Bayan Kalaman Jonathan, Obasanjo Ya Yi Magana kan Rikicin Boko Haram

Bayan Kalaman Jonathan, Obasanjo Ya Yi Magana kan Rikicin Boko Haram

  • Tsohon shugaban kasan Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya yi maganganu kan rikicin Boko Haram da aka dade ana fama da shi
  • Obasanjo ya yi tambayoyi kan yadda rikicin ya fara da kuma irin matakan da da aka dauka don ganin an kawo karshensa
  • Tsohon shugaban kasan ya nuna cewa rikicin ya riga ya zama wani abu da 'yan Najeriya ke rayuwa da shi na tsawon shekaru

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo, ya yi magana kan ta'addancin Boko Haram.

Olusegun Obasanjo ya yi gargadin cewa ta’addancin Boko Haram ya kusa zama wani ɓangare na rayuwar yau da kullum ga ‘yan Najeriya.

Obasanjo ya yi kalamai kan rikicin Boko Haram
Tsohon shugaban kasan Najeriya, Olusegun Obasanjo, na yin jawabi. Hoto: @SenBalaMohammed
Source: Facebook

Jaridar The Punch ta ce Obasanjo ya yi wannan bayani ne a ranar Juma’a a Abuja, yayin bikin laddamar da littafin “Scars: Nigeria’s Journey and the Boko Haram Conundrum”.

Kara karanta wannan

Jonathan ya ce Boko Haram ta taba zabar marigayi Buhari a matsayin wakili

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon babban hafsan hafsoshin tsaro, Janar Lucky Irabor (mai ritaya) ya rubuta littafin.

Me Obasanjo ya ce kan Boko Haram?

Tsohon shugaban kasan ya yi kira ga kasar nan da ta fuskanci wannan barazana da tambayoyi masu zurfi da kuma kuduri mai karfi don ganin an kawo karshenta, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar da labarin.

"Yanzu Boko Haram kusan ta zama wani ɓangare na rayuwarmu. Shin za mu yarda da hakan? Idan ba za mu yarda ba, me ya kamata mu yi?
"Mu na da isasshen ilimi game da rikicin? Ko daga bangarensu, ko daga bangarenmu, shin mun yi aiki yadda ya kamata? Shin mun yi taka-tsantsan da daukar tsauraran matakai tun kafin faruwar abin?"
"Ina ganin dole ne mu tambayi kanmu waɗannan tambayoyi don mu iya fuskantar wannan abu da ya fara zama dodo a cikin kasarmu."

- Olusegun Obasanjo

Tsohon shugaban kasan, wanda ya rubuta gabatarwa a littafin na Irabor, ya yaba wa tsohon hafsun kan rubuta kwarewarsa a yaki da ta’addanci domin amfanin tarihi, yana mai bayyana wannan mataki a matsayin jarumtaka.

Kara karanta wannan

Triumph: An shawarci Abba game da kalaman mataimakinsa, Sagagi kan zargin taba annabi

Obasanjo ya yi magana kan rikicin Boko Haram
Tsohon shugaban kasan Najeriya, Olusegun Obasanjo. Kola Sulaimon
Source: Getty Images

Jonathan ya yi jawabi a wajen taron

Daga cikin masu jawabi a wajen taron kaddamar da littafin, har da shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Jonathan ya bayyana cewa akwai lokacin da ’yan Boko Haram suka zaɓi tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin wanda suke so ya jagoranci tattaunawar zaman lafiya da gwamnatinsa.

Jonathan ya ce gwamnatinsa ta kafa kwamitoci da hanyoyi daban-daban domin kawo karshen rikicin, amma matsalar ta kasance mai rikitarwa fiye da yadda bayyana ta.

Ya kara da cewa, sace ɗaliban makarantar Chibok a 2014 zai kasance tabo na dindindin a kan gwamnatinsa.

Usman Bugaje ya 'karyata' Obasanjo

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon dan majalisar wakilai, Usman Bugaje, ya yi martani kan kalaman tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya yi kan batun neman wa'adin mulki na uku.

Usman Bugaje wanda ya kasance dan majalisa a lokacin mulkin Obasanjo, ya bayyana cewa tsohon shugaban kasan ya yi bakin kokarinsa wajen ganin ya ci gaba da zama a kan madafun ikon Najeriya.

Kara karanta wannan

"Akwai rikitarwa," Jonathan ya bayyana abin da mutane ba su sani ba game da Boko Haram

Tsohon dan majalisar ya tabbatar da cewa 'yan majalisu a wancan lokacin suna da masaniya kan batun tazarcen na Obasanjo.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng