:30 na dare a yankin Alapoka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Wani mummunan hatsarin mota ya faru a Alapoka, Papalanto–Ilaro Road, wanda ya shafi motar Dangote mai lamba GRZ 767 XA da kuma Keke Napep mara rajista. Mutum biyar da ke cikin keken sun mutu nan take."

- Babatunde Akinbiyi.

Kakakin ya ce wani ganau ya shaida cewa motar Dangote ta rasa birki ne a yayin da take tsaka da tafiya, lamarin da ya sa ta murkushe Keke Napep da ke ɗauke da mutum biyar.

“Direban motar bai san cewa ya yi karo da adaidaita sahun ba, har sai bayan da tayar motar ta murƙushe fasinjojin da ke ciki,” in ji majiyar.

Matasa sun nemi farwa jami'ai bayan hatsari

Bayan samun rahoton, jami’an TRACE karkashin jagorancin Adedayo Omonayajo, da kwamandan sashen Ilaro, Salako Idowu, sun isa wajen domin kai daukin gaggawa.

Kara karanta wannan

Gobara ta tashi a fitacciyar kasuwa a Najeriya, an yi asarar miliyoyin Naira

Rahoton ya bayyana cewa mazauna yankin sun fusata tare da yunkurin kai hari kan jami’an, yayin da suka zargi motocin Dangote na haddasa asarar rayuka ba tare da daukar mataki ba.

Sai dai Akinbiyi ya ce jami’an Amotekun sun isa wajen da wuri kuma sun kwantar da tarzomar, wanda ya sa lamarin bai rikide zuwa tashin hankali ba.

“An yi yunƙurin kai hari kan jami’anmu, amma zuwan jami’an Amotekun ne ya kawo daidaito. Daga bisani, jami’an FRSC suka dauki gawawwakin zuwa dakin ajiye gawa."

- Babatunde Akinbiyi, kakakin hukumar TRACE.

An rahoto cewa, motocin Dangote sun yi sanadin hadurran da suka jawo mutuwar mutane da dama
Taswirar jihar Ogun da ke a Kudancin Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Hatsarin tirelolin Dangote a baya

Wannan lamari ya sake jawo ce-ce-ku-ce game da aminci da kulawar motocin Dangote a titunan Najeriya, domin ba wannan ne karo na farko da irin wannan hatsari ke faruwa ba.

A cikin Nuwamba 2024, wani hatsari mai kama da wannan ya faru a tsakanin Lagos da Ogun, inda motar Dangote ta rasa birki ta kuma haddasa hatsari mai muni. A wancan lokacin, mutum hudu sun mutu, wasu bakwai suka jikkata.

Haka zalika, a Junin 2021, wani hatsarin motar Dangote a Ogun ya yi sanadin mutuwar direban babur da fasinjarsa, lamarin da ya sa fusatattun matasa suka kona motar nan take.

Kara karanta wannan

An hallaka shedanin dan bindiga, matasa sun kona fadar Sarki da harsashi ya samu dalibai

A baya-bayan nan, tauraruwar BBNaija, Phyna, ta fito ta caccaki Dangote bayan da ɗaya daga cikin motocin kamfanin ya murƙushe ‘yar uwarta, wadda daga baya ta rasu, inji rahoton Pulse Nigeria.

An hana motocin Dangote wucewa a Edo

A wani labarin, mun ruwaito cewa, mai fafutukar kare hakkin dan Adam, Martins Vincent Otse (VDM), ya hana motocin Dangote wucewa a Edo.

Very Dark Man ya ce sun dauki matakin ne domin kare jama’a daga hadura, inda suka ba mutanen cikin motar tallafi domin ci gaba da tafiya.

Fitaccen matashin dan gwagwarmayar ya bukaci Aliko Dangote ya kula da direbobinsa saboda yawan hadura, yayin da ake jiran jin ta bakin kamfanin.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com